Daga Dr Basak Ozan Ozparlak
Duk da cewar muna yawan kwatanta zamanin tattara bayanai da yawa sa na Ƙirkirarriyar Basira da Injin mai aiki da tiriri wajen kawo sauyin kere-kere, wasu abubuwa da aka gano a yankuna na iya samar da sakamako mabambanci a kan wannan gaba.
A yayin da ake jagorantar dan adam ya kirkiri tsari a fannonin kasuwanci, tattalin arziki da siyasa, wadannan sabbin abubuwa ba su iya samar da dama iri daya ga kowa ba.
Har a rubutun tarihi ma, ba wani nuna tausayi ga batun gano inda Amurka take ba. Akwai sakafa a Amurka tun kafin a 1493.
Fahimtar tarihi ta bangare guda na bukatar tausayawa kuma yanayi ne mai hatsari wajen ilmantar da yara manyan gobe.
A yau, domin Ƙirkirarriyar Basira ta taimaka wa mutane fahimtar rikitaccen al'amari game da duniya, inganta ayyukan noma don tabbatar da kowa ya samu abinci, da kuma samar da tsarin riga-kafin kula da lafiya, dole muna bukatar cimma manufofin da a matsayin mu na 'yan adam ba mu cimma a baya ba: cigaban fasahar kere-kere.
Domin tabbatar da hakan, muna bukatar kundin dokoki mai duke da ka'idoji a ciki.
Wannan ne ya sanya yake da muhimmanci cewa samarwa da amfani da Kirkirarriyar Basira, wanda suna da saukin fahimta da amfani sama da sauran kayan fasaha, da ake kula da su bisa dokoki.
Tare da wannan manufa, A watan Dismban 2023 Tarayyar Turai ta samar da wata yarjejeniya kan halin ada ake ciki da kuma amfani da Kirkirarriyar Basira a duniya.
Amma ba ri mu waiwaya mu kalli labaran kokarin samar da dokoki ga AI.
Ya zuwa karshen 2010, 'yan majalisun dokoki, ma'aikatan sashen shari'a da malaman jami'a da ke ayyuka a fagen doka da oda, injiniyoyi da malaman kimiyyar zamantakewa na da wani abu da suke tambaya. Me ya wajaba a yi?
Amsoshin wannan tambayar sun sauya zuwa ga ka'idoji da dokokin Kirkirarriyar Basira, an buga mafi yawansu a cibiyoyi da dama a duniya a karshen shekarun 2010.
A wannan lokaci, Masu Dabarun KB na kasa, ciki har da nazarin SWOT, sun fito daga hannun kasashen duniya da dama.
Daga daga cikin wadannan dabaru da aka fi fahimta shi ne, Rahoton farko na Turkiyya Kan Dabaru Amfani da Ƙirkirarriyar Basira da aka fitar a 2021 karkashin Ma'aikatar Masana'antu da Kere-Kere, wadda ayyukan ke taimakawa kokarin cigaban sadarwar digital na Turkiyya.
Shekarar 2021 na da muhimmanci ga Dabarun Amfani da Kirkirarriyar Basira ta Tarayyar Turai, tuna kasashen Tarayyar 27 suka amice da samar da kai'idoji da manhajin bai daya.
Duba ga Dokokin Amfani da Kirkirarriyar Basira na 2019, an bayar da shawarar saka dokokin amfani da KB ga Hukumar Tarayyar Turai, kuma har an kusa kai mataki na karshe.
Hanyoyi masu gargada
Sai dai kuma, tafiyar na da wahala sosai, kuma akwai gargada a hanyar sosai.
A Nuwamban 2023, bayan an kammala Babban Taron Tsaron Kirkirarriyar Basira a Ingila ta karbi bakunci, kuma kasashen Amurka da manyan kasashen Tarayyar Turai - Faransa, Jamus da Italiya sun fitar da sanarwar ba a hukumance ba da manufar kare fasahar KB da kuma aiki da lura wajen amfani da dokar KB ta Tarayyar Turai, sun mayar da hankali kan aiki da fasahar, ba wai ita fasahar kanta ba.
Sun bayyana cewa dole ne a samar da dokoki maimakon ka'idojin shari'a game da tushen samarwa da aiki da Kirkirarriyar Basira, wanda ke kara rikita dokar Turai game da fasahar KB.
Abun farin ciki, an kammala cimma matsayar samar da matani, bayan kokari na tsawon shekaru kwalliya ta biya kudin sabulu: Dokar KB ta Tarayyar Turai, sannan ga kuma kafa Hukumar Kula da KB da aka kafa kwanan nan don tabbatar da aiki da dokar yadda ya dace.
Kamar yadda aka yi bayani a makalar farko game da dokar KB, wannan doka na da manufar tabbatar da bayar da kariyar lafiya, tsaro, kare hakkoki, dimokuradiyya, tsarin dokoki da muhalli. Fadadar dokar Kirkirarriyar Basira na da iyaka.
Ko an assasa ta a karkashin iyakokin Tarayyar Turai ko akasin haka, dokar Kirkirarriyar Basira za ta yi aiki kan masu samar da tsarin matukar za su sayar da shi a kasuwannin Turai ko aiki da shi a yankunanta.
Saboda haka, idan kamfanin Turkiyya ko Amurka na son sayar da kayansa, dole ne kayan su dace da DOkar KB ta Turai.
A matanin Dokar Kirkirarriyar Basira ta Tarayyar Turai, an fi yarda da aiki da mataki da ke aiki da matsakaiciyar fasahar kere-kere. Wannan na zuwa ne saboda Dokar Kirkirarriyar Basira na d amanufar kasancewa yadda ba za a gurbata tsarin a nan gaba ba, a yayin da fasaha ke kara habaka.
Ta wannan hanya, za a yi amfani da tsarin Kirkirarriyar Basira a sabuwar fasahar kere-kere, misali fasahar AR da inji mai kwakwalwa da kamfanin Neuralink na Elon Musk ke amfani da shi, wanda a nan gaba za su zama wani bangare na rayuwarmu
Mataki marar hatsari
Dadin dadawa, Dokar Kirkirarriyar Basira ta Turai na da manufar sanya idanu kan hatsarin da ka iya zuwa.
Hatsarin da ake magana a nan shi ne na lafiya, tsaro da hakkoki. Wannan tsari mai sanya idanu kan hatsari, na nufin kula da dokokin da suka dace da hatsari na kai tsaye da Kirkirarriyar Basira za ta iya kawo wa.
An haramta Tsarin Kirkirarriyar Basira da ke dauke da hatsarin da ba a amince da shi ba. Misali, an ki yarda da tsarin da ake amfani da shi don gano halin da mutum ke ciki a wuraren ayyuka da cibiyoyin ilimi.
To a wajen Dokar Kirkirarriyar Basira ta Tarayyar Turai, za a haramta da hana amfani da tsarin Kirkirarriyar Basira da ake amfani da shi wajen auna hali da yanayin da ma'aikata suke ciki, ko suna farin ciki ko bakin ciki, ko dalibai da yadda suke mayar da hankali ko akasin haka.
Duk wani kamfani na Kirkirarriyar Basira da zai shiga kasuwar Turai, to yana bukatar ya san wannan.
A gefe guda kuma, idan har wani tsarin Kirkirarriyar Basira zai sanya hatsari kamar yadda dokokin Turai suka bayyana, ya zama dole masu samar da wannan tsari su cika sharuddan da aka sanya.
A karkashin Dokar Kirkirarriyar Basira, kayan tantance mutane a wajen daukar aiki ko karatu na zama misalin abubuw amasu hatsari game da Kirkirarriyar Basira. Tun lokacin da aka fara amfani da wadannan hanyoyi wajen daukar aiki, an gano matsaloli sosai da suka shafi doka.
Saboda haka, kamar kowanne kamfani da ke samar da Kirkirarriyar Basira mai hatsari, masu samar da kayan fasahar daukar ma'aikata aiki ma dole ne su kula da hakan sosai.
Sai dai kuma, an shirya sanya manyan dokoki masu tsauri wanda dole manyan kamfanoni iri su ChatGPT na OpenAI su yi aiki da su.
A karkashin matanin da aka amince da shi, ba za a hana amfani da wata Kirkirarriyar Basira ba matukar ba za ta cutar da mutane ba.
Sai dai kuma, tare da manufar kirkirar sabbin abubuwa, tsarin Kirkirarriyar Basira da ya shafi smaarwa d agudanar da binciken kimiyya, ba sa karkashin wannan Doka ta Kirkirarriyar Basira da Tarayyar Turai ta samar.
Har zuwa lokacin da aka saki ChatGPT a 2022 da kamfanin OpenAI ya yi,wasu na muhawara ko dokoki da sharuddan kare mutuncin da adam na ayyukan su sun isar ko kuma suna bukatar gyara domin kare hatsari daga tsarin.
Mafi yawa a Amurka, akwai akidar bai daya kan cewa duk wani yunkurin doka zai kawo nakasu dga kirkirar sabbin abubuwa. Wannan ne ya sanya Amurka ta dauki lokaci kafin saka wata doka.
Sai dai kuma, bayan fara gwamnatin Obama, an tsara taswirorin ayyukan Kirkirarriyar Basira.
Amma kuma, karancin dokoki da yawaitar kere-kere sun gaza, saboda yawan yarukan da ake amfani da su wajen samar da abubuwan, wanda dokoki ne kadai za su iya saita su.
Ta haka ne, dokar da Fadar shugaban kasar Amurka ta fitar kan Kirkirarriyar Basira ya karbu tun kafin Baban Taron Tsaron Kirkirarriyar Basira na Ingila da aka yi a 2023.
Duba ga Amurka, za mu iya cewa dokokin ba su da nisa kuma zai yiwu a dabbaka su. Cigaba cikin sauri da yiyuwar tasirin ChatGPT na kamfanin OpenAI da aka sanar wa da duniya fitar sa a 2022, ya fara bayyanuwa a tsarin Amurka.
Hatsarin sirri da kare bayanan sirri na abubuwan da ke aiki da Kirkirarriyar Basira sun fi fasahar da ta gabace ta yawa, a saboda haka rage wadannan hatsari na iya yiwuwa tare da matakar fasahar kere-kere da kuma dokoki masu karfi da tasiri.
Duba ga wannan, an shigar da dokokin shari'a a tsarin tafiyar da harkokin Kirkirarriyar Basira na Amurka. A ranar 30 ga Oktoba, an fitar da babbar dokar Kirkirarriyar Basira ta Amurka a karkashin wannan tsari.
Sabon tsaron ya bukaci yi aiki da gaskiya kuma a fayyace daga kamfanonin Kirkirarriyar Basira game da yadda salon Kirkirarriyar Basirar da suke samarwa yake aiki.
Haka kuma dokokin za su samar da sabbin ka'idojin aiki da duk wani abu da Kirkirarriyar Basira ta samar.
Manufar dokar ita ce a kara "Tsaron Kirkirarriyar Basira" kamar yadda Fadar White House ta sanar. Sai dai kuma, akwai kokwantogame da tasirin dokar saboda "tana da laushi sosai" kuma na da rikitarwa.
A bayyane take karara, matanin ya hada da wajabtawa masu samar da Kirkirarriyar Basira su fitar da bayanan tsaro ga gwamnatin Amurka matukar aka gano abinda za su samar na iya haifar da wani hatsari ga dan adam.
Shekarar 2024 ta alkawarta zama babban lokaci mai muhimmanci ga sanya dokoki game da Kirkirarriyar Basira, inda za a samu dokoki na gaske da za su yi wa tafiyar jagoranci.
Tunda bayanai da kula da bayanai ne ke fayyace juyin juya halin Kirkirarriyar Basira, dokokin kula da bayanan, tsare bayanai da kundin dokoki ga budaddun bayanai za su zama ginshikin dokar Kirkirarriyar Basira, tare da was dokoki na musamman kan wannan fasaha ta zamani.
Domin makoma mai kyau, yana da muhimmanci a nemo tsarin dokoki ga Kirkirarriyar Basira don amfanin kowa da yadda kowa zai amfana da fasahar zamani.
A littafinsa, The Hobbit, JRR Tolkien ya ce abubuwa marasa matsala da kyawawa ba sa zama labari: dukkan labarai si=un cancanci a fade su a yanayi rikitacce ko mai cike d rudani.
Yau kamar yadda yake afkuwa sosai, muna cikin yanayi na kalubale d arashin tabbas. Ya kuma zama mai muhimmanci sosai mutum ya zama mai yunkurin aikata abu maimakon zama mai fata da sa ran aikatawa.
Kuma abinda Tolkien ya ce zai zama jagora wajen kirkirar sabbin labarai a rayuwarmu a karni na 21.
Marubuciyar wannan makala Dr Basak Ozan Ozparlak, mataimakiyar farfesa ce kuma mai bincike kan Dokokin Fasahar Sadarwa s Jami'ar Ozyegin da ke Istanbul, ta kware a bangaren fasahar 5G/6G, Kirkirarriyar Basira, kare bayanai da tsaron intanet.
Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubucin ya zama daidai da ra'ayi da ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika.