| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Nijar ta kori ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba, NGO kusan 3,000 a kokarin ‘tsaftace ayyukansu’
Ministan Harkokin Cikin Gida ya ce dakatarwar wani bangare ne na “tsaftace ayyukansu” kuma an ba wa sauran kungiyoyin suka rage manufofin da za su dabbaka a yayin gudanar da ayyukansu.”
Nijar ta kori ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba, NGO kusan 3,000 a kokarin ‘tsaftace ayyukansu’
FILE PHOTO: Ministan Harkokin Cikin Gida na Nijar Janar Mohamed Toumba. / Others / Others

Gwamnatin Nijar ta dakatar da ayyukan kungiyoyin da ba na gwamnati ba da kungiyoyin ayyukan cigaba na cikin gida da na kasashen waje 2,900 daga 4,700 da aka yi wa rajista, in ji ma’aikatar harkokin cikin gida.

Tun watan Yulin 2023 gwamnatin da Janar Abdourahmane Tiani ke jagoranta ta bayar da fifiko ga karfin mulkin kasa, kamar makociyarta kuma kawa Burkina Faso.

A makon da ya gabata, mahukuntan Burkina Faso suka rushe kungiyoyin da ba na gwamnati ba sama da 100 da kungiyoyi tare da hana su gudanar da aiki.

A Nijar, sojoji na yawan zargin kungiyoyin da ba na gwamnati ba da rashin gaskiya da taimaka wa ‘yan ta’adda.

A shekarar bara, mahukunta sun hana ayyukan kungiyoyin da ba na gwamnati ba na cikin gida da na kasashen waje inda ta soke su bisa gaza buga bayanan kasashe kudadensu na 2024 a kan lokaci a jaridar kasa.

“A baya muna da kungiyoyin da ba na gwamnati ba 4,700. A yau muna da 1,800 kawai,” in ji Janar Mohamed Toumba a sanarwar da ya fitar ta gidan talabijin a yammacin Talata.

Kungiyoyin kasa da kasa da ba na gwamnati ba sama da 330 aka yi wa rajista a Nijar amma ba a bayyana adadin wadanda dakatarwar ta shafa ba.

Toumba ya yi karin bayanin cewa dakatarwar wani bangare ne na “tsaftace ayyukansu” kuma “an ba wadanda suka rage manufofin da za su dabbaka”, wanda a yanzu dole ne ayyukansu su zama sun dace da manufofin cigaban kasa.

Kungiyoyin da ba na gwamnati ba sun samo sama da dalar Amurka 448 a 2024, in ji alkaluman da mahukunta suka fitar.

Burkina Faso, wadda kawar Nijar da Mali ce a Kawancen Kasashen Sahel, a shekarar bara ta amince da wata doka da sanya wa kungiyoyin wasu ka’idoji da za su dinga bi wajen gudanar da ayyukansu.