Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya nemi majalisar dokokin ƙasar ta amince ya karɓo bashin $516m daga wani bankin Jamus domin gina sabuwar hanya da za ta haɗa arewa maso yammacin ƙasar da kudu maso yammacin ƙasar.
A wata wasiƙa da shugaban majalisar dattawan ƙasar ya karanta a zauren majalisar ranar Alhamis, Tinubu ya ce gwamnatinsa tana neman a ba da damar karɓo bashin ne daga wani babban banki na zuba jari, Deutsche Bank, yana mai ƙarawa da cewa bashin wani ɓangare ne na tsarin aron kuɗi na matsakaicin lokaci na gwamnatin ƙasar wanda ‘yanmajalisar suka amince da shi.
Bashin zai kasance wanda za a biya ne cikin shekaru tara ciki har da shekara uku na ɗaga ƙafa, kamar yadda Tinubu ya bayyana a wasiƙar.
Babbar hanyar da ta kai kimanin kilomita 1,000 za ta haɗa jihar Sokoto, a arewa maso yammacin Nijeriya da ta hanyar jihar Neja da Kwara da ke tsakiyar ƙasar zuwa garin da ke gaɓar teku na Badagry a jihar Legas, babban birnin kasuwancin ƙasar.
Alfanun babbar hanyar
Tinubu ya ce babbar hanyar za ta ƙarfafa hanyoyin zirga-zirga tsakanin arewaci da kudancin ƙasar da rage lokacin tafiya da kuma farashin dakon kaya da haɓaka cinikayya samar da abinci tare da inganta haɗin kan ƙasa.
A shekarar da ta gabata, Nijeriya ta karɓi bashin dala miliyan $747, daga bankuna ƙarƙashin jagorancin bankin Deutsche Bank, domin gina ɓangare na farko na babbar hanyar bakin teku ta kilomita 700.












