Wani gungun ‘yanta’adda kan babura sun kai mummunan hari kan wani sansanin sojin Nijeriya da ke arewa maso gabashin ƙasar, a iyaka da ƙasar Chadi.
Rahotanni sun ce harin na ranar Lahadi kan barikin soji na 242 Battalion a Monguno, ya halaka kwamandan sojin da ƙarin sojoji shida, kamar yadda wasu majiyoyin soji suka tabbatarwa kamfanin Reuters.
Majiyoyin sun tabbatar da cewa ‘yan ƙungiyar Boko Haram ne da na wani reshenta na ISWAP suka kai harin, ‘yan kwanaki bayan jerin hare-hare kan sansanonin soji a wasu yankunan Jihar Borno.
A wata sanarwa da Laftanar Kanar Sani Uba ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne a daren ranar 12 ga Afrilu, 2026, lokacin da dakarun Sector 3 na Joint Task Force (North East) suka fuskanci wani hari na kutse a wurin da ake kira Charlie 13 a Monguno.
Dakarun sun fafata da maharan a musayar wuta, inda suka yi nasarar fatattakar su tare da ci gaba da rike sansanin.
Sai dai bayan fafatawar, wani abin takaici ya faru. Kwamandan rundunar, wanda ke kan hanyarsa ta zuwa wajen domin tantance halin da ake ciki da kansa, ya fada kan wani bam din IED. Fashewar ta lalata motarsa tare da kashe shi da wasu sojoji shida, in ji sanarwar sojojin.
‘Yanta’addan sun zafafa farmaki kan sansanonin soji inda suke wawashe makamansu a yankin, kuma hakan na saka matsin lamba kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, wanda ya sha alwashin kawo ƙarshen rikicin.
Waɗanda harin na Lahadi ya rutsa da su sun haɗa da kwamandan sansanin, wanda ya rage wa makonni kafin yin ritaya, da kuma sojoji shida.
Motarsu ce ta taka nakiyar kan hanya da aka dasa yayin da suke ƙoƙarin kai ɗauki ga wani rukunin soji yayin farmakin, kamar yadda majoyoyi suka ambata.
A yayin musayar wuta lokacin harin, an kashe aƙalla ‘yanta’adda 12.
Irin waɗannan hare-hare an shekara 17 Nijeriya na fama da su, musamman a yankin arewa maso gabashi.
Rikicin ya halaka dubban mutane tare da tilastawa mutane miliyan biyu barin gidajensu, duk da cewa ƙasar ta yi ta ƙaddamar da yuƙurin daƙile rikicin.














