Masu fasahar zane da waƙa da ƙirƙirar labari suna aiki don samar da juriya tsakanin 'yan Sudan. / Hoto: alfarmar Fatma Naib

Daga Fatma Naib

Duniya ba ta tafiya da hanzarin da zai taimaki Sudan ko 'ya'yanta. A wani ƙoƙari na fito da batun ƙasar Sudan, Fatma Naib ta yi rubutu kashi huɗu game da mu'amalarta da Sudan da ma al'ummarta, a matsayointa na 'yar jarida, kuma tsohuwar jami'ar MDD kuma abokiyar ƙasar.

A wannan kashi na huɗu, ta yi rubutu kan babban fatan makomar Sudan, wato matasanta da kuma fikirarsu.

Karanta kashin farko na rubutun, game da tafiyarta daga aikin jarida zuwa gwagwarmaya a Khartoum, a nan. Kashi na biyu game da yara masu fama da yunwa a nan. Sai kashi na uku kan matsalar ilimi a Sudan a nan.

Ina so na sadaukar da wasiƙata ta ƙarshe zuwa Sudan, ga matasan ƙasar da duka matasa masu ƙirƙira da na yi aiki da su, gami da tawagata. Matasan Sudan su ne ruhin ƙasar kuma su ne suke nuna yanayinta da makomarta za ta kasance a jihohinta 18.

Na gani da idona yadda suka koma, tun daga farkon juyin juya-hali da ya kawar da shugabancin shekaru 30 na Omar al Bashir a 2019.

Lokacin annobar Covid-19 a ƙoƙarin kawar da labaran bogi game da rigakafin, UNICEF ta haɗa gwiwa da 'yan barkwanci da wani ɗan YouTube Mustafa Jorry, inda suka ƙirƙiri shirin murya na intanet da ke tattauna huhimman batutuwa cikin raha, "Dagiga Nefham' (Ba ni minti ɗaya don na fahimta). / Hoto: alfarmar Fatma Naib.

Wani lokaci ne mai haɗari, cike da rashin tabbas, amma kuma lokaci ne da ake amfani da fasaha . Mutane na amfani da fasaha don samar da zaman lafiya da bayyana tunaninsi da labarunsu.

Yawancin waɗannan labaran sun shafi zaman lumana, da soyayya, da adalici, da mara-baya, da ƙoƙarin cimma madaneya ko madaneyao, wato mulkin farar-hula.

Kisan kiyashi da sakamakonsa

Duka irin waɗannan burikan sun watse ranar 3 ga Yuni na 2019. An hallaka mutane da ke bikin ƙarshen Ramadana,da shirin sallar Eid al Fitr a wajen shedikwatar ma'aikatar tsaro, bayan an umarce su da su bar zaman dirshan ɗin da suke yi.

Babu wanda aka hukunta kan mutuwar mutanen da abin ya shafa, kuma duka abokaina da abokan aiki sun cutu daga lamarin kai tsaye ko a fakaice. Wannan tashin hankalin ba na jin an wartsake daga shi.

A hankali, rayuwa ta dawo daidai sannan aka kafa gwamnatin riƙo. An samu alamun kyakkyawan fata, amma abin bai ɗore ba saboda a Oktoban 2021 sojoji sun karɓe mulki. Haka dai muka ci gaba da rayuwa da aikinmu.

Wannan kamfe na sadar da saƙonni ya fito da tarin fasaha ta yaran Sudan (zane daga Christian Mugarura).

‘Tawagar bajinta’

Ana tsaka da haka, na yi aiki da wata tawaga a UNICEF kan ayyukan ƙirƙira don wayar da kai da ilmantarwa ga al'umma game da batutuwan yara.

Bayan watanni muna tattaro yara, na taimaka wajen haɗa tawagar bajinta ta matan Sudan da ƙwararriyar 'yar jarida Ba'amurkiya, Aaliyah Madyun.

Kowane mamba ya zo da hikimarsa da ƙwarewarsa, inda ya taimaka wajen tsara dabaru da kyautata ayyukanmu tare da yara a Sudan.

Tare da Madyun da Mai El Shoush’s masu ƙwarewa a yaɗa labarai, da Reem Abbas 'yar jarida mai ƙwarewa, da Iman Mustafa mai ƙwarewa a dijital, da kuma Hadeel Agab masaniya kan aiki da matasa, kuma mun cimma sakamako mai kyau matuƙa.

Aiki tare da wannan tawagar bajintar ya sanya na saka ƙaimi wajen zamowa jagora mai iya aiki da nuna tausasawa ga ɗan'adam. A lokacin ne muka samu nasarori, da ƙalubale, da soyayyar juna, da hazaƙa wajen kawo sauyi.

Lokacin da annobar Covid ta zo, fatanmu a hankali ya fara rushewa, har sai da ya zamo saura ni da Reem Abbas ya rage. A ƙarshe na bari a 2022, sai ita ma Abbas ta bari a 2023.

Shirya finafinai

Lokacin zamana a Sudan na haɗu da wasu matasa masu fasaha, muka yi aiki da su. Ɗaya daga cikin ayyukan da ba zan manta da su ba shi ne mun yi aiki kan shirin koya wa yara haɗa fim, shirin da masanin shirya fim, Mosab Hassouna ya ƙirƙira.

Manufarsa shi ne amfani da shirin fim don tallafa wa yara su ƙirƙiri sabuwar zuriya ta matasa masu shirin fim, ta amfani da hanyar ba da labari, da samun waraka da abota.

Shirin na da niyyar ƙarfafa yara ta hanyar koyar da su yadda za su isar da labarinsu ta shirin fim, har muka ƙirƙiri bikin nuna fina-finai don nuna ayyukan yaran. Haɗin-gwiwar ya kawo nasarori, kuma ya taimaka wajen ba wa yara damar a ji su a Sudan.

Don samun masaniya kan masana'antar ƙirƙire-ƙirƙire a Sudan, tawagata ta haɗa gwiwa da ƙananan gidajen jarida. Wannan haɗaka ta buɗe ƙofofin shirye-shirye da taruka, har da waɗanda na ambato a ƙasa.

Kiɗa da waƙa da waƙe ɓangare ne na rayuwar Sudan. Wani harshe ne da ke shiga zuciyoyin al'umma, kuma jijiyar cikin jikinsu ce. Kenan, ba mamaki a ga na yi amfani da kiɗa a matsayin hanyar kira kan haƙƙoƙi, musamman haƙƙoƙin yara.

Kiɗa da fasaha don haƙƙoƙin yara

A wani ɓangare na kamfen ɗin UNICEF a Sudan game da haƙƙoƙin yara, an ƙirƙiri waƙa mai taken "Tamam'', wadda ke nufin "ya yi" ko "daidai" a Larabci. A 2019, Idreesy Koum ya karɓi tawagar daga El Mastaba suka yi aiki tare da Nada Juneid 'yar shekara 14, kan ƙarfafa yara mata. Ana kunna waƙar a radiyo kuma ta yi tashe.

Waƙa ta biyu tana cikin shirin kamfe na mayar da yara makaranta mai taken "Hodana." Mun sabunta waƙar da sananniya ce a Sudan wadda Abdel Muneim Abu Sam ya yi, muka saka sabbin saƙonni amma muka bar sautin wajen mawaƙin da kuma Ambasadar UNICEF a Sudan Maha Jaafar, wadda mawaƙiya ce, kuma 'yar fim sannan sananniyar 'yar YouTube.

Wannan bidiyon yana da muhimmanci saboda ya dace da sake buɗe makarantu bayan tsawon lokaci da rufe su, saboda annoba da kuma juyin-juya hali, wanda ya shafi damar samun ilimin yara.

Ɗaliban jami'a da dama sun samu illa. A 2018 lokacin da juyin juya halin ya fara, an rufe jami'o'i na tsawon lokaci, aka tilasta wa ɗalibai dakatar da karatu na shekara guda. Lokacin buɗewar, sai COVID-19 ta faɗo, wadda ta haifar da sake rufe makaranta tsawon ƙarin shekaru uku.

Waɗanda za su iya tafiya don neman ƙarin ilimi a wajen Sudan sun tafi, yayin da wasu ala dole suka tsaya jiran shekaru uku, kafin suka iya kammala karatu ko ƙara aji.

Komawa makaranta

Ga bidiyon Hodana, mun ƙirƙiri siga ta biyu ta amfani da yaren kurame, kuma muka mayar da shi sara a TikTok wanda Jaafer ya jagoranta.

Shirin ya zo ne don martani kan suka kan rashin wakilcin yara masu nakasa, musamman al'ummar kurame. Wannan sara ta TikTok ta yi tasiri sosai, ta taimaka wa waɗanda suka kalla ciki da wajen Sudan suka koyi yaren kurame, ciki har da 'yata Noor.

Wadda ta taimaka wajen bidiyon na kurame ita ce Enas Yousif, wata kurma matashiya mai gwagwarmayar samar da makarantar da yara da manya za su koyi yaren kurame don dacewa da yanayin duniyarta.

Tana yawan magana kan yadda ake ware yara saboda kurumta a Sudan, sakamakon rashin tsarin tafiya da kowa a tsarin ilimin ƙasar.

“A garin Port Sudan, makaranta ɗaya ce tal ta yara kurame. Makarantar tana da nisa daga mutane kuma yara sai sun bi hanya mara tsaro kafin su je, wanda ke haifar da daina zuwa makarantar," cewar Yousif a wata hira da gidauniyar Malala Foundation a 2021.

Ina da haƙƙi

A shekarar 2019 Shelar Majalisar Dinkin Duniya kan Haƙƙoƙin Yara ta cika shekara 30. Saboda haka ne muka ƙaddamar da shirin "Ina da haƙƙi" don fito da manufofin dokar.

Mun haɗa gwiwa da haziƙin daraktan fasaha kuma mai shirya fim, Idreesy Koum. Kamfe ɗin ya ci gaba na 'yan shekaru, inda ya nuna matsalolin da suka fi girma game da kare yara a Sudan a wancan lokacin, har da na cin zarafin mata, da ilimi, da lafiya, da gina jiki, da rikici, da yanayi, da ruwa, da tsafta.

Bidiyoyin sun fito a lokacin da aka kashe yara bayan zanga-zanga a wajen makarantarsu. Bidiyon ya birge mutane saboda a ƙarshensa an ce "Ina so na je makaranta da kuma dawo gida".

Ayyukan da na yi tare da Koum sun yi tasiri, kuma sun zo kan lokaci. Sun yi silar haɗuwa ta da mutane masu basira a wannan masana'anta. Sun yi aiki da zuciya kuma hakan ya yi tasiri kan abin da aka samar.

Wata tawagar daban ta matasa masu ƙirƙira waɗanda su ma suka birge ni, kuma nake da ƙaƙƙarfan haɗin gwiwa da su, su ne 'yan jarida, ƙarƙashin Ahmed Ibrahim.

‘FGM, ya ƙare daga ita!'

Ɗaya daga cikin aiki na ƙarshe da na yi kafin barin Sudan a 2022 shi ne bikin nune-nune game da yankan anguryar mata (FGM). Batu ne da na yi rubutu sosai kansa a matsayina na 'yar jarida, har da fim ɗin da ya ci kyautar Peabody "The Cut". Abu ne da ya damu zuciyata matuƙa kuma na yi aiki kansa tare da tawagar kare yara lokacin ina MDD.

Duk da an haramta shi a Yulin 2020, al'adar kaciyar mata har yanzu ana yin ta a Sudan. A cewar bayanai na baya-bayan nan daga 2022, ana yin kaciyar da kashi 86.6, kuma hakan na faruwa a duka yankunan Sudan.

Don kawar da matsalar, mun yi amfani da zane-zane don isar da saƙon ga abokai da al'ummarmu. An haɗa ni da Safa Kazzam, daraktar fasaha.

Tana da kiyayewa matuƙa, kuma na ji daɗin aiki da ita da kuma tawagar da muka yi aiki kan kamfe daban daban. Ɗaya cikinsu shi ne aikin nune-nune kan kaciyar mata da aka yi wa taken "FGM, ya ƙare daga ita," tare da haɗin gwiwar Downtown Gallery a Khartoum, inda wanda ya kafa cibiyar Rahiem Shadad ya jagoranta.

Mun yi aiki da masu fasaha har muka nuna fim ɗin "The Cut," sannan aka saurari tambayoyi da kuma horo kan batun kaciyar mata wanda tawagar kare yara ta aiwatar.

Wannan ya haifar da samar da kayayyakin fasaha da kuma fim ɗin don manufar ƙirƙirar fasaha da za ta janyo tunani don yaƙi da kaciyar. An buɗe bikin nune-nunen kuma na ji daɗin ganin iyaye mata da maza sun zo tare da 'ya'yansu.

Mun samar da bangon labarai, inda muka naɗi muryar martanin mata da kaciyar ta shafa. Mutane suna zuwa bangon su saka na'urar sauraro don jin labaran matan.

Yara sojoji

Aiki cikin ƙasar da ke fama da yaƙi, da mulkin soji na nufin cewa na ci karo da batutuwa masu sosa rai. Wannan ya haɗa ni da yara da suka tsinci kansu a tsakiyar rikici, wato "sojoji yara."

Ina tuna wani labari da tawagata take aiki game da wani da a baya yaro soja ne, wanda ya girma yake so ya ba da labarinsa. Mun yi tunanin hanya mafi kyau na ba da labarinsa shi ne mu mai da shi fim na katun mai taken "Sunana Younis, ni yaro ne, ba soja ba."

Lokacin rikicin da yaƙi, yara suna shiga haɗarin zalunci, da cin zarafi, da lalata. Ɓangarorin yaƙi sukan yi amfani da yara don yin ayyuka da dama, baya da yin yaƙi. Tun ɓarkewar yaƙin a Afrilun 2023, MDD ta bayyana damuwa kan ƙaruwar haɗarin ɗaukar yara aikin soji da ƙungiyoyi masu makamai ke yi a Sudan.

Lokacin da na zauna a Sudan lokaci ne mai cike da rikici, da kuma ƙalubale, amma na samu fa'idoji. Na yi aki da tawaga mai sadaukarwa, da abokai masu basira da matasa.

An rasa komai, amma ba har abada ba

Zuwa lokacin da na bar Sudan a 2022, yawancin 'yan tawagata sun riga sun bar Sudan, sun tafi aiki wasu ƙasashen da aka tura su kafin yaƙin. Kamar duka sauran abokan aikina 'yan Sudan, su ma sun rasa komai, – gidajensu, 'yan uwansu, da kuma damar dawowa gida.

Makamanci haka, su ma duka tawagogin fasahar da suka kasance tare da mu a zamana a Sudan sun rasa komai. Na ga yadda suka yi aiki tuƙuru don gina kasuwancinsu. Hakan ya saraya a rana guda.

Wasu sun shiga tsaka mai wuya, tsawon kwanaki a ofisoshinsu da suke je don yin aiki, kuma sanda yaƙin ya ɓarke, babu wanda ya shirya, kuma akwai haɗari idan mutum ya fita. Da yawa sun ɗauki hanya mai hatsari don ficewa daga babban birnin zuwa wasu birane, inda suka baro komai a can.

A cewar MDD, kusan mutane miliyan 11 a yanzu sun rasa matsuguni, sakamakon rikicin na Sudan. Wasu miliyan tara kuma sun rasa matsuguni cikin Sudan, sannan miliyan 1.7 sun gudu zuwa ƙasashe maƙota. Duka wannan alƙaluma na nuni kan mutanen da ke da buri kala-kala.

Abokaina, da abokan aiki, da maƙota, suna cikin mutanen da aka tilasta wa barin gida: Idreesy, Ahmed, Mosab, Rahiem, Safa, Reem, Snoopy, Samah. Sunayen suna da yawa sosai. Yanzu duka suna neman sake fara rayuwa daga babu.

A wasiƙata ta ƙarshe ina so na ce na gode ga Sudan, kuma ina ba da haƙurin cewa duniya ta ba ku kunya.

Masu sa'a sun nemi mafaka a ƙasashe maƙota. Amma da yawa ba su iya samun haka ba saboda wasu dalilai. Wasu kawai ba sa son barin ƙasarsu kuma waɗanda suka tafi suna fatan yaƙin ya ƙare don su dawo gida.

Da yawan abokaina suna da iyalai da suka kwashe shekaru suna aiki tuƙuru a ƙasashen waje don gina gida a Sudan inda za su dawo bayan ritaya. Yau sun rasa gidajensu. An tarwatsa dangi kuma an lalata fata nagari.

Sudan ta kasance mafakar aminci ga mutane daga Habasha, Yemen, Syria da mutanen da suka fito daga ƙasata, Eritrea. Ga waɗanda za su iya komawa gida ba, saboda mabambantan dalilai, Sudan ta zama ƙasarsu kuma mafakarsu. Amma yanzu wannan mafakar da saraya.

Sai dai, har yanzu akwai fata, kuma na yi imani 'yan Sudan za su dawo, su sake gina ƙasarsu, kuma su samu juriya. Amma kuma, hakan zai faru ne kawai idan yaƙi ya ƙare.

Ba zan daina godiya saboda tarbar da aka ba ni ba, da yanayin hazaƙa da na gani daga matasan Sudan. Kun ba ni abin tunawa har abada a zuciyata.

A wasiƙata ta ƙarshe ina so na ce na gode ga Sudan, kuma ina ba da haƙurin cewa duniya ta ba ku kunya.

Marubuciyar, Fatma Naib, 'yar jarida ce da ta ci kyautar Peabody kuma ta yi aiki da Al Jazeera English. Kuma ita tsohuwar babbar jami'ar UNICEF Sudan ce ɓangaren sadarwa, wadda yanzu take zaune a Sweden.

Togaciya: Ra'ayoyin da marubuciyar ta bayyana ba sa wakiltar ra'ayi, ko fahimta ko tsarin editocin TRT Afrika.

TRT Afrika