Ministan Tsaron Nijeriya, Christopher Gwabin Musa ya yi zargin cewa wasu daga cikin ‘yan ƙasar na da hannu a rikice-rikicen tsaro da ake fuskanta, yana mai cewa irin waɗannan mutane na amfani da tashin hankali ne domin cim ma burin siyasa.
A wata hira da TRT Afrika Hausa a Taron Dilomasiyya na Antalya da ya halarta a Turkiyya, Ministan ya ce abin takaici ne yadda ake ganin yawaitar hare-hare a lokutan da ake tunkarar zaɓe.
“Akwai waɗanda ba sa son zaman lafiya, kuma duk lokacin da zaɓe ya zo sai ka ga rikici ya ƙaru,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa kashe-kashen da ake yi ba zai amfani kowa ba, yana mai gargadin cewa neman shugabanci bai kamata ya zama dalilin tura mutane aikata laifuka ba.
“Idan kana son zama shugaba, ba dole sai ka tura mutane su kashe wasu ba,” ya jaddada.
Ministan ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su haɗa kai wajen yaƙi da masu haddasa rikici, yana mai cewa waɗannan mutane ba sa ƙaunar ƙasar, kuma akwai wasu daga waje da ke amfana da halin da ake ciki.
Ya ce haɗin kai tsakanin al’umma da jami’an tsaro na da matuƙar muhimmanci wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro, yana mai cewa idan aka samu zaman lafiya, hakan zai buɗe ƙofar cigaba.
Musa ya tabbatar da cewa jami’an tsaro na ci gaba da aiki tuƙuru dare da rana domin tabbatar da tsaro a ƙasar, yana mai nuna fatan samun nasara da taimakon Allah.
‘Rikicin duniya na shafar Nijeriya’
Da yake magana kan tasirin halin rashin tabbas da ake fama da shi a duniya, Ministan ya ce rikice-rikicen ƙasa da ƙasa na da tasiri kai-tsaye ga Nijeriya.
Ya bayyana cewa tashin hankali a wurare kamar Iran, Isra’ila da Amurka, da kuma rikicin Rasha da Ukraine, na shafar tattalin arziki da tsaro a duniya baki ɗaya.
A cewarsa, hauhawar farashin kayayyaki da man fetur da ake gani a yanzu na da alaƙa da waɗannan rikice-rikice.
Ya ƙara da cewa halartar mutane kusan 5,000 a Taron Diflomasiyya na Antalya na nuna yadda ƙasashe ke damuwa da halin da duniya ke ciki.
Ministan ya jaddada cewa matsalolin tsaro da Nijeriya ke fuskanta ba ita kaɗai ba ne a wannan hali, yana mai kira ga haɗin kai tsakanin al’umma da gwamnati domin shawo matsalolin.
“Idan babu zaman lafiya, ba za a samu cigaba ba,” in ji shi, yana mai cewa tattaunawa da haɗin gwiwa da sauran ƙasashe na da muhimmanci wajen nemo mafita mai ɗorewa.

















