| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Nijeriya na neman Turkiyya ta sasanta ta da Nijar don ƙarfafa hadin kai da yaƙi da ta’addanci
Ministan ya jaddada cewa babu wata ƙasa da za ta iya magance matsalar tsaro ita kaɗai, yana mai cewa ‘yanta’adda ba sa girmama iyakoki.
Nijeriya na neman Turkiyya ta sasanta ta da Nijar don ƙarfafa hadin kai da yaƙi da ta’addanci
Tinubu / Nigeria Presidency
6 awanni baya

Ministan Tsaron Nijeriya, Christopher Gwabin Musa ya bayyana cewa Nijeriya na neman taimakon Turkiya ta shiga tsakani wajen gyara alaƙarta da Jamhuriyar Nijar, a wani yunƙuri na ƙarfafa haɗin gwiwar yaƙi da ta’addanci a yankin.

A wata hira ta musamman da TRT Afrika Hausa a Taron Diflomasiyya na Antalya, Minista Musa ya ce ya gaya wa Ministan Tsaron Turkiyya hakan ganawarsu a wajen Taron Diflomsiyyar, inda ya ce sun roƙi Ankara ta yi amfani da alaƙarta da Nijar wajen ƙarfafa su su dawo cikin haɗin gwiwar tsaro na yankin Tafkin Chadi.

“Mun faɗa musu su ma suna da alaƙa da Nijar, su roƙe su su dawo. Ba mu ƙin su, muna son su domin ‘yan’uwa ne,” in ji shi.

Ministan ya jaddada cewa babu wata ƙasa da za ta iya magance matsalar tsaro ita kaɗai, yana mai cewa ‘yanta’adda ba sa girmama iyakoki.

Mista Musa ya ce muhimmancin hakan ne ya sa Shugaban Chadi, Mehmet Idris Deby ya ziyarci Nijeriya a kwanakin baya don ƙarfafa alaƙa da hadin kai a yankin.

Ya ƙara da cewa haɗin gwiwar ƙasashen yankin, ciki har da Kamaru da Chad na da muhimmanci wajen kawo ƙarshen matsalar.

Ya kuma nuna fatan cewa ƙasashen yankin kamar Burkina Faso da Mali za su ci gaba da aiki tare da Nijeriya domin shawo kan barazanar tsaro.

Haɗin gwiwa da Amurka

TRT Afrika Hausa ta tambayi ministan kan wani abu da ‘yan Nijeriya ke yawan magana a kai wato batun wanzuwar sojojin Amurka a kasar, amma suna cewa ba su ga wani sauyi a raguwar hare-hare ba, inda Minista Musa ya ce a yanzu an mayar da hankali ne wajen horo da tsara dabaru da dakarun Amurkan.

Ministan ya ce akwai haɗin gwiwa tsakanin ɓangarorin biyu, amma ya bayyana cewa irin wannan aiki na buƙatar lokaci da shiri kafin a fara ganin sakamako.

“Ana kan bayar da horo da shirye-shirye tare da su,” in ji shi, yana mai cewa samun kayan aiki shi ne mafi muhimmanci domin bai wa Nijeriya damar gudanar da ayyukan tsaro da kanta yadda ya kamata.

Ya jaddada cewa Nijeriya za ta ci gaba da aiki da duk wata ƙasa da ke da niyyar taimakawa wajen samar da zaman lafiya, amma za ta tabbatar da cewa irin wannan haɗin gwiwa ba zai haifar da wata matsala ba a nan gaba.