| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Trump ya fasa kai wa Iran hari da makamin nukiliya
Shugaban Amurka Donald Trump ya fasa yin amfani da makaman nukiliya kan kasar Iran, yana mai cewa Amurka ta “kassara” karfin sojin Iran.
Trump ya fasa kai wa Iran hari da makamin nukiliya
Trump ya ce Amurka tana da "cikakkiyar iko" kan mashigin tekun Hormuz, yana mai cewa sun rufe shi har sai an kammala tattaunawar. / Reuters

Shugaba Trump ya kawar da yiwuwar amfani da makamin nukiliya wajen yakar Iran, yayin da kuma ya nuna cewa kila Iran ta sake tattara makamanta a lokacin yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta mako biyu.

“A’a,” Trump ya ba wa wani dan jarida amsa a Fadar White House ranar Alhamis. “Me zai sa in yi amfani da makamin nukiliya alhali mun gama murkushe Iran gaba daya ba tare da shi ba?”

Ya kara da cewa, “Kada a taba barin kowa ya yi amfani da makamin nukiliya.”

Trump ya kuma bayyana cewa kila Iran ta dan sake tara makamanta “kadan” a lokacin hutun yaki na mako biyu, amma ya kara da cewa Amurka za ta iya lalata hakan cikin kankanin lokaci.

“Sojojin ruwansu sun kare. Sojojin samansu sun kare, kariya daga harin sama duk babu su... watakila sun dan kara wasu abubuwan a cikin hutu na mako biyu, amma za mu ruguza hakan cikin rana daya idan har sun yi hakan,” in ji Trump.

“Ina son kulla yarjejeniya mafi kyau. Zan iya kulla yarjejeniya a yanzu haka... amma ba na son yin hakan. Ina so in samu wadda za ta dore har abada,” in ji Trump.

A ranar 7 ga watan Afrilu, Trump ya fitar da wata barazana ga Iran cewa “dukan wata wayewa za ta mace a daren yau, wadda ba za a taba dawo da ita ba,” amma cikin ’yan sa’o’i ya amince da tsagaita bude wuta wanda ya tsawaita tun lokacin da aka kaddamar da yakin da Amurka da Isra’ila ke yi.

Trump ya kuma ce Amurka tana da “cikakken iko” a Mashigar Hormuz, inda ya ce sun rufe shi har sai an kammala tattaunawa.

“Sun zo wurinmu, suka ce, ‘Za mu amince mu bude mashigar.’ Kuma dukan mutane na sun yi farin ciki, in ban da ni,” in ji Trump.

“Na ce, ‘Dakata tukunna, idan muka bude mashigar, hakan na nufin za su rika samun dala miliyan 500 a kowace rana.’ Ba na son su samu dala miliyan 500 a rana har sai sun sasanta wannan matsalar. Don haka ni ne na sa aka rufe mashigar.”

Game da farashin man fetur, Trump ya gaya wa manema labarai cewa ya kamata Amurkawa su sanya ran biyan farashi mafi girma “na dan lokaci.” Yakin da Amurka da Isra’ila suke yi da Iran ya yi sanadin tashin farashin makamashi a duniya.

Trump ya shaida wa manema labarai cewa yana son ganin Iran “ba tare da makamin nukiliya ba wanda zai yi kokarin tayar da daya daga cikin biranenmu ko kuma tayar da daukacin Gabas Ta Tsakiya.”

Ita dai Iran ta musanta cewa tana neman mallakar makamin nukiliya, kuma hukumar sa ido kan makaman nukiliya ta MDD ta ce kasar ba ta yi kusa da kera bam nukiliya ba, kafin barkewar yakin.

Amurka ce kadai kasa da ta taba amfani da makaman nukiliya a lokacin yaki, inda ta ruguza biranen Hiroshima da Nagasaki na kasar Japan a karshen Yakin Duniya na Biyu, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 214,000.

Abokiyar kawance ga Amurka, wato Isra’ila, an san ta sosai da mallakar makaman nukiliya, kodayake ba ta fito fili ta amince da hakan ba.