Falasɗinawa a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye da kuma tsakiyar yankin Gaza da aka yi wa ƙawanya, na kaɗa ƙuri’u a rumfuna a zaɓen ƙananan hukumomi. Wannan shi ne zaɓe na farko tun bayan kisan kiyashin da Isra'ila ta ƙaddamar a Gaza, wanda ke gudana a cikin wani yanayi na ƙuntataccen fagen siyasa da kuma rashin ƙwarin gwiwa daga jama'a.
Kusan mutane miliyan 1.5 ne suka yi rajistar zaɓe a Gabar Yamma, sannan wasu mutane 70,000 a yankin Deir al Balah na Gaza a ranar Asabar, kamar yadda Hukumar Zaɓe ta Hukuma da ke Ramallah ta bayyana.
Yawancin jerin 'yan takarar na da alaƙa ne da jam'iyyar Fatah ta shugaba Mahmud Abbas ko kuma a matsayin masu zaman kansu. Babu wasu 'yan takara da ke da alaƙa da ƙungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas.
A mafi yawan biranen, 'yan takara masu samun goyon bayan Fatah za su fafata ne da 'yan takara masu zaman kansu waɗanda wasu ɓangarori kamar ƙungiyar "Popular Front for the Liberation of Palestine" ke jagora.
'Tsari Mai Sahihanci'
Mahmud Bader, wani ɗan kasuwa daga birnin Tulkarem da ke arewacin Gabar Yamma—inda wasu sansanonin 'yan gudun hijira biyu ke ƙarƙashin mamayar sojin Isra'ila sama da shekara guda—ya ce zai jefa ƙuri'a duk da cewa ba shi da wani babban fata na samun sauyi mai ma'ana.
"Mamayar (Isra'ila) ita ce ke mulkin Tulkarem. Wannan zai zama tamkar hoton nuna wa kafafen yaɗa labarai na duniya ne kawai — wai muna da zaɓe, jiha, ko 'yancin kai," kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Rumfunan zaɓe a Gabar Yamma za su kasance a buɗe daga ƙarfe 7:00 na safe (0400 GMT) zuwa 7:00 na yamma, yayin da a Deir al Balah za a rufe zaɓen da ƙarfe 5:00 na yamma domin sauƙaƙa ƙidayar ƙuri'u da hasken rana saboda rashin wutar lantarki a yankin da yaƙi ya daidaita, in ji hukumar zaɓen.
Wakilin Majlisar Ɗinkin Duniya, Ramiz Alakbarov, ya yaba wa hukumar bisa shirya "tsari mai sahihanci."
"Zaɓen ranar Asabar wata dama ce mai muhimmanci ga Falasdinawa don yin amfani da haƙƙinsu na dimokuradiyya a cikin wani lokaci mai matuƙar ƙalubale," in ji Alakbarov a cikin wata sanarwa.
'Tabbatar Da Wanzuwa'
Wani jami'i mai suna Fadi ya ce an zaɓi Deir al Balah ne saboda tana ɗaya daga cikin wuraren da jama'a "suka fi zama a wurarensu ba tare da an raba su da muhallansu ba" duk da kisan kiyashin da Isra'ila ta kwashe sama da shekaru biyu tana yi.
Farah Shaath, mai shekaru 25, ta bayyana farin cikinta na jefa ƙuri'a a karon farko.
"Kodayake bai yi kama da kowane irin zaɓe a duniya ba, amma tabbaci ne na ci gaba da wanzuwarmu a yankin Gaza duk da komai," kamar yadda ta shaida wa AFP.
Kakakin hukumar zaɓen, Fareed Taamallah, ya shaida wa AFP cewa sun ɗauki ma'aikatan zaɓe daga ƙungiyoyin sa-kai sannan sun yi hayar da "wani kamfanin tsaro mai zaman kansa don tsare cibiyoyin zaɓe" a zaɓen na Gaza.


















