About 15% of the global trade, worth around $1 trillion goes through the Red Sea . Hoto: Reuters / Hoto: Reuters Archive

Daga Omar Abdel-Razek

Cigaba da samun rikicin soji a Bahar Maliya na sanya damuwa a makomar tattalin arziki da tsaro da muhalli na Afirka.

A yayin da wasu kasashen Afirka da ba su da yawa za su amfana, mafi yawan su kuma za su fuskanci tashin farashin kayayyaki da gurbacewar muhalli.

Kasashe biyar daga cikin takwas da ke da gaɓa da Bahar Maliya kasashen Afirka ne. Sai dai kuma, yadda kafafen yada labarai ke rawaito rikicin, ana mantawa da asarar da Afirka ke tafkawa daga rikicin.

Maimakon haka, sai aka mayar da hankali ga barazanar tattalin arziki da rikicin zai yi wa manyan kasashen duniya da masu sayen kayayyaki a Yammacin Duniyar, wanda hare-hare kan jiragen ruwa na dakon kaya a daya daga cikin manyan hanyoyin teku na duniya.

An fara rikicin a watan Nuwamba a lokacin da mayakan Houthi na Yaman suka fara harar jiragen ruwa da na dakon kaya da ke wucewa ta Mashigar Teku ta Bab al-Mandab mai fadin kilomita 32, da nufin mayar da martani ga yakin da Isra'ila ke yi a Gaza.

An tirsasa daruruwan jiragen ruwa na dakon kaya da mai su sauya hanya zuwa Afirka, wanda hakan ke kwara kwanaki 12 da nisan kilomita 6000 a tafiyar da suke yi.

Wannan na kara janyo tsadar mai da ta inshora, wanda a karshe dai daga aljihun masu sayen kayayyaki kudaden za su fito, kuma hakan barazana ce ga tattalin arzikin duniya.

An yi hasashen cewa kaso 15 na kasuwancin duniya da ya kai darajar dala tiriliyan ɗaya na giftawa ta Bahar Maliya, zuwa mashigar teku ta Suez da ke Masar.

Wannan ne ya sanya Masar zama a tsaka mai wuya a yayin da ake wannan rikici, duk da cewa Tekun Bahar Rum ce ke babbae hanyar da kasar ke samun kudadeb shiga.

A 2023 kadai, sama da dala biliyan 10 Mashigar Teku ta Suez ta bai wa tattalin arzikin Masar.

Sai dai kuma, alkaluma na baya-bayan nan da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar sun bayyana an samu raguwar kaso 42 na kudade da ake samu a watanni biyun da suka gabata, yanayi mara dadi da ka iya tabarbarewa idan har aka ci gaba da yakin.

Wannan lokaci ne mara dadi ga Masar, kasa mafi yawan jama'a a Gabas ta Tsakiya, kuma daya daga cikin manyan kasashen Afirka.

Tattalin arzikin Masar ya fuskanci matsalar karancin tsabar kudi wanda ke taimaka mata wajen biyan kudaden shigo da kayayyaki, sannan ya janyo daduwar bashin kasashen waje da ya haura dala biliyan $160.

Tsaron Tekun Bahar Maliya:

Amma tsaka mai wuyar da Masar ta shiga ta wuce ga batun tattalin arziki kawai.

Tarihi ya bayyana cewa, Tekun Maliya na da matukar muhimanci ga tsaron Masar, tun ma a zamanin Sarauniya Hatshepsut, a lokacin da ta fadada kasuwanci zuwa kasar Punt, Somalia a yau, a tsakanin 1479-1458.

A lokacin yakin watan Oktoban 1973, Masar ta rufe mashigar teku ta Bab al-Mandab don hana kai kayan soji ga Isra'ila.

Sai dai kuma, a yanzu Alkahira na yin kaffa-kaffa wajen amincewa da ayyukan sojin Yammacin duniya kan Houthi, wato farmakan da Amurka ke jagoranta, domin ta kaucewa zama wadda ta fahimci tushen rikicin ba - Yaki kan Gaza.

Kasashenmu na Afirka da ke d agaba da Bahar Maliya na fuskantar irin nasu kalubalen. Sudan na cikin yakin basasa, yayin da Somalia kuma ta so afkawa rikici da Ethiopea bayan da Ethiopia ta sanya hannu da Somaliland kan ayyukan soji.

Yarjejeniyar ta bawa Ehtiopia izinin shekara 50 na amfani da gabar Somaliland a nisan kilomita 20, inda ita kuma za ta amince da 'yancin kan kasar Somaliland.

Wannan abu da Ehtiopia ta yi ya janyoi mayar da martani daga bangarori daban-daban, ciki har da Masar, Eritrea, da Saudiyya, wand ahakan ke kara ta'azzara rikicin na Bahar Maliya.

A wannan hali da ake ciki a yanzu da irin sakamakon da zai haifar, ba a kallon kasashen Afirka da ke da gaba da Bahar Maliya, a lokacin da ake tattauna duk wani batu na tsaron mashigar tekun.

A kusan tsawon shekara 30, Tsaron Tekun Bahar Maliya ya fi karfin kasashen Afirka da ke da gaba da shi (Masar, Sudan, Somalia, Eritrea da Djobouti), wanda hakan ke sanya kasashe da dama shigo wa don samar da tsaro saboda ayyukansu na soji da kasuwanci a tekun.

Wannan rikici na yanzu na iya ta'azzara yanayin da ake ciki, inda ake sa ran kasashen duniya na iya hanyar magance rikicin don kawar da barazanar soji a Bahar Maliya, wanda daidai yake da matakan yaki da bulluwar 'yan fashin teku a Somalia.

Kadan na amfana, mafi yawa na asara

Tirsasawa jiragen ruwa su sayna hanyoyinsu na iya amfanar wasu tashoshin jiragen ruwa na dan lokaci a Afirka ta Kudu, Namibia da Mauritius, kamar yadda kamfanin safarar kaya a teku na A.P. Moller-Maersk A/S ya bayyana.

Jirgin dakon kaya a Cape Town Afirka ta Kudu. Hoto: Reuters

Amma kuma, kwararru na yin gargadin cewa matsalar da Afirka gaba daya ke fuskanta ta fi wannan amfani girma.

Kasashen Gabashin Afirka, da suka dogara kan hatsi da kayayyakin da ake dakko wa daga Turai da kasashen Baharul Aswad, na iya fuskantar babbar matsala, tare da tsadar kudin dakon kaya, wanda za a samu karin dala $8 a kowanne tan guda, kamar yadda Kungiyar Cinikayyar Hatsi ta Kasa da Kasa ta bayyana.

Asarar da Afirka za ta yi saboda rikicin Tekun Maliya na iya zarce ta tattalin arziki kawai, za kuma ta shafi gurbata muhalli.

Hatsarin yiwuwar zirarar mai sakamakon harin da z aa iya kai wa jiragen ruwan dakon man, na sanya barazana sosai ga harkokin teku a yankin.

Rayuwar cikin tekun Bahar Maliya, wadda ke da mhimmanci wajen samun abincin teku, na fuskantar hatsari.

Yawaitar manyan tankokin mai da ke kai komo a Afirka, na janyo dole a dinga tsayawa don shan mai ko satar sa.

Sai dai kuma, mafi yawan tashoshin jiragen ruwa na Afirka ba su da kyawawan kayan aiki da za su iya karbar irin wadannan jiragen ruwa, kuma suna fama da rashin kayan aiki da cunkoson jirage, kamar yadda Rueters suka rawaito.

Haka kuma, yanayin na kawo barazanar samun hatsarin jirage kamar zirarar mai ko nutsewar jirgi a teku.

Burbushin rikicin na Bahar Maliya ya tsallake kasashen da ke gaba da tekun, ya shafi dukkan nahiyar.

Ya kamata Tarayyar Afika ta yi amfani d ahanyoyin diplomasiyya da dama doon rage radadin da wannan barazana ka iya janyo wa, ta yadda abinci da tsaron muhallan Afirka ba za su zama a hannun manyan kasashen duniya ba.

Marubucin wannan makala, Omar Abdel-Razek, masanin zamantakewar jama'a kuma tsohon editan Sashen Larabci na BBC.

Togaciya: Ba lallai ra'ayin da marubucin ya bayyana ya zama ya yi daidai da ra'ayi ko manufofin dab'i na TRT Afirka ba.

TRT Afrika