| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Dakarun Nijeriya sun kama masu kai wa 'yanta'adda makamai a Jihar Kogi
Kazalika sojin ƙasar sun daƙile harin 'yanta'adda a jihar Kwara da ke arewa maso tsakiyar Nijeriya.
Dakarun Nijeriya sun kama masu kai wa 'yanta'adda makamai a Jihar Kogi
Sojin Nijeriya na yaƙar 'yanta'adda da masu tayar da ƙayar baya a ƙasar / Reuters

Dakarun runduna ta 12 ta sojin Nijeriya sun yi nasarar kama masu yi wa ‘yanta’adda safarar makamai a wani aiki na musamman da suka shafe watanni suna yi a jihar Kogi da ke tsakiyar ƙasar.

Wata sanarwa da muƙaddashin dakartan watsa labaran rundunar Laftanar Hassan Abdullahi ya fitar ranar Litinin ta ce dakarun sun yi nasarar kama wani ƙasurgumin mai yi wa ‘yanta’adda safarar makamai
Mathew Elisha (da aka fi sani da suna Nasara).

Kazalika sanarwar ta ce ranar 20 ga watan Afrilu rundunar ta sake yin nasarar kama mutum biyu da ake zargi da yi wa ‘yanta’adda safarar makamai, Mallam Zubairu Abubakar da Adamu Abubakar Abdullahi.

Masu AlakaTRT Afrika - Sojojin Nijeriya sun kama mutum 14 da ake zargi da satar mai a Jihar Legas

“An miƙa waɗanda ake zargin da ababen da aka ƙwace daga gare su ga ɓangaren binciken sirri na runduna ta 12 domin ƙarin bincike da ɗaukar matakin da ya kamata,” in ji sanarwar.

Sojoji sun daƙile harin ‘yanta’adda a Kwara

A jihar Kwara da ke arewa ta tsakiyar Nijeriya kuwa, sojojin ƙasar sun yi nasarar daƙile wani harin da ‘yan ta’adda suka kai kan wani sansanin soji ne a ƙaramar hukumar Kaima ta jihar.

Gwamnan jihar Adulrahman Abdulrazaq ya tabbatar da harin da ‘yanta’addan suka kai sansanin sojin inda rahotanni suka ce sojoji uku sun rasa rayukansu.

“Da misalin ƙarfe uku na safiyar yau, jaruman sojojinmu sun kakkaɓe ‘yanta’adda da suka kai hari kan sansaninsu a Kemanji, Kaiama. Dakarunmu masu bajinta sun kashe da yawa daka cikin ‘yanta’addan,” kamar yadda jaridar The Cable ta ambato gwamnan yana cewa.

Gwamnan ya ƙara da cewa nasarar daƙile harin da sojojin suka yi ta sa sojojin sun kare mutanen garin daga harin da ‘yantaddan suka yi ƙoƙarin kaiwa.