Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Amurka tana gudanar da “tattaunawa mai kyau kwarai” da ƙasar Iran.
“Muna gudanar da tattaunawa mai kyau sosai. Abubuwa suna tafiya daidai. Sun yi ƙoƙarin nuna wayo, kamar yadda suka saba yi tsawon shekaru 47. Babu wanda ya taɓa tunkararsu, amma mu mun tunkare su,” in ji Trump a ofishinsa na Oval Office a ranar Asabar.
Ya ƙara da cewa, “Ba su da rundunar sojan ruwa, ba su da rundunar sojan sama, ba su da shugabanni. Ba su da komai. A gaskiya... wannan canza gwamnati ne. Kuna iya kiran hakan canza gwamnati da ƙarfi, amma muna magana da su.”
“Muna magana da su... mun tsaya tsayin daka,” in ji Trump, yana mai ƙarawa da cewa: “Za mu sami ƙarin bayani kafin ƙarshen yau,” game da tattaunawar da ake yi da Iran.
Trump ya kuma gargaɗi Iran da kada ta yi amfani da batun rufe mashigar ruwan Hormuz don yi wa Amurka “barazana”, bayan da Iran ta sake sanar da rufe hanyar ruwan wadda ke da matuƙar muhimmanci ga tattalin arziƙin duniya.
“Suna son su sake rufe mashigar — ka sani, kamar yadda suka sha yi tsawon shekaru — kuma ba za su iya yi mana barazana ba,” in ji shi.
Tsagaita buɗe wuta
Tashe-tashen hankula sun tsananta tun lokacin da hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran suka fara a ranar 28 ga Fabrairu, inda Irran ta mayar da martani da hare-haren jiragen yaƙi marasa matuƙa da makamai masu linzami da suka nufi Isra’ila da ƙasashen Larabawa wadanda suke da sansanonin dakarun Amurka.
An dakatar da yaƙin ne tun ranar 8 ga Afrilu, lokacin da ƙasar Pakistan ta shiga tsakani aka amince da tsagaita buɗe wuta na tsawon makonni biyu.
Amurka da Iran sun gudanar da tattaunawa a Pakistan a ƙarshen mako da ya gabata, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin sake gudanar da wata tattaunawar a Islamabad.
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Trump ya ce Amurka na yin tattaunawa mai kyau da Iran, ya yi gargaɗi kan rufe Mashigar Hormuz
Shugaban na Amurka ya gargaɗi Iran kan abin da ya kira “barazana” biyo bayan sauya matsayar da Iran ta yi, inda ta sake sanar da rufe Mashigar Ruwan Hormuz.

Rumbun Labarai









