Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa dimokuraɗiyya za ta ɗore a Nijeriya duk da barazanar da take fuskanta, yana mai ba da tabbacin cewa gwamnatinsa ta jajirce wajen gina wata ƙasa mai ƙarfi.
Shugaban ya yi waɗannan kalamai ne ranar Talata yayin da yake karɓar wata babbar tawaga daga jihar Enugu, a ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Peter Mbah, a Fadar gwamnati ta Aso Villa da ke Abuja.
Ya kuma yaba wa gwamna Mbah game da matakan da ya ɗauka wajen magance rashin tsaro da inganta lafiya da ilimi da samar da ababen more rayuwa a jihar.
“Za mu yi komai domin tabbatar da cewa mafarkin Nijeriya ya tabbata. Fatan da ka bayyana a jawabinka ba burin da ba zai yiwu ba ne. Na gaske ne kuma za a iya cika shi tare.
“Dimokuraɗiyya za ta ɗore du da dukkan barazana. Ku ƙyale duk masu cewa hakan ba zai yiwu ba. Ku mayar da hankali. Idan kuka yi nasara kuma suna jin haushi, ku bar su kawai. Ba na kasa barci domin suka saboda mun jajirce wajen gina wata ƙasa mai fata mai haske ga ‘ya’aynmu.
“Waɗannan su ne shugabannin da suka sayar da wutar lantarki ga ‘yan kasuwa, abin da ba ya aiki. Sun ba mu duhu, kuma muna ƙoƙarin ficewa daga ciki. Domin gina wata ƙasa mai fata na gari da kuma mutane masu murna da kuma bar wa ‘ya’yanmu rayuwa da ta dace da alfahari,’’ in ji Tinubu.
Shugaba Tinubu ya yi godiya ga tawagar domin goyon bayanta a gare shi, yana mai cewa abubuwan da ake faɗa game da ci-gaba da da inganta ababen more rayuwa daga jihohi sun tabbatar da tasirin gyran tattalin arziki na gwamnatinsa.
Ya yaba wa gwamnoni wajen amfani da kuɗaɗen da aka bai ƙananan matakan gwamnati yadda ya dace, lamarin da ya janyo inganta kiwon lafiya da ilimi da ababen more rayuwa da rayuwar ‘yanƙasa.
Shugaban ya duba cewa sake haɗaka cikin jam’iyyar APC mai mulki ya samo asali ne daga sakamakon gyaran tattalin arziki, yana mai ƙarawa da cewa Gwamna Mbah ya haɗa kai da APC ne biyo bayan tallafin gwamnatin tarayyar da jihar Enugu ta yi ta samu.
Mbah ya yi alƙawarin goyon baya
A jawabinsa, Gwamna Peter Mbah ya ce tawagar ta kai ziyara fadar gwamnatin tarayya ne domin nuna goyon baya ga manufar shugaban ƙasar ta gina ginshiƙin tattalin arziki mai ƙarfi ga Nijeriya.
“Wannan abu mai cike da alama ne domin ya nuna makomarmu ɗaya da kuma jajircewarmu ga ci-gaba. Mun zo ne domin mu nuna godiyarmu bisa yadda kake yi da mu da kuma zuba jari cikin al’ummar jihar Enugu,” in ji gwamnan.









