Daga Ersin Cahmutoglu
A bazarar 2017, duniya ta shaida abin sai daga baya aka fahimci cewa hari ne ta yanar gizo mafi muni a tarihi, wanda ya gurgunta kamfanoni masu zaman kansu da cibiyoyin gwamnati tare da janyo babbar asarar kudi da ta kai dala biliyan 10 zuwa 19 a duniya baki daya.
Manhajar NotPetya, wadda daga baya aka sauya mata suna, ta kasance wani farmaki na yanar gizo da ke tattare da kirkirarriyar basira da aka gina don kutse kan cibiyoyin tsaro da ke da rauni ayyukansu.
Idan da ace za a kai irin wannan hari a yau, a lokacin da fasahar KB ta inganta sosai kuma take da tasiri, to da zai illa da janyo asarar kudade sosai, kai har ma da kawo cikas ga kasuwancin duniya.
Babu mamaki, gwamnatoci a duniya na lura da sanya idanu kan illolin da Kirkirarriyar Basira (KB) ke janyo wa, musamman a hannun masu kutse da sauran kuniyoyi marasa daraja.
Kazalika kasashe na karfafar rundunonin sojinsu da ayyukansu na tsaro don kare su daga irin wannan hari.
Cigaban da aka samu a fannin KB ya daukaka sosai, musamman a 'yan shekarun nan da suka shude.
A yayin da Kirkirarriyar Basira (KB) ta yadu a yaruka da dama kuma ake aiki da ita a manhajoji da yawa, dole ne kasashe su hanzarta sabunta kawunansu da wannan cigaba.
Sabbin abubuwan da Kirkirarriyar Basira suka kawo na da tasiri a bigire da dama.
Sojoji, hukumomin leken asiri da jami'an tsaro da ke tabbatar da doka da oda, na gudanar da ayyuka masu kyau, madalla da hare-haren yanar gizo da ke zuwa tare da Kirkirarriyar Basira.
Kazalika, tare da taimakon krkirarriyar basira, manyan makaman kasashe manya na iya cimma matakai masu girma.
Akwai misalai da dama na irin wannan a sassan duniya, amma dukkan wadannan an yi su ne karkashun farmakai ko kuma leken asiri.
Za a iya cewar har yanzu ba a samu harin yanar gizo da ke tattare da KB da ya lalata manyan kayan more rayuwa da amfani ba a duniya.
Ko KB na iya tasiri kan yaki ta yanar gizo?
Duk da cewa har yanzu duniya ba ta shaida amfani da kirkirarriyar basira a yakin gaba da gaba da aka saba gani ba, akwai cigaba da samun damuwa kan likaci kawai ake jira na afkuwar hakan.
Misali, Birtaniya na ikirarin cewa Rasha da sauran kasashe abokan adawa na kokarin kara karfin ikon kai hari ta yanar gizo kuma suna shirin kai wa muhimmna kayana amfani rin wannan hari.
Kasashen Yamma na fadin cewa kasashe irin su Rasha da China na iya amfani da KB a yakin yanar gizo a nan gaba, duk da kasashen biyu sun yi watsi da ikirarin suna cewa farfagandar Turai ce kawai.
Kwararru a harkokin soji na cewa ba wai China da Rasha har da dukkan sauran kasashe na kai hari ta yanar gizo da amfani da KB.
Amurka, Birtaniya da kasashen Turai da dama sun zuba jari a wanan fanni a 'yan shekarun nan.
Sama da shekaru 10 da suka gabata, ana amfani da wata guba a na'urar kwamfuta da Amurka da Isra'ila suka samar wajen kai wa aikin nukiliyar Iran hari.
Wadannan jaruman yanar gizon, da za su iya kai mummunan hari ta yanar gizo kan kasashe abokan gaba ta hanyar hukumomin leken asirinsu da sojojinsu, na kuma iya kai farmakan da za su iya samar da mummunan sakamako saboda harin yanar gizo da ke hade da fasahar kirkirarriyar basira.
Misali, muhimman kayan sufuri, makamashi da sadarwa, da ma dukkan hukumomi da cibiyoyin kudade da muhimman hukumomin gwamnati, na iya lalacewa sakamakon hare-haren.
Tabbas, kasashe da dama na aiki don daukan matakan da suka zama wajibi a yayin da ake fuskantar wannan barazana.
Ana assasa sabbin cibiyoyi ko hukumomi don kariya daga hare-haren yanar gizo da ke dauke da fasahar KB.
A lokaci guda kuma, ana samar da dabaru da manufofi don gina kayan aiki da tsari da za su kalubalance irin wadannan hare-hare.
A 'yan watannin nan, gwamnatin Biden ta kaddamar da wani nazari da yake duba wa da auna ayyukan cibiyoyin kudi.
Kazlaika, an fahimci cewa ayyukan zamba cikin aminci da ake yi da fasahar KB irin su kudin jabu da damfara a ayyukan banki sun karu, wanda dole ne a dauki matakin magance su.
A wannan yanayi, amfani da kirkirarriyar basira a yakin yanar gizo na nufin yanayi mai cike da hatsari da damuwa game da tsaron kasashe da zaman lafiyar duniya.
Duba ga wannan yanayi da ake ciki, babbar tambayar da ke fuskantar duniya ita ce: Ta yaya girman hatsarin yakin yanar gizo mai aiki da KB yake da wacce irin damuwa za a yi?
Ga duniya don ta ama cikin shiri
Kutse ko hari ta yanar gizo mai aiki da kirkirarriyar basira ya sha bam-bam da harin yanar gizo na kutse da aka sani ta hanyoyi da dama masu muhimmanci, kuma wadannan bambance-bambance ne suka sanya shi zama mai hatsari.
Kazalika, KB na iya sanya harin yanar gizo ya yi tasiri sosai, ya zama mai saurin aiwatarwa, da samun inda aka nufa.
Game da wannan, za mu iya cewa yana samar da damarmaki ta wasu bangarori:
Aiki cikin hanzari: Kirkirarriyar Basira na iya rage lokacin shirya wa da kaddamar da hari da yake daukar kwanaki ko makonni, zuwa cikin 'yan awanni ko mintuna.
Misali, tsarin haska wa da nemo raunin wajen kai hari da yake daukar kwanaki, ta amfani da KB ana iya yi cikin 'yan saniyoyi, madalla ga alkaluman yanar gizo.
Layar zana: Makamin yanar gizo da aka samar da alkaluman yanar gizo na KB na iya buya tare da kaucewa kayan tsaron da aka saba da su a saboda haka ba a iya ganin su.
Kaifin basira: Hare-Haren yanar gizo da aka kai da fasahar Kirkirarriyar Basira (KB) na sbaa wa da yanayin da suke ciki cikin sauri tare da fahimtar ina ne za a kai harin.
Ta hanyar nazari kan martanin tsarin tsaro, KB na iya kara karfi da tasirin hare-haren da aka kai da shi.
Manyan hare-hare: KB na iya amfani da sakamakon nazarin muhimman bayanai don kaddamar da manyan hare-hare, musamman kai hari kan daidaikun mutane ko kamfanoni don kawo bazarana ta musamman.
KB na iya kai hare-hare zuwa wurare daban-daban a lokaci guda.
Ana iya kallon irin wannan damuwa a matsayin alamun shigar da tsarin kirkirarriyar basira ga fagen yaki.
A wannan gaba, KB ba iya kayan aiki ba ne, zai zama cibiyar dabarun yaki a fagen kasa da kasa.
Ya kamata a fahimci cewa duk irin saurin da aka yi na daukan matakan kariya daga hare-haren da aka kai da kirkirarriyar basira, hatsarin da barazanar ke da shi na iya lalata duk wannan kokari.
Ya zama dole a a fahimci cewa yakin yanar gizo mai aiki da kirkirarriyar basira ba wai kagagen shirin fim ba ne, a'a lamari ne na gasken gaske.
Amfani da wannan fasaha da kasashen da suka ci gaba ke yi na kawo babbar barazana ga kayan aikin sojoji da fararen hula.
A saboda haka, wasu kasashen ba lallai su iya kawar da wannan barazana ba.
Sakamakon wannan dalili kadai, zai iya zama dole a samu hadin kai da aiki tare, gami da zuba jari a fannin tsaro a tsakanin kasashen duniya.
Marubucin, Ersin Cahmutoglu na yin rubutu game da tsaron yanar gizo, basirar yanar gizo, hare-haren yanar gizo da kasashe ke daukar nauyi da aiki da bayanai. Yana yi karatun digirgir kan hare-haren yanar gizo da Isra'ila ke kai wa, a Jami'ar Sakarya.
Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar mahanga, da ra'ayoyin editocin TRT Afrika.