Daga Abdalftah Hamed Ali da Sarah Khamis
Yaƙin Sudan, wanda ya ɓarke a watan Afrilun 2023, ya jefa ƙasar cikin mummunan rikicin siyasa, da koma bayan tattalin tattalin arziki da jin kai. Duk da girman ibtila'in, ƙasar na gwagwarmayar janyo hankulan duniya da kafafan yada labarai na kasa da kasa, ba kamar sauran rikicin da ake ci gaba da yi a Gabas ta Tsakiya ba, ciki har da Gaza da Lebanon, da ma na baya-bayan nan Siriya.
Ƙarfin rikicin Sudan da halin da ake ciki da tasirin da yake da shi a yankin da ma duniya baki daya, abu ne da ya zama dole a kalle shi da idanuwan basira kuma cikin tsanaki. Tsawon lokaci, akwai babban gibi a yadda kafafen yada labarai na duniya ke dauko labarai game da Sudan. Me ya sa aka bar hakan na faruwa, kuma me za a yi don magance matsalar?
Mummunan halin jin kan bil'adama a Sudan
Sama da mutane miliyan 14 - kamar dai kashi 30 na jama'ar Sudan - sun rasa matsugunansu tun watan Agustan 2023, ciki har da mutum miliyan 11 a cikin gida da milyan 3.1 da suka gudu zuwa kasashe makota, in ji Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta MDD.
Anihini abin da ke girgiza kwakwalwa shi ne sama da rabin jama'ar Sudan (Kashi 53) na wadanda aka tsugunar yara ne kanana 'yan kasa da shekaru 18. Rikicin ya jefa 'yan kasar Sudan miliyan 130 cikin halin neman taimakon jin kai, inda yunwa ke addabar su musamman a sansanin ZamZam da ke Dafur ta Arewa, in ji hukumomin Majalisar Dinkin Duniya.
Wadannan ba alkaluma ba ne kawai da za a yi watsi da su, amma gaskiyar ita ce; alkaluman na bayyana girman rikicin da ke azabtar da miliyoyin mutane, wanda gaza tsagaita wuta yake kara ta'azzarawa inda kuma hankalin kasashen duniya ke kara barin wajen.
Mayakan RSF da tun asali gwamnatin Sudan ta kafa wanda suke masu hatsari - na da hannu a ta'annati da dama da aka yi. Barnar da suka yi ta hada da kashe fararen hula, da yi musu fyade, da rikicin kabilanci da amfani da yunwa a matsayin makami da sauran keta hakkokin ɗan'adam.
A farkon watan Disamban 2024, aƙalla mutane 127 - mafi yawan su fararen hula - aka kashe a cikin kwanaki biyu da aka dauka ana ruwan bama-bamai, wanda hakan ya zama lamari mafi muni na kashe rayuka a 'yan watannin nan, kamar yadda masu kare hakkokin dan adam suka bayyana.
Wadannan munanan ayyuka wani bangare ne na gangamin da ake yi na yakar wasu kabilu, misali a Masalit, wanda masu sanya idanu na kasa da kasa suka yi gargadin cewa zai iya zam laifin zarafin ɗan'adam. Waɗanda suka tsira a Darfur sun bayyana mummunan halin da suka shiga bayan kona kauyukansu, aka tarwatsa danginsu tare da cin zarafin mata.
An kuma yi amfani da yunwa a matsayin makami a yakin. An zargi RSF da aikata munanan kisa tun bayan barkewar rikicin a 2023, inda aka samu rahotanni da yawa da ke bayyana yadda suka yi amfani da yunwatarwa a matsayin makamin yakar fararen hula da suka tirje da kuma samun iko a kan su.
Yadda 'yan tawayen suka hana a kai kayan abinci na agaji zuwa yankunan da yunwa ke addaba ya jefa miliyoyin mutane cikin yunwa. A sansanoni irin su Zamzam, dubunnan daruruwan fararen hula na fuskantar yunwa inda aka gaza kai musu abinci da magunguna.
UNICEF ta ƙiyasta cewa dubunnan ɗaruruwan yara za su wahala sosai saboda tsananin ƙarancin abinci a wannan shekarar, suna masu bayyana tsananin ibtila'in. Misali, a sansanin 'yan gudun hijira na Zamzam, kusan kashi ɗaya cikin huɗu na yara ƙanana da aka tantance na ɗauke da cutar yunwa mai tsanani, in ji likitocin da suke ba da agaji na ƙasa da ƙasa wato MSF.
Duk da tsananin wannan rikici, rikicin Sudan na ta ƙoƙarin janyo hankalin kafafan watsa labarai na duniya. Wahalhalun da ake ci gaba da sha sun zama ba a ganinsu saboda wasu rikice-rikicen yankuna daban, inda aka bar miliyoyin 'yan Sudan ba tare da tallafi da taimakon kayayyakin da suke tsananin buƙata ba. Ana buƙatar babban yunkuri na bayar da fifiko ga halin da Sudan ke ciki tare da taimaka wa waɗanda lamarin ya rutsa da su a matakin ƙasa da ƙasa.
Rashin zaman lafiya a yankin da tasirinsa ga sauran yankuna
Yaƙin Sudan ba wai ibtila'i ne na ƙasa kawai ba; wani babban rikici ne da ke addabar Yankin Kusurwar Afirka. Masu neman mafaka da ke guje wa rikicin sun cika ƙasashe maƙota, da suka hada da Chadi da Masar, da Sudan ta Kudu.
An lalata hanyoyin kasuwanci da ke da muhimmanci ga Gabashin Afirka da Sahel, kuma cibiyoyin kayan amfanin gona irin su El Gezira ma sun lalace, sun kawo matsalar abinci a yankunan. A yayin da hakan ke faruwa, yadda RSF ke shiga ayyukan fasa-ƙauri da safarar mutane da makamai, ya sake munana yanayin tsaro a yankin. Idan ba a tsananta bincike ba, Sudan na kan hatsarin zama cibiyar aikata muggan laifuka da za su hana gudanar da shugabanci da lalata tsaro a yankin.
Baya ga munanan ta'annatin da suke aikatawa, mayakan RSF na nuna alamun rauni a cikin gida. Yadda a baya-bayan nan manyan kwamandoji da masu bayar da shawara suka ɓalle na nuni ga samun baraka a rafiyarsu, da kuma taɓarɓarewar ƙarfin gwiwa a tsakanin manyan mayaƙan ƙungiyar.
A lokaci guda, rundunar sojin Sudan ta mayar da hankali ga kai manyan hare-hare da suka kwato yankuna a Khartoum da Sinar masu muhimmanci. Wannan abu ya lalata shirin RSF da yadda suke samun kayan aiki, inda suka koma ga kare kai.
Ga ƙasashen duniya da ke goyon bayan RSF, wannan ci gaba na sanya musu damuwa da ƙalubale. Ci-gaba da taimaka wa ɓangaren da ake ci-gaba da yi wa kallon wanda ya gaza marar halasci ba iya rashin nasara ke kawo wa ba, har ma da zubar da mutunci.
Ƙarfin RSF da ke dusashewa da yadda ake ware ta daban na sanyawa tana ƙara zama wani nauyi ga masu tallafa mata, waɗanda nan da wani lokaci za su fuskanci ɓacin ran duniya saboda hannu a ayyukan kisan kiyashi.
Ba a bayar da rahotannin da suka kamata game da rikicin Sudan
Duk da wannan abu da ake gani marar daɗi, manyan kafafen watsa labarai ba sa ɗauko rahotanni daga Sudan yadda ya kamata, wanda abin damuwa ne matuka, kuma hakan na hana bayar da tallafi yadda ya kamata. Abubuwa da dama ne ke sanya shirun kafafen watsa labaran.
Da farko, sauran rikice-rikicen yankuna na jan hankalin kafafen watsa labarai na duniya tare da mamaye kanun labarai. Rikicin Ukraine, an dinga bayyana shi a matsayin rikicin ƙasashen duniya da ke da tasiri na kai tsaye ga Ƙasashen Yamma, shi ya sa yake mamaye kafafen watsa labaran.
Haka kuma, rikicin Gaza da ake ci gaba da yi na zuwa a shafukan farko na jaridu, saboda yadda yake da ɗanɗanon siyasa da tausayi a idanuwan jama'ar duniya. Na baya-bayan nan shi ne rikicin Lebanon da faɗuwar ba-zata da gwamnatin Assad ta yi a Siriya suma sun mamaye kafafen watsa labaran.
Wani abin mamaki kuma, ana bayyana yaƙin Sudan a matsayin rikicin yankin da ba shi da wani muhimmanci ga batutuwan siyasa na ƙasa da ƙasa.
Batu na biyu shi ne yadda aka hana 'yan jarida samun damar shiga Sudan. An tursasa wa 'yan ajrida da dama barin ƙasar, sun jefa rayuwarsu cikin haɗari suna neman maɓoya. RSF da wasu bangarorin na kai wa 'yan jarida hare-hare, suna hana su motsawa, tare gaza ba su wata kariya, ana watsi da dokar ƙasa da ƙasa da ta ce a dinga kare martabar 'yan jarida.
Kawo rahotanni daga Sudan na da hatsari, inda 'yan jarida ke fuskantar barazana, da garkuwa da su da tantancewa mai tsauri. ba sai ma an faɗa ba, RSF ba su da wani ra'ayi na bayar da dama a sanya ido kan ayyukan da suke yi, suna ta kawo yanayin da za a yi ta aikata ɓarna a duhu.
A ƙarshe, rashin masu bayar da rahotannin me ke wakana ya gurgunta yadda duniya ke bayar da labarai game da Sudan. 'Yan jarida na ƙasahen waje na fuskantar ƙalubalen shiga ƙasar. Rikicin da ke ƙara tsamari da yadda ba a samun damar shiga ƙasar na kawo naƙasun samun cikakkun bayanai na gaskiya. Wannan ya haifar da giɓin bayanai, wanda ya sanya da wahala a san gaskiyar me ke wakana a kan lokaci, da ma samar da cikakken rahoto.
Wani abu da ke ƙara ta'azzara wannan yanayi shi ne rikitaccen yanayin rikicin na Sudan, wanda ke kawo babban ƙalubale ga abin da kafafen watsa labarai za su faɗa. Ba kamar irin yaƙe-yaƙen da ake iya ganin wa ke kai hari wa ke shan wahala ba, rikicin Sudan ya ƙunshi wasu masu hannu na yankin, da ƙulla ƙawance, da wasu abubuwa da suke daƙile ɗauko rahotannin. Duk da haka, mummunan halin da mutane ke ciki na ƙara ta'azzara, wanda ke buƙatar kawo rahotanni na gaskiya da za su bayar da dama a fahimci lamarin.
Kokarin wayar da kan mutane game da Sudan kamar magana ne ga kurame. Babu wanda ya damu da yara da ke cikin yunwa ko kuma waɗanda ba su ji ba ba su gani ba da RSF ke karkashewa kowacce rana. An manta da Sudan baki ɗaya. Amma ba za mu dakata ba har sai duniya ta ji mu #KuSanyaIdanuKanSudan
Sakamakon da wannan giɓi na kafafen watsa labarai zai kawo na da muni. Shugabanni da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa na aiki da 'yan bayanai kaaɗn, wanda hakan ke kawo jinkiri ga matakan tallafi da za a su iya ɗauka don kuɓutar da rayuka.
Gangamin tallafin jin kai, ba ya samun kuɗaɗen da suka kamata, inda ake barin miliyoyin mutane babu abinci. A duk lokacin da aka bayar da wani tallafi ba ya isa, inda kashi 32 na dala biliyan 2.7 da MDD ke nema kawai aka iya tattarawa. Ƙungiyoyin tallafi na bayyana muhimmanci aiki tare da ƙungiyoyi na cikin gida, saboda babu alamun za a tsagaita wuta a ƙasar.
Wannan cakuɗaɗɗen yanayi mai muni na kawo tarnaƙi ga dukkan wani yunƙurin kuɓutar da jama'ar Sudan tare da kawo jinkiri ga duk wani mataki da ake ƙoƙarin dauka don warware rikicin.
Kira ga ɗaukar mataki
Kafafen watsa labarai na duniya na da muhimmiyar rawar takawa wajen isar da muryoyin jama'ar Sudan da yaƙi ya rutsa da su da kuma sanya wa a tuhumi masu hannu a rikicin. Domin magance wannan giɓi na dauko rahotanni, dole ne kafafen watsa labarai na ƙasa da ƙasa su bayar da fifiko ga yaƙin Sudan, su zuba jari wajen gudanar da zuzzurfan binciken 'yan jarida da nemo hanyoyi ingantattu na magance ƙalubalen.
Ta hanyar kawo wa duniya halin da Sudan ke ciki, kafafen watsa labarai na iya matsa lamba don ganin gwamnatoci da ƙungiyoyi masu zaman kansu da ƙungiyoyin agajin jin ƙai sun yi abin da ya kamata.
A lokaci guda, dole ne ƙasashen duniya su ƙara ƙarfafa matakin da suke ɗauka. Samar da tuddan mun tsira don samun damar kai kayan agaji ga yankunan da aka illata, kamar Darfur, fifiko ne da ake buƙata cikin gaggawa.
Ya kamata ƙoƙarin diflomasiyya ya mayar da hankali wajen ganin an tsagaita wuta da kuma goyon bayan matakan da ake ɗauka don warware rikicin tun daga tushe. Dole ne a ƙarfafa aiki da gaskiya, da suka hada da bincike mai zurfi daga ɓangaren Kotun Hukunta Manyan Laifuka, domin tabbatar da adalci ga jama'ar Sudan.
Sake zaɓar Trump na iya ta'azzara ƙalubalen da rikicin Sudan ke fuskanta. A loakcin mulkinsa na farko, Trump ya rungumi tsarin ba-ni-in-baka, tare da samun taimako nan da nan, inda ya kawo sasantawar Sudan da Isra'ila, shi kuma ya cire ƙasar daga jerin ƙasashe 'yan ta'adda.
Sabuwar gwamnatin Trump na iya amfani da wannan salo, ta bayar da fifiko ga buƙatu na gajeren lokaci, maimakon warware rikicin baki ɗaya. A yin da hakan ka iya kawo nasara ta gajeren lokaci da ma tsagaita wuta, tana kuma da hatsari saboda togace ƙoƙarin ƙasa da ƙasa na sake gina Sudan da kuma daƙile ƙoƙarin neman haƙƙi kan waɗanda suka aikata ta'annatin.
Ga Sudan, wannan na iya nufin taimako daga ƙasashen waje da za su bayar da fifiko ga buƙatun yankuna maimakon tallafin jin ƙai, wanda zai ƙara ta'azzara mummunan halin da ake ciki.
Abdalftah Hamed Ali ƙaramin jami'i ne a Cibiyar Harkokin Duniya ta Gabas ta Tsakiya, yana neman mafita mai dorewa ga gwamutsuwar makamashi, da yanayi, da sauyin ci-gaban al'umma don magance matsalolin yankin na Gabas ta Tsakiya.
Dr. Sahar Khamis ƙwararriya ce kan kafafen watsa labaran Musulmai da Larabawa, inda ta ƙware wajen rubutu da binciken ilimi. Babbar Jami'a a Cibiyar Harkokin Duniya ta Gabas ta Tsakiya, ta zama shugabar Sashen Sadarwa a Jami'ar Qatar kuma Farfesa ce da ta ziyarci Jami'ar Chicago. Ta haɗa hannu da wasu wajen rubuta litattafai da dama kan batutuwan Musulunci da gwagwarmayar siyasa, kuma ta yi rubutun litattafai a yarukan Turancin Ingilishi da Larabci. Dr. Khamis na kuma yin nazari da warwara a kafafen yaɗa labarai, mai jawabi a bainar jama'a. Tana gudanar da wani shirin rediyo a kowanne wata a "US Arab Radio" A lokacin sanyin 2023, an zaɓe ta a matsayin Shugabar Ƙungiyar Larabawa Masana Kafafen Yaɗa Labarai Mazauna Amurka.
Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar mahanga, da ra'ayoyin editocin TRT Afrika.