Yaƙin Gaza wanda ya ɓarke a watan Oktoba ya ja hankalin duniya baki ɗaya sakamakon irin kisan jama'a da lalata ababen more rayuwa.
Kamar yadda UNICEF ta bayyana, Isra'ilar ta kashe dubban mutane a watanni goma da suka gabata daga ciki har da yara sama da 15,000.
Akwai wasu da dama da suka samu raunuka ko kuma suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzai haka kuma akwai dubbai waɗanda suka rasa muhallansu inda suke neman mafaka a muhallai marasa tsafta.
Haka kuma matsalar tattalin arziƙi da kuma asara da aka tafka ta biliyoyin dala na cikin ƙarin abubuwan da suka ƙara gurgunta tattalin arziƙin Gaza.
Ta yaya ƙasashen duniya ke mayar da martani? Bari mu tsaya mu yi duba dangane da yadda kafofin watsa labarai na duniya ke bayar da rahoto game da wannan yaƙin, inda za a kwatanta kafafen watsa labarai na gargajiya na Ƙasashen Yamma da kuma abubuwan da ake watsawa a kafofin sada zumunta na zamani.
Matakai masu sarƙaƙiya
Akwai matsala sosai a kan yadda kafofin watsa labaran Ƙasashen Yamma ke ba da rahotanni a kan yaƙin Gaza saboda dalilai masu yawa.
Bisa ga wani bita da Cibiyar Al Jazeera ta yi a watan Janairu, abubuwa da yawa irin su ayyukan watsa labarai da manufofin hukumomi da tsarin zamantakewa sun shafi aikin jarida na wannan yakin, lamarin da ya yi matuƙar shafar zurfafawa na labaran.
Hanyoyin watsa labarai, waɗanda suka haɗa da ingantattun hanyoyin gudanar da aiki a kafafen yaɗa labarai, sau da yawa sun fi ba da fifiko wajen gaggawar fitar da labarin fiye da yin rahoto mai zurfi.
Manufofin kafofin labarai kamar dokokin aikin jarida da rabon albarkatu, suna ƙara takura wa 'yan jarida, inda ake samun yuwuwar bayar da rahoto na son zuciya.
Wannan haduwar tasirin yana haifar da yin rahotanni marasa inganci da wadatar da ake buƙata don fitar da ainihin sarƙaƙiyar da ke cikin rikice-rikicen, wanda hakan ke shafar yadda jama’a za su fahimci lamarin da yadda za su tattauna shi.
Manyan kafafen watsa labarai sun fuskanci tarnaƙi kan rahorannin da suke yi a kan Gaza, wadanda suka hada da shingen siyasa da kalubalen akida da takun saka.
An soki kafafen yada labarai na Ƙasashen Yammacin Duniya da kasa bayar da rahoto na daidai kan rikicin Gaza, da gaskiya, da kuma cikakkiyar fahimta.
Ɗaya daga cikin manyan sukar shi ne labaran son zuciya wanda galibi ke fifita ɓangaren Isra'ila a kan labaran Falasɗinawa, inda suke dogara kacokan kan rahotannin hukuma daga ɓangaren Isra'ila ba tare da tantance cikakkiyar gaskiya ba.
Bugu da ƙari, akwai ƙarancin isassun bayanai na tarihi da kuma cin mutuncin Falasdinawa wadanda abin ya shafa, inda galibi ake ƙin nuna wahalar da suke sha ta yau da kullum.
Haka kuma, takaita wa 'yan jarida na kasa da kasa damar zuwa Gaza saboda takunkumin siyasa daga bangaren Isra'ila da kuma matsalolin tsaro na ƙara taƙaita samun cikakkun rahotanni.
Wannan yana sa wa yawancin kafofin watsa labarai na duniya su dogara ga maganganun gwamnati da na ‘yan jarida kaɗan da ke wajen, lamarin da ke iyakance samun mabambantan ra'ayoyi da zurfafan rahoranni.
Sarƙaƙiyar rikicin na Gaza sau da yawa ana taƙaita shi zuwa "rikicin Isra'ila da Hamas," wanda ke ƙara tsananta raguwa da rashin daidaituwa na yada labaran yaƙin.
A cewar wani bincike da Intercept ta yi a watan Janairu, CNN da MSNBC da FOX News duk sun ba da karkatattun rahotanni a farkon watannin farko na yaƙin Gaza.
Manyan jaridu irin su New York Times da Washington Post, da Los Angeles Times sun fifita bangaren Isra'ila, suna nuna ƙyama ga Falasdinawa da yin ko oho da irin wahalhalun da suke sha yau da kullum.
Rahotannin da kafofin yada labarai na Ƙasashen Yamma, musamman ma na Amurka ke yi suna da giɓi da dama.
Wadannan sun hada da rashin bayar da rahoto game da asarar fararen hula na Falasdinu da rashin cikakken ba da labari game da labaran sirri na asara da wahala, da rashin isasshen wakilci na ra'ayoyin Falasdinu.
Rawar da soshiyal midiya ke takawa
Saɓanin haka, kafofin sada zumunta sun cike giɓin da ake samu wajen bayar da rahotanni kan yaƙin Gaza. A cikin 'yan shekarun nan, sun zama masu ƙarfi wajen fitar da labarai a kan rikice-rikice na duniya, ciki har da wannan na baya-bayan nan.
Shafukan sada zumunta sun zama wasu kafofi masu mahimmanci da ke maye gurbin manyan kafofin watsa labarai da ke samar da labaran abubuwan da ke faruwa.
Dandali irin su Instagram da Facebook, da Twitter sun zama muryoyin mutanen da ke yankin inda suna baje kolin labaran abubuwan da ke shafarsu da yada hotuna da bidiyoyi kai tsaye.
Rubutun bidiyo da hashtags, irin su #freepalestine da #Gazaunderattack, sun ƙara wayar da kan jama'a da kuma haifar da tattaunawa a kan iyakokin yanki da akida.
Saƙonnin da suka watsu kamar wutar daji masu maudu’ai irin su #freepalestine da #Gazaunderattack sun ƙara wayar da kai da kuma jawo muhawara a fadin yankin da ma gaba da nan.
Aikin jarida na jama'a a shafukan sada zumunta ya ba da damar samun ra'ayoyi daban-daban ta hanyar gabatar da labaran da ba za a iya samu a kafofin watsa labarai irin su rediyo da talabijin da jarida ba.
Wannan dimokraɗiyya ta bayanai tana ba wa mutane damar bayyana ra'ayoyinsu ga ɗimbin masu bibiya a duniya
Shafukan sada zumunta sun kuma ba da damar haɗa tarurruka ga masu fafutuka da 'yan jarida, da jama'a don jawo hankali ga cin zarafin bil'adama da matsalolin jinƙai da ake fama da su waɗanda kafofin watsa labaru na yau da kullum suka yi watsi da su.
Shafukan sada zumunta suna tasiri sosai a kan ra'ayoyin jama'a da kuma watsa labarai a kan yaƙin Gaza. Alal misali, "shafukan sada zumunta suna tasiri kan yadda Amurkawa, musamman matasan Amurkawa, ke fahimtar rikice-rikice.
Matasa masu bibiya suna samun ƙarin labaransu daga shafukan sada zumunta - musamman TikTok da Instagram - fiye da kafofin watsa labarai da aka saba da su irin su jaridu da talabijin."
Fafutuka a shafukan sada zumunta ta haɓaka wayar da kan jama'a da ƙarfafa ɗaukar matakai daga al'ummar duniya, kamar sanya hannu kan koke-koke da tara kuɗaɗe ta amfani da na'urar gani da sauti da kuma ƙddamar da maudu'ai hashtags kamar #GazaUnderAttack.
Bugu da ƙari, shafukan sada zumunta suna samar da labaran abubuwan da ke faruwa kai-tsaye da ra'ayoyi daban-daban. Misali, Rosie da @ajplus a TikTok suna ba da rahotanni kai tsaye a kan Gaza, yayin da @mizna_arabart da e7saswafa ke amfani da Instagram don ba da rahoton abubuwan da suka faru da kuma asarar rayuka daga bangarorin biyu.
Wadannan dandamali suna ba mutane damar gani da jin fiye da abin da kafofin watsa labarai ke bayarwa.
Yayin da shafukan sada zumunta ke ba da dama mai kyau ga samun madadin labarai game da yakin Gaza, sai dai hakan na da nakasu.
Yaduwar labaran ƙarya da farfaganda cikin sauri na haifar da wani babban ƙalubale, lamarin da ke buƙatar samun ƙwarewa a ilimin amfani da intanet.
Bugu da ƙari, yin amfani da kafofin watsa labarai a wuraren rikici yana bijiro da tambayoyi game game da tsaro da bayanan sirri. Bayani mai mahimmanci da aka yi a bainar jama'a na iya jefa waɗanda ke ƙasa cikin haɗari.
Misali, kungiyar agaji ta Red Cross (ICRC) dole ne ta fitar da sanarwa don karyata labarai masu cutarwa a matsayin martani ga labaran karya da ke yaduwa game da ayyukansu a Isra'ila da Falasdinu.
Duk da waɗannan iyakoki, kafofin watsa labarai sun kasance masu mahimmanci don wayar da kan jama'a da haɓaka haɗin kai, da kuma yin tasiri ga watsa labarai na yau da kullum.
Shafukan sada zumunta suna ba da damar watsa labaran abubuwan da ke faruwa kai-tsaye da samun mabambantan ra'ayoyu da ma cike giɓin da kafofin watsa labarai na yau da kullum suka gaza gabatarwa.
Kafofin yada labarai na Ƙasasehn Yammacin Duniya suna yawan bin son ransu a lamarin yaƙiin Gaza ta hanyar rashin ba da ra'ayi na Falasdinawa da kuma watsi da yanayin tarihi, da tsara ra'ayin jama'a a cikin wannan tsari.
Kafofin watsa labarai kamar Instagram da TikTok suna taimakawa cike waɗannan gibin ta hanyar ba da labaran abubuwan da ke faruwa kai tsaye daga waɗanda abin ya shafa, amma kuma suna gabatar da haɗari kamar rashin fahimta da barazanar tsaro.
Ilimin kafofin watsa labarai yana da mahimmanci don kauce wa waɗannan ƙalubalen da amfani da fa'idodin kafofin watsa labarun yayin rikice-rikice.
Marubutan wannan maƙala su ne Sahar Khamis, ƙwararriya a harkokin watsa labarai na yankin Larabawa da Musulunci; da kuma Felicity Sena Dogbatse, ɗaliba mai yin karatun digirin-digirgir a sashen Sadarwa na Jami'ar Maryland a Amurka.