China ta bayyana ranar Laraba cewa tana "godiya mai yawa" ga ƙasashen Afirka bayan wasu daga cikinsu sun janye takardar izinin wucewa ta samaniyarsu, lamarin da ya katse shirin tafiyar shugaban Taiwan zuwa Eswatini, ƙasa ɗaya tilo mai alaƙar diflomasiyya da tsibirin a nahiyar.
China ta bayyana cewa Taiwan wani ɓangare ne na ƙasarta kuma ba ta yarda tsibirin mai mulkin kansa ya riƙa shiga cikin ƙungiyoyi na ƙasa da ƙasa ba da kuma tattaunawa da sauran ƙasashe.
An shirya Shugaban Taiwan Lai Ching-te zai kai ziyara Eswatini ne daga ranar Laraba domin bikin cika shekara 40 na hawa karagar mulkin Sarki Mswati na III da kuma bikin zagayowar ranar haihuwarsa ta 58.
Amma wasu ƙasashe — ciki har da Seychelles da Mauritius da kuma Madagascar — sun janye izinin wucewar Lai ta sararin samaniyarsu bayan "matsi mai yawa " da kuma tilastawa ta tattalin arziki daga China, kamar yadda wani jami’in Taiwan ya bayyana ranar Talata.
"Ƙasashen da lamarin ya shafa suna tabbatar da goyon baya ga manufa ta China ɗaya… bisa ɗabi’ar dangantaka ta ƙasa da ƙasa, China ta nuna godiya mai yawa," kamar yadda wani mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China ya bayyana a wata sanarwa.
"Babu wanda zai iya dakatar da tafiyar tarihi ta sake haɗa kan China ," in ji sanarwar da aka fitar a matsayin martani ga janye izinin.
Eswatini, wadda aka sani a baya da suna Swaziland, tana cikin ƙasashe 12 ƙawayen Taiwan da suka amince da iƙirarinta cewa ita ƙasa ce, bayan Beijing ta gamsar da sauran ƙasashen cewa su yanke alaƙar diflomasiyya da Taipei.
Wani mai magana da yawun gwamnatin Eswatini ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa ta yi "nadamar" cewa Lai ba zai kai ziyara ba , amma ya jaddada cewa koma-bayan "ba zai sauya matsayar dangantakarmu daɗɗɗiya da Jamhuriyar China (Taiwan) ba".














