| Hausa
NIJERIYA
1 minti karatu
Shuguba Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin kudin Nijeriya na 2026, ya tsawaita wa'adin na 2025
Kason da aka ware wa ayyukan raya ƙasa ya kai kusan kashi 50 cikin ɗari, wanda ke nuna yadda gwamnatin Tinubu take ci gaba da nuna aniyar daidaita tattalin arziƙi da cigaban ƙasa.
Shuguba Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin kudin Nijeriya na 2026, ya tsawaita wa'adin na 2025
A wasu shekarun baya akan kammala aiki kan dokar kasafin kuɗin kafin shigar shekarar aikinsa. / Others
17 Afrilu 2026

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan ƙudurin dokar kasafin kuɗin gwamnatin tarayyar ƙasar na 2026, kamar yadda mashawarcinsa kan bayanai da dabaru, Bayo Onanuga ya faɗa.

Sanarwar da aka fitar ranar 17 ga Afrilun 2026, ta ce kasafin kuɗin ya kai jimillar naira tiriliyan ₦68.32, wanda ya ƙunshi tiriliyan N4.799 na biyan manyan cibiyoyin gwamnati kai-tsaye, da kuma tiriliyan N15.8 da biyar bashi.

Baya ga sabon kasafin kuɗin 2026, Shugaban ya sanya hannu kan dokar tsawaita wa’adin zartar da tsohon kasafin kuɗin na 2025, daga 31 ga Maris ɗin 2026, zuwa 30 ga Yunin 2026.

A sabon kasafin, an ware tiriliyan N15.4 don hidimomin gwamnati na yau-da-kullum, da kuma tiriliyan N32.2 a matsayin kuɗaɗen ayyukan raya ƙasa da na samar da ababen more rayuwa.

A cewar sanarwar, kason ayyukan raya ƙasa ya kai kusan kashi 50 cikin ɗari, wanda ke nuna yadda gwamnatin Tinubu take ci gaba da nuna aniyar daidaita tattalin arziƙi, tsaron ƙasa, gina ƙasa, da daidaiton cigaban ƙasa.

A halin yanzu, dokar kasafin ƙundin na 2026 ya fara aiki a 1 ga Afrilu, inda gwamnatin tarayya za ta fara aiwatar da shi gadan-gadan daidai da shirin shugaban na Renewed Hope Agenda.