| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
A karon farko Nijeriya ta fitar da mai fiye da wanda ta shigar cikin ƙasar
Ƙasar da ta fi samar da mai a Afirka ta sauya wani yanayi da ta daɗe tana bi a tarihinta inda matatar man Dangote ta ba da rahoton rara yayin da take rage yawan man fetur ɗin da ƙasar ke shigarwa zuwa mataki mafi ƙaranci.
A karon farko Nijeriya ta fitar da mai fiye da wanda ta shigar cikin ƙasar
Matatar man babban attaijirin Nijeriya Aliko Dangote mai tace ganganr ɗanyen mai 650,000 a rana ita ce mafi girma a Afirka / TRT Afrika English

Nijeriya ta sauya yanayi na fitar da ɗanyen mai yayin da take shigowa da tataccen mai domin kasancewa ƙasa mai fitar da tataccen mai a karon farko a tarihinta.

Matatar man Aliko Dangote ta fitar da gangar man fetur 44,000 ko wace rana a watan Maris, fiye da abin da ƙasar ke shigarwa, lamarin da ya samar da rara ta gangar mai 3,000 a ko wace rana.

Iskar gas ɗin da Nijeriya ke shigarwa ta ragu zuwa gangar mai 41,000 a cikin watan, mataki mafi ƙanƙanta a tarihin ƙasar.

Adadin man da Nijeriya ke shigarwa ya ragu ne yayin da man da matatar ke samarwa ya ƙaru, kuma aka soma fitar da rarar zuwa ƙasashen waje.

Matatar tana iya tace gangar ɗanyen mai 650,000 a ko wace rana.

Mafi yawa

Ta tace kimanin gangar ɗanyen mai 565,000 a watan Maris, ɗaya daga cikin mafi yawa da aka taɓa samu tun lokacin da matatar ta fara aiki a ƙarshen shekarar 2023.

Manufofin Nijeriya na inganta yanayin zuba jari a fannin makamshinta sun taka muhimmiyar rawa wajen kawo wannan sauyin.

Nijeriya ta daɗe tana dogaro a kan shigowa da man fetur domin biyan buƙatunta na cikin gida saboda rashin iya tace mai da kanta, duk da cewa ita ce ƙasar da ta fi samar da ɗanyen mai a nahiyar.

Matatar da ke Legas ta fara aiki ne a watan Janairu bayan ɗankasuwan Nijeriya, ɗaya daga cikin attajiran da suka fi arziki a Afirka, ya kafa ta kan $19bn.

Matatar tana yankin Lekki na jihar Legas, kusa da tekun Atlantika.