| Hausa
NIJERIYA
1 minti karatu
Aƙalla mutum 60 aka kashe a hare-hare daban-daban a arewa maso yammacin Nijeriya cikin mako guda
‘Yan bindiga sun kashe a kalla mutane 60 a yankina masu nisa daban-daban a arewa maso-yammacin Nijeriya a makon nan, kamar yadda kungiyoyin jinkai suka bayyana a ranar Laraba.
Aƙalla mutum 60 aka kashe a hare-hare daban-daban a arewa maso yammacin Nijeriya cikin mako guda
A kalla mutane 60 aka rawaito an kashe a hare-hare daban-daban a arewa maso-yammacin Nijeriya. / Reuters / Reuters
6 awanni baya

‘Yanbindiga sun kashe a kalla mutane 60 a yankuna masu nisa daban-daban a arewa maso-yammacin Nijeriya a makon nan, kamar yadda kungiyoyin agajin jinkai suka bayyana a ranar Laraba.

Hare-haren sun shafi jihohi biyu makotan juna na Kebbi da Naija, a kauyuka 10, in ji malaman addini da kungiyoyin agajin jinkai kanar yadda AFP suka rawaito.

Wani rahoton halin da ake ciki da ya bayar da bayanan majiyoyin kungiyoyin bayar da agaji da wata kungiyar al’umma, an kashe mutane 20 a ranar Talata a harin da aka kai Erena, a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Wani rahoton jami’an soji kan sha’anin tsaro ya bayyana cewa maharan ‘yan bindiga ne da ke dauke da manyan makamai da suka afka wa sansanin soji.

Daruruwan mutane sun tsere

‘Yan sanda sun tabbatar da harin na Shiroro, suna masu kara da cewar “an kashe ‘yan sintiri biyu da direbansu da suka fito daga dakarun tsaron hadin gwiwa.”

A jihar Kebbi mai makotaka, wani malamin addini ya ce yana mai iya tabbatar da an kashe mutane 24 “amma daga rahotannin da muka samu yau an kashe sama da mutane 40”.