Yaƙin Sudan: Dalilin da ya sa dole ɓangarorin da ke rikici su hau teburin sulhu

Yaƙin Sudan: Dalilin da ya sa dole ɓangarorin da ke rikici su hau teburin sulhu

Kafin a samu zaman lafiya, dole ne ƙasashen duniya su saka takunkumi ga masu rura wutar rikicin Sudan.
Ana ganin yaƙin Sudan shi ne yaƙi mafi girma da ya raba mutane da muhallansu. / Hoto: Reuters

Daga Edgar Githua

Sudan ta shafe sama da shekara ɗaya tana fama da mummunan yaƙi. Abokan gaba biyu waɗanda a baya suka yi aiki tare sun soma rikici kan mulki a 2023, wanda hakan ya haddasa yaƙin basasa.

Rundunar Sojin Sudan ƙarƙashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan da kuma rundunar RSF ƙarƙashin jagorancin Mohamed Hamdan Dagalo wanda aka fi sani da Hemedti, sun yi hannun riga, wanda hakan ya ja ga soma rikici a ƙasar a ranar 15 ga watan Afrilun 2023.

Jigon rikicin dai shi ne ƙin raba mulkin ƙasar tsakanin Janar al-Burhan da Janar Dagalo. Mutanen biyu sun yi aiki tare wajen hamɓarar da tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir a shekarar 2019.

Babban abin da ya jawo wannan rikicin shi ne ƙoƙarin da aka yi na haɗe rundunonin SAF da RSF a ƙarƙshin inuwa guda. A taƙaice dai ana so RSF ɗin ta dawo ƙarƙashin sojojin na Sudan, wanda lamari ne wanda Dagalo ke kallo a matsayin wanda bai ji daɗinsa ba.

Bayan sun haɗa kai sun rusa gwamnatin farar hula a shekarar 2021, Burhan da Dagalo ba su jituwa da juna inda daga baya rikici ya ɓarke.

Rikicin dai ya yi sanadin mutuwar kimanin mutane dubu goma sha hudu a cikin shekara guda da ta gabata tare da raba wasu miliyoyi daga muhallansu.

Jerin yarjejeniyar tsagaita wuta da suka gaza

An yi yunƙurin maido da zaman lafiya a Sudan da dama. Duk da haka, waɗannan yunƙurin sun ci tura saboda yawancin buƙatu masu cin karo da juna a cikin yanki, da siyasar duniya.

Ƙasashen duniya da ke da wata munufa ta daban sun ƙara dagula lamura domin samar da zaman lafiya. Daga cikin irin wannan gasar da ake yi tsakanin ƙasashe akwai batun samun damar samun ƙarfi ko tasiri kan Sudan sakamakon wurin da take a nahiyar Afirka.

Iran da Rasha suna kallon Sudan a matsayin wani wuri da za su ƙaddamar da tasirinsu kan nahiyar Afirka inda suke ta ƙoƙarin neman Janar Burhan ya bar su domin gina tashoshin ruwa a Bahar Maliya.

Birnin Khartoum da Omdurman da Darfur su ne wuraren da yaƙin ya fi lalatawa. / Hoto: Reuters

Wannan dai wani lamari ne da ya ga kawancen kasashen yammacin duniya wato Amurka da Birtaniya sun hada karfi da karfe da Saudiyya wajen kafa kawancen "Quad" da ke jagorantar tattaunawar sulhu tsakanin bangarorin da ke gaba da juna.

An tsara matakan samar da zaman lafiya da dama a wani yunkuri na kawo karshen rikicin Sudan. A karkashin jagorancin Amurka, Saudiyya, da IGAD, an warware yarjejeniyoyin da aka rattaba wa hannu a yayin da bangarorin biyu ke ci gaba da ayyukan soji.

An tsara matakan samar da zaman lafiya da dama a wani yunkuri na kawo karshen rikicin Sudan. A karkashin jagorancin Amurka da Saudiyya da IGAD, an warware yarjejeniyoyin da aka rattaba wa hannu a yayin da ɓangarorin biyu ke ci gaba da ayyukan soji.

Tasirin yaƙi

Rikicin kasar Sudan ya haifar da babbar matsalolin jin kai a kasar da kuma yankin. Hakan ya janyo rarrabuwar kawuna, da karancin abinci da rashin ababen more rayuwa.

An kuma samu matsalar ‘yan gudun hijira a yankin. Kimanin mutane miliyan takwas ne ke gudun hijira a cikin gida, suna rayuwa cikin munanan yanayi ba su da tsaftar muhalli da sauran muhimman ayyuka.

Wasu kiyasin mutane miliyan biyu sun tsere daga kasar kuma a halin yanzu suna kasashen Chadi, Sudan ta Kudu, Libya, da Masar, lamarin da ya haifar da wani rikicin zamantakewa da tattalin arziki a wadannan kasashe.

Matsalar abinci ita ma wata babbar matsala ce da Sudan ke fuskanta a halin yanzu a wannan rikicin da ake yi a ƙasar.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce aƙalla 'yan Sudan miliyan 25 na buƙatar taimako domin ceto rayuwarsu. / Hoto: Reuters

Shirin Samar da Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayar da rahoton cewa aƙalla mutum miliyan 18 suna fusakantar yunwa.

Matsalar dai na da nasaba da fari a makwabciyarta Sudan ta Kudu, da kuma Chadi inda ‘yan gudun hijirar Sudan da dama suka nemi mafaka.

Lamarin dai ya yi kamari inda kungiyoyin agaji ke neman agajin da ba a taba ganin irinsa ba.

Rikicin jinƙai da ke tasowa a Sudan yana da nasaba da cin zarafin bil'adama da suka hada da hare-hare kan fararen hula, cin zarafi ta hanyar lalata da kuma gudun hijira.

Kungiyoyin kare hakkin duniya da na Majalisar Dinkin Duniya sun zargi mayakan RSF da SAF da aikata munanan laifuka da suka hada da yiwuwar aikata manyan laifukan yaki da kuma kisa.

Neman mafita

Rikicin Sudan dai ya kasance mai sarkakiya sakamakon kasancewar ɓangarori daga waje da ke da muradu a yankin. Bukatar Rasha a cinikin zinari a Sudan tare da huldar kasuwanci da Janar Dagalo ne ya kara ruruta wutar rikicin.

Shi ma Janar Halifa Khafta daga kasar Libya ya yi zargin cewa ya goyi bayan Dagalo ya kara karfafa masa gwiwa. A gefe guda kuma, Masar ta yi zargin cewa tana goyon bayan Janar Burha.

Kimanin 'yan Sudan miliyan 1.7 ne aka tilasta wa yin hijira zuwa kasashe makwabta yayin da sama da miliyan shida ke neman mafaka a Sudan. / Hoto: Reuters

Domin zaman lafiya ya ɗore a Sudan, akwai buƙatar ƙasashen duniya su saka takunkumi kan masu goya wa rikicin Sudan baya.

Janyewar masu katsalandan ɗin zai ƙarfafa wa masu rikicin su zauna su tsara yadda za su sasanta. Kamata ya yi a bi wannan tare da hadin kai na diflomasiyya don ganin an kawo karshen rikicin.

Haka kuma akwai buƙatar ƙasashen waje su yi ƙoƙarin magance munanan matsalolin jin kai da ke tasowa a kasar.

Akwai buƙatar a mayar da hankali kan al'ummomi da yankuna ba wai a cikin Sudan ba kawai, ba a yankin ba.

Ana bukatar a kai agajin abinci da magunguna da sauran ababen more rayuwa ga wadanda abin ya shafa a kokarin ba wai kawai kare mutuncinsu ba har ma da ceton rayuka.

Marubucin, Dakta Edgar Githuamai bincike ne kan dangantakar ƙasa da ƙasa da zaman lafiya kuma mai sharhi ne kan tsaro a Jami'ar Strathmore da ke Kenya

Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubucin ya yi daidai da ra'ayi ko ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika ba.

TRT Afrika