| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Nijar ta ƙaddamar da sabon katin ɗan ƙasa na zamani mai tambarin AES
Manyan jami’an ‘yansandan ƙasar ne suka miƙa masa katin, wanda ake kira CNIB-AES, a gaban ministoci da mambobin majalisar mulki, lamarin da ya nuna fara aikin rajistar jama’a a fadin ƙasar domin maye gurbin tsofaffin katunan takarda.
Nijar ta ƙaddamar da sabon katin ɗan ƙasa na zamani mai tambarin AES
Shugaban Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya karɓi sabo katinsa na ɗan ƙasa / Nigeria Presidency

Shugaban Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, a ranar Juma’a ya ƙaddamar da sabon tsarin katin shaidar zama ɗan ƙasa na zamani (biometric) bayan karɓar katin farko a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Niamey.

Manyan jami’an ‘yansandan ƙasar ne suka miƙa masa katin, wanda ake kira CNIB-AES, a gaban ministoci da mambobin majalisar mulki, lamarin da ya nuna fara aikin rajistar jama’a a fadin ƙasar domin maye gurbin tsofaffin katunan takarda.

Hukumomi sun ce sabon katin na daga cikin ƙoƙarin Ƙungiyar Ƙasashen Sahel na daidaita takardun shaida da na tafiye-tafiye, inganta tsaro da sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a tsakanin ƙasashen mambobi.

Jami’ai sun bayyana wannan shiri a matsayin wani babban mataki na zamantar da tsarin katin, inda ake sa ran sabon tsarin zai ƙarfafa tantance mutane da kuma rage yin na bogi.

Ana sa ran fara gwajin samar da katin a watan Afrilun 2026, kafin a fara rabon katunan ga jama’a gaba ɗaya. Katin zai kasance ga ’yan ƙasa masu shekaru 15 zuwa sama, sannan yana da wa’adin shekara biyar zuwa sama, kuma yana ɗauke da matakan tsaro na zamani don kare bayanan mutane.

Gwamnati ta ce wannan shiri ya biyo bayan watanni na shirye-shirye, ciki har da yarjejeniyoyi da kamfanonin fasaha domin samar da kayayyakin aiki na rajistar katin na zamani da kuma kula da bayanai cikin tsaro. Ana kuma sa ran gina cibiyar bayanai ta zamani da tsarin tabbatar da sahihanci mai ƙarfi.

Hukumomi sun ƙara da cewa sabon katin zai taimaka wajen ƙarfafa tsaro a ƙasa da ma yankin gaba ɗaya, ta hanyar samar da ingantacciyar hanyar tantance ’yan ƙasa, musamman a yankin da ke fuskantar matsalolin tsaro da barazanar ƙetare iyakoki.

An ƙera katin CNIB-AES da robar polycarbonate mai inganci, wanda ya dace da ƙa’idojin ƙasa da ƙasa, inda jami’ai suka ce wannan mataki na nuna gagarumin ci gaba na zamani da inganta tsarin rajistar jama’a a Nijar.

 

Rumbun Labarai
Ministan Tsaron Mali Camara ya yi musayar wuta da 'yanta'adda kafin a kashe shi
An kashe Ministan Tsaron Mali a harin ta'addanci: Al Jazeera
Turkiyya ta yi Allah wadai da hare-haren ta’addanci da aka kai a kasar Mali
WHO ta amince da maganin maleriya na jarirai na farko
An bayar da rahoton fashewar bama-bamai da ƙarar bindigogi a kusa da barikin sojin Mali mafi girma
Dangote ya sha alwashin gina matatar mai a Gabashin Afirka tare da goyon bayan shugabanni
Aƙalla mutane 518 ne suka mutu a zanga-zangar bayan zaɓe a Tanzania: Bincike
Makomar abinci a Afirka: Bankin Duniya na fuskantar matsin lamba don ba wa ƙananan manoma fifiko
Nijar ta kori ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba, NGO kusan 3,000 a kokarin ‘tsaftace ayyukansu’
China ta 'gode wa' ƙasashen Afirka da suka ƙi amincewa jirgin shugaban Taiwan ya wuce ta samaniyarsu
Yadda Ghana ke samun nasarar ɗaɓɓaka Kishin Afirka
Me Faransa ke nema a Kenya bayan korar ta daga Sahel?
Morocco ta saki magoya bayan Senegal da aka ɗaure kan hargitsin wasan ƙarshe na AFCON
Ziyarar Afirka: Fiye da mutum 500,000 ake sa ran sun halarci taron ibada na Fafaroma Leo a Kamaru
Yara mata ne suka fi cutuwa daga yaƙin Sudan da aka manta da shi
Fafaroma Leo ya nufi Kamaru ƙasa ta biyu a ziyararsa ta Afirka
Yaƙi ya jefa fiye da kashi 70 cikin 100 na 'yan ƙasar Sudan cikin talauci, in ji MƊD
Yadda yakin Iran ke shafar tattalin arziki, yanki da siyasar Afirka
Za a cim ma yarjejeniyar bututun gas na Nijeriya-Maroko kan biliyan $25 a bana: Jami'i
Fafaroma Leo ya fara ziyararsa ta farko zuwa Afirka