| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Nijeriya ta yi maraba da 'yarwasan tsere, Favour Ofili wadda aka hana ta sauya kasar da take wakilta
Hukumar wasannin motsa-jiki ta Nijeriya ta ce dawowar Ofili dama ce ta sake gina aminci da kare dangantaka da masu wasan motsa-jiki a lokacin da Nijeriya ke shiryawa gasannin duniya masu gabatowa.
Nijeriya ta yi maraba da 'yarwasan tsere, Favour Ofili wadda aka hana ta sauya kasar da take wakilta
Ofili mai lambar zinariya ce sau shida a gasar zakarun. / Others

Hukumar Wasannin Motsa-Jiki ta Nijeriya (AFN) ta karɓi dawowar 'yar wasan gudu, Favour Ofili cikin jerin ‘yanwasanta, bayan da Hukumar Wasannin Motsa-Jiki ta Duniya ta ƙi amincewa da buƙatar Ofili ta sauya ƙasar da take wakilta.

A cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, AFN ta tabbatar da cewa matashiyar mai shekaru 23 za ta ci gaba da cancantar ta wakilci Nijeriya.

Wannan dai ya kawo ƙarshen watanni na rashin tabbas game da makomarta a matakin ƙasa-da-ƙasa.

Hukumar wasannin ta duniya ta ƙi yarda da buƙatar Ofili, tana mai nuna damuwar cewa hakan na iya zamowa wani sabon salon da zai iya raunana ingancin wasannin. A cewar AFN, an duba wannan buƙata tare da ta wasu ‘yanwasa goma.

Ko da yake an yi la'akari da halin da Ofili take ciki na musamman, ciki har da abin da ya faru yayin halartar Gasar Olympics ta Paris 2024, kwamitin bita ya kammala cewa amincewa da sauyin ƙasa zai tauye manyan ƙa'idodin cancantar ƙasa-da-ƙasa.

Neman goyon baya

A martaninta kan hukuncin, AFN ta nuna kalaman neman sasantawa, tana neman a ba 'yarwasan sabon goyon baya.

Shugaban AFN, Tonobok Okowa, ya ce yanzu ya kamata a mayar da hankali wajen samar da yanayi mai kyau da zai ba Favour Ofili damar yin fice.

"Abin da tafi buƙata a wannan lokaci shi ne ƙauna, goyon baya, ƙarfafawa da kuma ƙarin ƙauna," in ji shi.

Kungiyar ta ƙara da cewa dawowarta wata dama ce ta sake gina amana da ƙarfafa dangantaka da 'yanwasa, yayin da Najeriya ke shirin halartar gasanni masu zuwa.

Ofili ta nemi sauya ƙasa ne bayan takaici kan gazawar gudanarwa a tsarin Nijeriya. Ta kasance cikin 'yanwasan da suka rasa Gasar Olympics ta Tokyo 2020 saboda gaza cika ƙa'idodin hana amfani da miyagun kwayoyi da ake buƙata.

A baya-bayan nan, an cire ta daga tseren mita 100 a Wasannin Olympics na Paris, saboda abin da ta bayyana a matsayin wani kuskuren gudanarwa, duk da cewa ta shiga gasar mita 200, inda ta zo ta shida.