Mutum-mutumin Ameca na kamfanin Edisalat da aka gani a taron Mobile World Congress na 2024 da ake yi a birnin Barcelona na kasar Spain, a ranar Litinin 26 ga Fabrailun. Hoto: AP      

Daga Melike Tanberk

Jawabin Shugaban Kamfanin SpaceX, Elon Musk na kwanakin baya, inda ya ce ƙirƙirarriyar basira za ta iya fin mutane wayo nan da zuwa shekarar 2026, magana ce wadda ba za a yi watsi da ita ba baki dayanta, musamman a yanzu da bangaren kirkirar fasahohin zamani ke ƙara haɓaka.

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, 'yan kasuwa a bangaren fasahar zamani suna ta kokarin bayyana irin ci gaban da ake samu a bangaren kirkirarriyar basira, sannan suna bayyana fargabarsu a kan yiwuwar basirar ta maye gurbin wasu ayyuka na mutane.

Amma da gaske hasashen da wasu ke yi cewa zuwan fasahar ba abu ba ne mai kyau?

Akwai wani sananniyar karin magana da aka dinga yi a Karni na 19 da Ingilishi 'Clogs to clogs in three generations’ wanda a takaice yake nufin a wanke tukunyar yau domin gobe. Wato duk kokari da fasahar da mutum ke bukata domin samun nasara a yau, ya kuma cigaba da samun nasara a gobe, tun yau yake bukatarta.

Amma lura da yanayin habakar ilimin a yanzu, sai sauyin zamani ya rage tasirin wannan karin maganar a yanzu, amma zamanin baya, misali al'umma 800 da suka gabata, za a iya amfani da karin maganar.

Yanzu a ce duk tarin ilimin da mutane suke da shi tun farko halittar dan'adam, za a kwashe a zuba wa mutum-mutumi, wanda mutane suka kirkira.

Yanzu da ake tunanin wadannan kirkirarrun abubuwan za su ɗara mutane wayo, shin idan haka ne akwai bukatar mu cigaba da neman ilimin sanin rayuwa?

Kirkirarriyar basira za ta iya fin mutane wayo?

Zai iya yiwuwa hakan ya faru, amma idan an takaita fasaha a kan ilimi da aikace-aikace ne kawai. Amma ai a hakikanin ma'anar, hikima ta wuce batun wayo kawai.

Hikima ta kunshi abubuwa irin su tunani da dawainiya da sauransu. Shin za mu iya saka wa kirkirarriyar basira tunanin bambancewa tsakanin abubuwa, ta yadda za mu huta tunanin wasu kamar yanayin addini ko mutuwa da sauransu?

Za a iya tafka muhawarar ko kirkirarriyar basira za ta iya bambanta abubuwa masu kyau da marasa kyau, sannan ko za ta iya gano muhimmin abubuwa game da mutane da inda suke rayuwa.

Tun shekaru aru-aru mutane suke nazarta tare da fahimtar wadannan abubuwa kamar yanayin yadda duniya take ta hanyar amfani da ilimin falaki.

Irin wadannan ilimomin har yanzu ana cigaba da amfani da su. Akwai mamaki a ce abubuwan da muka kirkira, muka saka musu abin da muke so su yi, amma wai a ce su ne kuma za su iya fin mu ilimin.

Ilimin da iya fassara wasu bayanai ba kadai ba su ne hikima ba, suna dai iya ganewa tare da fassara bayanan da suka samu.

Mu mutane tun haihuwa ake haifarmu da basirarmu, sannan ilimin da muke da shi, da kuma yadda muke sarrafa abubuwan da suke faruwa, sai suka kara mana hikima.

Wani bangaren kuma kirkirarriyar basira ba za ta iya gane yanayin rayuwa da canjin zamani ba. Su suna aiki ne matukar akwai lantarki, ba tare da fargabar mutuwa ba, sannan ba su san kauna ba, ko kuma wani burin rayuwa.

Kalmar "qualia" na nufin tunani, fahimta, gogewa da sauransu.

Su kuma kirkirarrun basira nan ba su da wannan siffar, su dai kawai suna sarrafa bayanan da suka samu ne, sai su fitar da fahimtarsu.

Yadda mutane suke iya bambance sauyin lokaci da zamani ma yana cikin wasu manyan siffofin da suka bambanta mu da dabbobi da kirkirarriyar basira. Don haka kwatanta mutum da kirkirarriyar basira bai ma taso ba.

Za mu iya barin wani bangaren na ilimi ga kirkirarrun abubuwan, kamar yadda kirkirar rubutu ya sa mutane suka rage haddace abubuwa, wanda shi ma ya rage armashin yadda mutane suke iya ba da labari da baki.

Shi ma rubutu ya sha suka irin haka a farko; Socrates ya bayyana rubutu a matsayin yaudarar sauya mutane daga abin da suka saba, ba tare da hangen nesa ba.

Tarihi ne ke maimaita kansa, kamar yadda muka ba rubuto wani bangare na ilimominmu, ita ma kirkirarriyar basira ta dauke mana nauyin kallo da nazarta tare da fahimtar wasu abubuwan domin bayyana wasu abubuwan. Don haka don kawai kirkirarriyar basira ta yi wayo, ba yana nufin basirarmu za ta ragu ba ne.

Fahimtar God equation'?

Watakila yanzu duniya za ta kara fahimtar lissafin 'God's Equation,' wanda ke nufin alaka da ke tsakanin addini da fahimtar kimiyya. Ana amfani da kalmar wajen bayyana yanayin yadda duniya ke gudana.

Fitattun masana irin su Aristotle zuwa su Ibn Sina da magadansu irin su Muhammad ibn Musa al Khwarizmi, Newton da Abu Bakr al Razi da Schrodinger da Farabi da Aryabhatta da Shen Kuo da sauransu masana ne daga addinai da harsuna da launin fata daban-daban.

Duk da irin fasahohi na wadannan mutanen, dukkansu yanzu sun bar duniyar.

Watakila ba za su damu ba cewa ilimomin da suka tara, an zo lokacin da za iya zuba su, a wasu kirkirarrun abubuwa wadanda ba sa mutuwa, amma za su yi takaicin a ce magadansu sun bar wa kirkirarrun abubuwa ilimomin, wai har ake tunanin sun fi su sanin rayuwa.

Wadannan kirkirarrun abubuwan ba su da basira, duk da ana ganin sun fi mu wayo, domin basira ta samo asali ne daga hankali da tunani da hangen nesa da kare martabar duniya da mutanen cikinta.

Don haka bai kamata bayanin Elon Musk ya daga hankali ba.

Lokaci ya yi da za mu ba wadannan kirkirarrun abubuwan wasu lissa-lissafai marasa muhimmanci su yi ta yi ga wadannan kirkirarrun abubuwan don gano wasu abubuwan kafin rana ta koma gidanta na tsamiya - kimanin da kusan shekara biliyan biyar.

Game da marubuciyar: Melike Tanberk mai bincike ce a kan ka'idoji da hanyoyin adana bayanai a kirkirarriyar basira da kididdiga a Jami'ar Cambridge. Tana kuma da digiri a fannin Falsafa daga Jami'ar Oxford.

Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubucin ya yi daidai da ra'ayi ko ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika ba.

TRT Afrika