Turkiyya ta raba tan 36 na tallafin abinci ga ‘yan gudun hijira a Nijeriya ta hanyar hukumarta ta ba da agajin gaggawa (AFAD), domin taimakawa wajen ƙoƙarin jinƙai da ake yi a ƙasar.
An tura tallafin ne a wani ɓangare na wani shiri da aka yi da Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD), kuma an raba shi a sansanin ‘yan gudun hijira na Malkohi kusa da Yola, babban birnin jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Nijeriya.
Da yawa daga cikin waɗanda suke zama a sansanin ‘yan gudun hijiran sun tsere ne daga gidajensu sakamakon hare-haren ƙungiyar ta’addanci ta Boko Haram kuma suna ci gaba da rayuwa cikin yanayi mai tsanani.
Bikin raba kayayyakin ya samu halartar jakadan Turkiyya a Abuja, Mehmet Poroy, da kwamishinan jinƙai na jihar Adamawa Bello Hamman Diram, da wata jami’ar hukumar ba da agajin gaggawa Selen Laori, tare da hukumomi na yankin da kuma baƙi.
Da yake bayani a wurin, Poroy ya jaddada cewa Turkiyya na cikin ƙasashen da ke sahun gaba wajen ba da tallafi na jinƙai, yana mai cewa: “Waɗannan matakan tallafin [ana yin su ne] domin rage, koda ma zuwa wani ƙaramin mataki ne, wahalar da mutane masu rayuwa da ƙyar a mawuyacin yanayi ke fama da ita .”
Da yake bayyana cewa Turkiyya ta daɗe tana ba da tallafin jinƙai ga Nijeriya, Poroy ya ƙara da cewa ƙasar tana kuma ba da ƙarin tallafi a yaƙin da take yi da ƙalubalenta na tsaro.
A nata ɓangaren jami’an hukumar NEMA ta Adamawa Laori ta gode wa gwamnatin Turkiyya da tallafin , tana mai jaddada cewa kayayyakin tallafin da AFAD ta tura suna da muhimmanci sosai ga mutanen da ke zama a sansanin ‘yan gudun hijiran .
Tan 36 na kayayyakin abincin ana sa ran za su ba ga gudumowa wajen samar da ababen buƙatar yau da kullum a yankin. Kayayyakin sun haɗa da muhimman kayayyakin abinci da abubuwan da za su taimaka wa rayuwar yau da kullum ga mazauna sansanin.
Turkiyya ta ja hankali cikin shekarun nan zuwa ga ayyukanta na jinƙai a faɗin Afirka, inda ta ci gaba da tallafa wa fararen-hula da rikici da ta’addanci suka shafa.
Tallafin, wanda AFAD ta shirya, ana ganin wani ɓangare ne na matakan diflomasiyya na jinƙai na Turkiyya da wanda ke ba da gudunmawa ga ayyukan MƊD a yankin.
Tayar da ƙayar baya da Boko Haram ta daɗe tana yi a arewa maso gabashin Nijeriya ya tilasta wa ɗaruruwan dubban mutane tserewa daga gidajensu, lamarin da ya haddasa matsala ta jinƙai da ke ci gaba da buƙatar tallafi na ƙetare.
















