'Yan Nijar sun dinga gudanar da zanga-zangar nuna kyamar Faransa bayan juyin mulki. / Hoto: Reuters

Daga Mohamed Guleid

Nan da wasu 'yan kwanaki za mu riski shekarar 2024. Ga nahiyar Afirka, hakan na nufin kunshin wasu kalubale da suke barazana ga ci gaba da zaman lafiyar nahiyar.

Wadannan matsaloli sun faru ne sakamakon al'amuran da ke faruwa a bangarori daban-daban na yankuna da ma duniya baki daya, tun daga rikicin Ukraine da Falasdinu, zuwa ga matsalar tattalin arzikin da ta afku saboda karin kudin ruwa da Amurka ta yi.

Dadin dadawa, matsalar sauyin yanayi da ke laɓe da yawan rikici tsakanin jama'a da fatan samun sabon salon rayuwa da mu'amala a Afirka na daga cikin wadannan kalubale.

Sai dai kuma, tattare da wadannan kalubale, akwai damarmaki na juriya da habaka da kawo sauyi.

Rikicin da ake yi a wurare masu nisa da Afirka kamar su Ukraine da Falasdinu sun yi tasiri a sha'anin tattalin arziki a duniya.

Duk da nisanta da juna da suka yi, kasashen Afirka sun tsinci kawunansu a yanayi na rikice-rikice.

Illar da za a samu a nan gaba za ta shafi gudanar da kasuwanci da farashin kayan masarufi da rashin tabbas a sha'anin tattalin arziki, wanda ke kara yawan kalubalen da kasashe suke fuskanta a yanzu haka.

Matakan da suka zama wajibi a dauka

Dadin dadawa, tashin dala a 'yan kwanakin nan, wanda kara yawan kudin ruwa ya janyo, ya kawo matsalar tattalin arziki ga Afirka da suka doga kan shigo da kayayyaki daga kasashen ketare.

Wannan tashi na dala farar daya ya janyo takura da matsin lamba ga kudaden kasashe, inda ake da damuwa game da tashin farashi da karyewar tattalin arziki, inda ake samun kalubalen samun ci gaba mai dorewa.

Nijeriya daya daga cikin da kudinsu ya karye sosai a 2023. Hoto: Reuters

Mummunan tasirin sauyin yanayi na ci gaba da illata nahiyar Afirka, misali shi ne na guguwar El Nino da ta tagayyara garuruwa da al'ummu da dama.

Kasashen Afirka, musamman wadanda ke yankunan da ke fuskantar barazana, suna bukatar wani shiri na gaggawa da zai sanya su saba da wannan sauyin yanayi.

Wannan na bukatar zuba jari a fannin samar da kayan more rayuwa da kuma rungumar tsarin da zai magance illar da sauyin yanayi da gurbatar muhalli za su janyo.

A yayin da ake fuskantar wadannan kalubale, rikicin cikin gida da rashin zaman lafiyar siyasa na ci gaba da addabar yankunan nahiyar daban-daban.

Nuna kyama ga Faransa

Mummunan yanayi na takaici da ake ciki a Kongo ya zama babban lamarin da ke tuna yadda rikicin siyasa ya cakude da na ma'adanan kasa suke addamar kasar, wanda hakan ke hana kasar samun zaman lafiya da cigaba.

Kasashen Afirka sun fuskanci munanan matsalolin da sauyin yanayi ya janyo. Hoto: Others

Duk da haka, a yayin d aake tsaka da fuskantar wadannan matsaloli, musamman a kasashe rainon Faransa da ke Yammaci da Tsakiyar Afirka, ana kallon akwai alamun samun habakar nahiyar ta hanyar sauya mata fasali.

Kira ga 'yancin shugabanci da sabunta hadin kai na da manufar sauya wannan yanayi, habaka cin gashin kan a fannin tattalin arziki da sake dawo da karsashen al'adu da sanin waye mutum shi kansa.

Raunin da kasashe ke da shi ne ya janyo rikici a kasashe rainon Faransa, mafi yawan wadannan kasashe na Yammacin Afirka, kuma suna yawan fama da rikicin siyasa da karyewar tattalin arziki da rashin adalci wajen samun arziki da batun shugabanci da sauran matsaloli.

Manyan dalilan da ke janyo matsalolin na da yawa, amma wadana aka fi sani su ne cin hanci da rashawa da raunanan hukumomi da rikicin kabilanci da gwagwarmayar neman mulki da 'yan siyasa ke yi.

Nijar

A Mali, Guinea-Bissau, da Burkina Faso, rikici na faruwa saboda irin wannan rauni na shugabanci, hukumomi da ba su da karfi, rikicin kabilanci da ta'addanci, wanda ke kuma janyo rikicin cikin gida da rigimar neman mulki.

Wadannan rikice-rikice na da tasiri har a wajen kasashen, suna bayar da gudunmowa wajen tabarbarewar tsaron yankunansu, illata kasashe makota, a wasu lokutan ma kan janyo rikicin 'yan gudun hijira.

Amfanin jama'ar Afirka

Albarkatun kasa na yawan janyowa ko ta'azzara rikici. Samun arziki da yawa, abu ne da yake da damar sanya kasa ta habaka tatalin arzikinta, amma sai yake janyo gogayyar mallaka da amfana da arzikin, rikici da yake-yake.

Rikici a wadannan yankunan na da tasiri kan tattalin arziki, yana hana a samu cigaba, yana hana masu zuba jari zuwa kasashen, yana rusa kasuwanci, da janyo rikicin jin kai.

Wadannan rikice-rikice sun karya tattalin arzikin kasashe, sun hana su habaka, sun kara yawan talauci da dogaro kan taimako daga kasashen waje.

Magance wadannan matsaloli na bukatar kokari sosai wajen karfafa shugabanci, samar da hukumomin da za su tafi da kowanne bangare, da kuma habaka tattalin arziki domin rage dogaro kan taimako daga waje.

Hadin kan yankuna da taimakon kasa da kasa na da muhimmanci wajen rage illar rikici a wadannan kasashe da Faransa ta yi wa mulkin mallaka, gudunmowar zaman lafiyar da za a samu ba a iya kasashen kadai ba ne, har ma da sauran kasashe makota na Afirka.

A yayin da wadannan ibtila'o'i ke afkuwa, jama'ar Afirka da ke da karancin shekaru sun zama wata babbar kadara - ribar jama'a da za su iya samar da cigaba da habakar tattalin arziki idan har aka yi amfani da su yadda ya kamata, ta hanyar ilmantarwa da smaar da ayyukan yi.

Dadin dadawa, yadda dimukuradiyya ke yaduwa da habaka a nahiyar na nufin samun sauyi mai kyau zuwa ga shugabancin da ke tafiya da kowa, sannan hakan na sanya 'yan kasa shiga harkokin siyasa da gudanarwa.

Cigaban fasaha

A yayin da Afirka ke tunkarar 2024, nahiyar na da wani babban abu da zai zama gadar isar ta ga cigaba; babban bambancin da ake da shi wajen cigaban fasahar zamani da kuma tasirin samar da abinci.

A yayin da mafi yawancin duniya suka rungumi fasaha don kawo sauyi a bangarori daban-daban, wasu kasashen Afirka da dama na sahun baya a wannan bangare.

Kananan kamfanunnukan Ghana na kan gaba a Afirka. Hoto: Reuters

Daya daga cikin bangarori masu muhimmanci da ake fuskantar tsananin wannan matsala shi ne zamanantar da smaar da kayayyaki, musamman a bangaren noma da kiwo.

Duk da wanzuwa kasar noma mai albarka, amma ba a iya amfana da wannan arziki wajen samar da abinci saboda gaza amfani da tsarin zamani wajen noma da kiwo.

Wannan bambanci ya bayyana karara a yayin da ya kasance kai da kai tare da matsalar samar da abinci da ta zama ruwan dare a kasashen Afirka da dama.

Rashin iya amfani d akasar noma mai albarka yadda ya kamata don samar da abinci isasshe na kara ta'azzara matsalar nahiyar wajen fuskantar karancin abinci.

Miliyoyin mutane a Afirka na fuskantar matsaloli inda suke dogaro kan taimako da tallafi daga kasashen wajen don smaun abincin da za su ci.

Akwai bukatar gaggawa don bunkasa fasaha da ayyukan noma a 2014 a Afirka.

Ba tare da samun cigaban fasahar kere-kere da ayyukan noma ba, Afrika na da babban hatsari idan ta ci gaba da dogaro kan taimako daga waje, wanda hakan zai sanya ta gaza samun cigaba mai dorewa da wadatar da kai.

Magance wannan matsala ta cigaban zamani babban mataki ne wajen habaka wadatar nahiyar.

A karshe, kalubalolin da ke fuskantar Afirka a 2024 na da hatsari kuma suna da yawa, dole ne a samar da mafita ta hanyar hada kai waje guda a matakin kasa da kuma tsakanin kasashe.

A yayin da wannan kalubale kan iya zama karfen kafa, amma juriya da dagewar Afirka kuma, da irin kokarinta wajen ɗabbaka dimokuradiyya, amfani da matasanta na bayar da manyan damarmaki na cigaba.

Idan aka magance wadannan matsaloli ta hanyar hada kai waje guda da amfani da karfin da Afirka ke da shi, Afirka z ata iya isa ga tudun mun tsira tare sa samar da makoma mai kyau.

Mohamed Guleid, wani marubuci ne mai kishin Afirka kuma Mai Kula da Shirin Kasa na NEDI.

Togaciya: Ba lallai ne ra'ayin da wannan marubuci ya bayyana su zama sun yi daidai da ra'ayi ko manufofin dab'i na TRT Afirka ba.

TRT Afrika