| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
’Yanbindiga sun kashe fararen-hula 16 kusa da iyakar Nijar da Mali
Wannan hari ya zo ne bayan an kwashe watanni ana samun kwanciyar hankali a yankin Banibangou, inda ’yanta’adda suka Ƙaddamar da jerin munanan hare-hare kan fararen-hula tsakanin shekarar 2021 zuwa 2023 a ƙauyuka, gonaki, hanyoyi, har da masallatai.
’Yanbindiga sun kashe fararen-hula 16 kusa da iyakar Nijar da Mali
Yan bindiga sun kashe fararen hula a kan iyakar Nijar da Mali / Reuters

Wasu ’yanbindiga sun kashe fararen-hula 16 a wani harin kwanton-ɓauna da suka yi wa ayarin motocin ɗaukar kaya a yammacin Jamhuriyar Nijar, kusa da iyakar ƙasar da Mali, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana a ranar Lahadi.

Wasu majiyoyi a Nijar sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Lahadi cewa, maharan sun kashe mutanen ne a cikin wannan mako bayan sun tare ayarin motocin a gundumar Banibangou da ke yankin Tillabéri, yankin da yake fama da ’yanta’adda masu alaƙa da ƙungiyar Al-Qaeda.

“An tsayar da manyan motoci biyar masu ɗauke da fasinjoji da kaya a yammacin ranar Juma’a. Maharan sun kashe maza 16, amma suka ƙyale mata,” in ji wani mazaunin Banibangou yayin tattaunawa da AFP.

Mutumin ya ƙara da cewa motocin sun taso ne daga birnin Yamai a kan hanyarsu ta zuwa Tizigorou, kuma harin ya auku ne a wani yanki na “hamada” mara nisa daga garin.

Sace motoci

Wani mazaunin maƙociyar gundumar Tondikiwindi ya shaida wa AFP cewa mutanen na kan hanyarsu ta zuwa kasuwar mako-mako, kuma “mata ne kaɗai aka bari da rai.” Daga cikin mutane 16 da aka kashe, har da wasu “yan kasuwa na yankin.”

Maharan, waɗanda har yanzu ba a san ko su wane ne ba, sun yi awon-gaba da motoci uku maƙare da kaya, sannan suka ƙona mota ɗaya.

Wannan hari ya zo ne bayan an kwashe watanni ana samun kwanciyar hankali a yankin Banibangou, inda ’yanta’adda suka ƙaddamar da jerin munanan hare-hare kan fararen-hula tsakanin shekarar 2021 zuwa 2023—a ƙauyuka, gonaki, kan hanyoyi, har ma da cikin masallatai.

Tallafi daga fararen-hula

A ranar Jumma’a, gwamnatin Nijar ta sanar da cewa za ta amince da kafa dakarun sa-kai na fararen-hula domin taimaka wa rundunar sojin ƙasar wajen yaƙi da ƙungiyoyin ta’addanci.

“Mun yi nasarar samar da tsaro. Jaruman dakarunmu na tsaro da kariya suna da iko a ƙasa, duk da hare-haren da ƙasarmu ta fuskanta,” in ji Shugaba Abdourahamane Tiani a makon da ya gabata.

Baya ga wannan yanki na yamma, Jamhuriyar Nijar na fuskantar hare-hare daga ’yanta’addan Boko Haram a kudu maso gabashin ƙasar.

Rumbun Labarai
Ministan Tsaron Mali Camara ya yi musayar wuta da 'yanta'adda kafin a kashe shi
An kashe Ministan Tsaron Mali a harin ta'addanci: Al Jazeera
Turkiyya ta yi Allah wadai da hare-haren ta’addanci da aka kai a kasar Mali
WHO ta amince da maganin maleriya na jarirai na farko
An bayar da rahoton fashewar bama-bamai da ƙarar bindigogi a kusa da barikin sojin Mali mafi girma
Dangote ya sha alwashin gina matatar mai a Gabashin Afirka tare da goyon bayan shugabanni
Aƙalla mutane 518 ne suka mutu a zanga-zangar bayan zaɓe a Tanzania: Bincike
Makomar abinci a Afirka: Bankin Duniya na fuskantar matsin lamba don ba wa ƙananan manoma fifiko
Nijar ta kori ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba, NGO kusan 3,000 a kokarin ‘tsaftace ayyukansu’
China ta 'gode wa' ƙasashen Afirka da suka ƙi amincewa jirgin shugaban Taiwan ya wuce ta samaniyarsu
Yadda Ghana ke samun nasarar ɗaɓɓaka Kishin Afirka
Me Faransa ke nema a Kenya bayan korar ta daga Sahel?
Morocco ta saki magoya bayan Senegal da aka ɗaure kan hargitsin wasan ƙarshe na AFCON
Ziyarar Afirka: Fiye da mutum 500,000 ake sa ran sun halarci taron ibada na Fafaroma Leo a Kamaru
Yara mata ne suka fi cutuwa daga yaƙin Sudan da aka manta da shi
Fafaroma Leo ya nufi Kamaru ƙasa ta biyu a ziyararsa ta Afirka
Yaƙi ya jefa fiye da kashi 70 cikin 100 na 'yan ƙasar Sudan cikin talauci, in ji MƊD
Yadda yakin Iran ke shafar tattalin arziki, yanki da siyasar Afirka
Za a cim ma yarjejeniyar bututun gas na Nijeriya-Maroko kan biliyan $25 a bana: Jami'i
Fafaroma Leo ya fara ziyararsa ta farko zuwa Afirka