Duk da yadda yaƙin Iran ke shafar hada-hadar ciniki da tattalin arziƙin duniya, Nijeriya za ta samu haɓakar tattalin arziƙi a wannan shekarar, kamar yadda Bankin Duniya ya ambata.
Ranar Talata ne Bankin Duniya ya sanar da wannan a Abuja, babban birnin Nijeriya, yana cewa tattalin arziƙin ƙasar zai nuna juriya tare da haɓaka a rabin farko na shekarar 2026.
Juriyar da Bankin ya ambata ta ƙunshi kaucewa ƙaruwar farashin mai, hauhawar farashin kayan masarufi, waɗanda suke barazanar tsuke kuɗin-shiga da rage saurin yaƙi ta talauci.
Babban mai nazarin tattalin arziƙin Nijeriya a Bankin Duniya, Fiseha Haile, ya bayyana cewa ana samun ƙaruwar hada-hada kasuwanci a Nijeriya, duk da yaƙin Iran da Amurka-Isra’ila ya haddasa ƙarin farashin mai.
Haile ya ce, "Duka-duka hada-hadar cinikayya tana ta ƙaruwa cikin ‘yan watannin nan, wanda ke nuna an bijirewa mummunan tasiri kan haɓaka. Amma duk da haka ana jin raɗaɗin ta hanyar hauhawar farashi".
Tuni dai gwamnatin Shuagaba Bola Tinubu ta cire tallafin man fetur, da rage darajar naira da sauya tsarin haraji, da nufin daidaita tattalin arziƙi.
A watan Fabrairu, hauhawar farashi ya ragi zuwa kashi 15.06%, wanda ya taɓa kai wa kashi 33% a Disamban 2024.
Haka nan farashin mai ya hau da kashi 50% yayin yaƙin Iran, wanda kuma ya bayu zuwa ƙaruwar farashin sufuri, kayan abinci, da ayyukan samar da kaya.









