hhAn kashe Ministan Tsaron Mali Sadio Camara a wani hari na ta'addanci a gidansa a ranar Asabar, kamar yadda rahoton farko daga Al Jazeera ya bayyana a ranar Lahadi. Yana ambato majiyoyin dangi, Kamfanin dillancin labarai ta AFP ma ya tabbatar da mutuwar ministan.
An kai hari da mota maƙare da bama-bamai gidan Camara a Kati, wani gari da ke kilomita 15 arewa maso yamma na babban birnin Mali, Bamako, wanda ya lalata gidansa sosai. AFP ta ruwaito a ranar Lahadi cewa matar ministan ta biyu da jikokinsa biyu ma an kashe su a harin.
An kai Camara asibiti a Bamako, amma ya rasu sakamakon raunukan da ya samu, a cewar Al Jazeera wacce ta ambato majiyoyi masu sahihanci.
A safiyar Lahadi, an girke babbar tawagar sojoji a bakin asibitin da ake kula da Camara, in ji AFP. Masu taimakonsa sun ƙaryata rahotannin da suka ce harin ya ji masa rauni.
Muhimmin jigo a gwamnati
Gwamnatin Mali ba ta fitar da wata sanarwa ta hukuma game da halin da Camara yake ciki a lokacin da ake wallafa wannan labarin ba.
Rahoton mutuwar Sadio Camara shi ne mafi girman asarar jami'in gwamnati a jerin hare-haren ta'addanci da ke ci gaba a Mali, waɗanda, a baya bayan nan, ke kai hari kan farar hula da jami'an soja.
Camara mutum ne mai ƙarfin faɗa-a-ji a cikin gwamnatin Mali, kuma yana da kyakkyawar dangantaka da Shugaban ƙasa, Assimi Goita.
Camara ya taɓa rike mukamin ministan tsaro na Mali sau biyu — na farko daga Oktoba 2020 zuwa Mayu 2021, sannan kuma daga Yuni 2021 har zuwa mutuwarsa da aka ruwaito a ranar 26 ga Afrilu, 2026.
Hare-haren da aka tsara su
Wannan babban soja da aka horar a Mali da Rasha ya rasu yana da shekaru 47.
A ranar Asabar an kai hare-haren ta'addanci da aka tsara a sassa daban-daban na Mali, inda birane da dama, ciki har da babban birnin ƙasar, suka fuskanci harin daga ‘yan ta’adda da ‘yan’a-ware.
Aƙalla mutane 16 ne suka rasa rayukansu a hare-haren, a cewar gwamnati. Majalisar Dinkin Duniya, da Tarayyar Afirka, da Turkiya sun yi Allah-wadai da hare-haren.
A ranar Lahadi an ɗan samu kwanciyar hankali, kodayake an ruwaito sabuwar fafatawa a garin Kidal da ke arewa. Rundunar sojoji tana yaki da Abzinawa 'yan’a-ware a can.
















