Sauyin AI ya riga ya iso, har ya mamaye rayuwarmu, yana shigewa duka lamuranmu. Hoto: Reuters

Daga Matthew Chan-piu

A tunani irin na duniyar da fasahar injina ta yi katutu, ana kallon fim din Terminator a matsayin wani babban misali. Sunan cibiyar duniyar Skynet, inda fasahar Kirkirarriyar Basira ta kankane karkashin jagorancin Cyberdyne Systems.

Skynet, wanda asali aka shirya shi don ya karfafa kariyar cibiyar Tsaro ta Sama, wato Strategic Air Command, daga baya ta girmama har ta fara iko da duniyar da ba a yi zato ba.

Ta karbe iko da duniyar halittun Cyberdyne, sannan ta gano cewa wadanda suka kirkire ta su ne manyan hadari gare ta. Skynet ya kaddamar da yakin kare-dangi da burin gwagwarmayar neman mulki tsakanin dan'adam da injina.

A matsayina na mai sha'awar wannan batu sanda nake karami, wannan fim ya sa na ni zumudi. Wannan kimiyya da aka nuna a adabin fasahar kimiyya, da kuma yadda aka nuna ta a fim, da masu kirkirar sun nuna yadda alaka za ta iya kasancewa da mu da kirkirarriyar basira.

An nuna duniyar da ake tunanin za ta zo, amma a zamani mai nisa. Sai dai kuma, a yau ga mu muna dab da wannan gagarumin sauyi. Sauyin AI ya riga ya iso, har ya mamaye rayuwarmu, yana shigewa duka lamuranmu.

Ana tsaka da wannan batu, wata fasahar kirkirarriyar basira da ta yi fice yanzu ita ce - Chat GPT, ta farko a fagenta na nuna cigaban dan'adam. Tana nuni da irin cigaban da zai faru a gaba, a matafiyar ginuwar fasahar AI, Chat GPT ya yi zarrar da za ta dade ana jin duriyarta.

A kidayar cigaban AI, Chat GPT zai samu matsayi na musamman tamkar wani abin tsafi. Zai zamo mafari, jagora, kuma wanda ya assasa wautar cigaba kuma ya nuna karfin basirar dan'adam.

Chat GPT manuniya ce ta sirrin cigaban AI, Amma gamayyar wadannan fasahohi da basirar dan'adam za su wuce wanda ake da su yanzu. Abu da zai faru daidai da tafiyar zamani.

A fagen tarihi, da kuma tarihin adabi, an yi ta ganin ana mayar da hankali kan karfin injina da suke kwaikwayon dan'adam. Mun samo sirrin abin da yake burge mua a adabin gargajiya. Tunanin injina masu magana da harshen dan'adam, kuma suna gogayya da dan'adam wani jigo ne da ya yi ta bayyana.

Amma kuma, an yi zaton wannan tunani ya yi wuri, har sai da aka ga zuwan Chat GPT wanda ya rusa duka wata tababa. A yau, muna iya bin tafarkin da ba a taba bi a baya ba. Abin da muke iya yi da AI ya sha kan tunani.

Duk wata mu'amala da Chat GPT da martanin da yake bayarwa, yana kai mu fagen rushe katangar da ke raba mu da shigar da kwakwarwar dan'adam cikin injina. Amma ya za mu sarrafa wannan cigaba?

Labarin da aka nuna a fim din Terminator na gargadi ne, kuma yana nuna mana karfin da hadarin saka wa abubuwan da muke kirkirar wata basira. A irin wannan yanayin, dukan mu za mu gajiya amma kuma za mu iya shiga hadari.

Batun Chat GPT's mafari ne kawai, kuma alama ce ta abin da zai biyo baya na kirkirarriyar basira ba shi da iyaka. Yana nuna mana cewa mu yi nazari kan iyakokin ginin kwamfuta da ladubban aikinta, da nauyin da ke kan dan'adam na mutuntaka.

A yayin da muke ƙarfin halin rungumar wannan sabuwar duniya, ka da mu bari tsoro da fargaba su mamaye mu, maimakon haka gara mu kwantar da hankali mu ci gajiyar rayuwar fasaha da muke fuskanta inda mutum da inji za su shaidi wani yanayi mai ban mamaki.

Mawallafin ra'ayin Mathew Chan-Piu, marubuci ne kuma mai shirya fina-finai da ke zaune a birnin Kampala na Uganda.

Togaciya: Mahangar da marubucin ya bayyana a nan ba sa wakiltar ra'ayoyi da mahangar editocin TRT Afrika.

TRT Afrika