| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Tinubu ya cim ma yarjejeniya da kamfanonin jiragen sama domin hana shirinsu na dakatar da aiki
Shugaba Bola Tinubu ya amince ya yafe wa kamfanonin jiragen sama wani bangare na basussukan da ake binsu, bayan da kamfanonin suka yi barazanar dakatar da dukkan zirga-zirgar jirage matukar ba a rage farashin man jirgi ba.
Tinubu ya cim ma yarjejeniya da kamfanonin jiragen sama domin hana shirinsu na dakatar da aiki
Kamfanonin jiragen saman Nijeriya sun ce farashin man jiragen sama ya tashi da fiye da kashi 300 a cikin makonni kaɗan / Reuters

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya bayyana a ranar Laraba cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da tsarin yafe wa kamfanonin jiragen saman gida wani bangare na basussukan da suke bin hukumomin sufurin jiragen sama. Wannan mataki ya biyo bayan nasarar tattaunawar da aka yi bayan kamfanonin sun yi barazanar tsagaita aiki saboda tsadar man jirgi da ta durkusar da su.

Kungiyar Masu Kamfanonin Jiragen Sama na Nijeriya (AON) ta yi barazanar dakatar da dukkan zirga-zirgar jirage daga ranar 20 ga watan Afrilu, matukar ba a rage farashin man jirgi ba.

Keyamo ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya bukaci a mika masa bukatar hakan a hukumance cikin gaggawa, inda shi da kansa zai tantance adadin kason da za a yafe daga cikin bashin.

Masu AlakaTRT Afrika - Kamfanonin jiragen saman Nijeriya sun yi barazanar dakatar da aiki saboda tashin farashin man jirgi



Haka kuma, gwamnati za ta kafa wani kwamiti da zai duba batun haraji da sauran kudaden da ake karba a kan tikitin jiragen saman gida, domin bayar da shawarar rage su don saukaka wa kamfanonin jiragen da ma fasinjoji.

Sakatariyar ma’aikatar man fetur, Patience Oyekunle, ta bayyana bayan kammala tattaunawar ranar Laraba cewa, dillalan man fetur za su zauna da jami’an gwamnati a ranar Alhamis don kokarin warware takaddamar da ake yi kan farashin man jirgin cikin hanzari.

Tsadar man jirgin da aka samu a duniya sakamakon yakin Iran ya girgiza masana’antun sufurin jiragen sama na duniya, wanda hakan ya tilasta wa kamfanoni kara kudin tikiti na zuwa-da-dawowa, takaita shirye-shiryen bunkasa ayyukansu, da kuma sake duba hasashensu na gaba.