| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Iran ta sanar da bude Mashigar Ruwa ta Hormuz ga dukkan jiragen ruwan duniya
Tuni Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi wa Iran din godiya kan matakin nata, a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, inda ya ce: “Iran ta sanar da cewa ta buɗe Mashigar Hormuz ga dukkanin jirage. Nagode!”
Iran ta sanar da bude Mashigar Ruwa ta Hormuz ga dukkan jiragen ruwan duniya
Iran ta sanar da bude Mashigar Ruwa ta Hormuz ga dukkan jiragen ruwan duniya / Reuters
kwana ɗaya baya


Iran ta sanar da buɗe Mashigar Ruwa ta Hormuz ga dukkan jiragen kasuwanci na duniya domin su rika wucewa har zuwa ƙarshen tsagaita wutar da aka cimma.

Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi ne ya sanar da hakan ne a saƙon da ya wallafa a shafukan sada zumunta a ranar Jumma'a, inda ya ce: “A cikin tsarin tsagaita wuta a Lebanon, an ayyana cewa dukkan jiragen kasuwanci za su ringa wucewa cikin ‘yanci ta Mashigar Hormuz har zuwa ƙarshen wannan tsagaita wuta.”

Ya ƙara da cewa wannan zirga-zirga za ta gudana ne ta wata hanya da aka tsara tun da farko, wadda Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Iran ta sanar.

A wani ɓangaren kuma, kafar labarai ta Axios ta ruwaito jami’an Amurka na cewa ana tattaunawa tsakanin Amurka da Iran kan wani shiri mai shafuka uku domin kawo ƙarshen yaƙin.

Rahoton ya ce ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da ake tattaunawa a kai shi ne yiwuwar Iran ta miƙa sinadarin uranium ɗinta , a musayar Amurka ta saki dala biliyan 20 na kuɗaɗen Iran da aka daskarar.

Tuni Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi wa Iran din godiya kan matakin nata, a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, inda ya ce: “Iran ta sanar da cewa ta buɗe Mashigar Hormuz ga dukkanin jirage. Nagode!”

Matakin buɗe mashigar Hormuz na daga cikin muhimman abubuwan da ake ganin zai rage tashin hankali a yankin, tare da taimakawa harkokin kasuwanci na duniya, musamman ma a fannin man fetur.

Iran ta yi fatan samun dala biliyan $15B daga kuɗin wucewa ta Mashigar Hormuz a takardar kuɗin ƙasar

Tun da fari a ranar Alhamis, wani ɗanmajalisar dokokin Iran ya ce shirin tabbatar da ikon Iran a hukumance a kan Mashigar Ruwan Hormuz na da zummar ƙarfafa kuɗin ƙasar, rial, ta hanyar tsarin kuɗi na yanki, in ji kamfanin dillancin labaran ISNA da ƙasar ke da ƙwarya-ƙwaryar iko a kansa.

Ahmad Naderi, wani ɗanmajalisa da ke cikin kwamitin da ke sa ido, ya ce shirin na ganin kuɗaɗen shiga da ke da alaƙa da wucewar jiragen ruwa za a biya su ne a rial, yana mai bayyana shi a matsayin wani mataki da zai ƙarfafa tasirin ƙasar a kasuwancin yankin.

Ya kuma yi kiyasin cewa kuɗaɗen shiga daga tafiyarwa da kuma gudanar da lamarin kaikomon jiragen ruwa a mashigin mai muhimmanci zai kama daga dala biliyan $10 zuwa dala biliyan $15 a ko wace shekara, yana mai gargaɗin cewa kuɗaɗen suka zarce haka waɗanda ke yawo a cikin wasu sharhi an “kanbama ” su ne kuma ba daidai hakan yake da gaskiyar abin da ke faruwa ba.

Naderi, wanda ke wakiltar Tehran a majalisar dokokin, ya yi gargaɗin kan abin da ya kira siffatanta kuɗaɗen shiga Hormuz da “son zuciya da abin da ya saɓa wa zahiri” , yana mai cewa irin waɗannan tunanin suna iya taimaka wa matsin tattalin arziki da zamankewa na abokiyar hamayyar ƙasar .

Jigilar kayayyaki ta Mashigar ruwan Hormuz ya samu tsaiko sosai tun lokacin da yaƙin Amurka da Isra’ila kan Iran ya fara ranar 28 ga watan Fabrairu, inda tashin hankali ke daɗa ƙamari bayan an yi shelar ƙawanyar sojin ruwa da Amurka ta ƙaƙaba bayan tattaunawar Washington da Tehran ta ci tura a Islamabad.

Kimanin kashi 20 cikin 100 na dukkan man duniya na wucewa ne ta mashigin ruwan a ko wace rana, kuma ƙarin rashin tsaro ya tura farashin mai sama, tare da farashin jigilar man da na inshora.