Masu sharhi da kuma masu tsare-tsare sun yi imanin cewar ana sabon wawaso kan Afirka/ Hoto: AA

Daga Burak Elmalı

A sannanun kafofin sadarwa, da manazarta a makarantu, da masu muhawara, abin da kawai ake ji shi ne munanan labarai game da Afirka.

Yawancinsu sun samo asali ne daga lokutan mulkin mallaka, da kuma tunani irin na ‘yan kama-wuri-zauna.

Wannan ne ya sa maimakon a kalli batutuwan Afirka a doron kansu, za ka ga ana mayar da Afirka tamkar wani abin da ake kallo ta mahangar wasu kasashe.

Amma bari mu fara fayyace wani batu, ba magana muke kan nahiya mai jama’a daya zalla ba.

Nahiyar tana da al’umma mabambanta kuma akwai tsarin siyasa daban-daban, da harsuna, da kabilu, da al’adu kala-kala.

Sai dai kuma lokaci ya yi da za a duba danniyar da salon zance kan Afirka wanda ke kallonta kamar wani abin cefane.

Yadda aka saba gani shi ne, “Kara X ta zuba jari a Afirka” ko “Afirka ta zama dandalin nuna iko tsakanin kasa X da kasa X”.

Idan ana batun rubutu da bayar da rahoto, ko jin labarai game da Afirka, to ya dace mu ringa duba da idon basira.

Bari mu yi nutso cikin batun gano me ya sa aka mayar da Afirka tamkar wata abar cefane irin yadda muka taso muna ga ana yi.

Don yin haka, abubuwa uku za su fito fili domin bayyana me ke faruwa yau game da yadda ake zayyana Afirka.

Harshe makamin nuna tazarar karfi

Yadda muke nuna Afirka ba wai batu ne kawai na kalmomi ba, batu ne na nuna iko.

Harshen da muke amfani da shi wajen zantuka kan Afirka suna nuna bambancin karfi, da kuma kallon Afika tamkar abin cefane, wanda wani dafi ne da ya faro tun lokacin mulkin mallaka.

Harshe yana da matukar tasiri. Yana iya sauya salon tarihi ta amfani da kalmomi.

A Afirka, kakabawa kasashe harsunan Turai a matsayin harshen hukuma, lokacin mulkin mallaka ya lahanta yadda ake kallon nahiyar da yadda ake ambata ta.

An yi amfani da harsuna a matsayin abin jigilar salon tunani na Turawa na yadda za a yi rubutu kan Afirka.

Hakan yana janyo mummunar fassara da kaskanci da kallon raini. Kenan, abin da ya faru na mulkin mallaka, abu ne na raini.

Sakamakon haka, yadda muke magana da rubutu da tattaunawa kan Afirka yana nuna irin wannan tasiri.

Tushen raini daga tunanin ‘yanci

Fikirori kan nazarin alakar al’umma sun hararo cewa salon da ake yin a kebance bakaken mutane daga shiga harkokin ‘yanci.

Zamanin nuna wariyar launin fata a Turai a karnin wayewar kai, ya ajiye batun tafiya tare a kan kankara.

Yadda ta kaya shi ne, “alakar jama’a” da ma can abu ne bambarakwai, kamar yadda littafin Charles W. Mills ya fada mai suna “Racial Contract”.

A wannan yanayi, babu mamaki idan wani rukunin mutane da ake ganin a matsayi “marasa wayewa” sun zamo abin kallo wadanda ya kamata a su “masu wayewa” su gyara.

Wannan salon tunani ba sabon abu ba ne, kuma ya bayyana a yanayi daban-daban a tarihi.

Wannan mahanga da ake wa lakabi da “progressive liberalism”, an yi amfani da ita don daukaka tsarin harkokin waje na kasar Amurka bayan yakin cacar baki.

Wannan wani babban misali ne na karyar cewa za a samar da ‘yanci” ga yankuna “marasa ‘yanci”.

Sabon salon raini a zamanin wayewa

Sabon salon wayewa ya mamaye mu ta amfani da tsarin gamewar duniya. Hakan ya janyo abin da Wendy Brown ya kira da juyin juya-hali a boye.

Wannan sabon tsarin tattalin arziki ya rage darajar zuwa kadara da ake auna kimarta da ma’aunin riba.

A wannan yanayi ne tsofaffin ‘yan mulkin mallaka suka ci gaba da dabarun sarrafa tunani ta amfani da tallafin ci gaban kasa.

Hakan yana jaddada bambanci tsakanin mai abu da wanda aka raina. A Afirka wannan raini ya dauki wani salon munafurci.

Shugaban Faransa Macron ya taba fallasa yadda tsarin dogaro kan agaji yake, da nuna tsarin fifiko, da ambato irin na nuna fifikon wayewa, a kalamansa lokacin taron G20 na 2017.

“Shirin Marshal Plan shiri ne na sake gini […] Kalubalen da ke gaban Afirka ya bambanta gaba daya kuma yana da rikici.

A yau batu ne na wayewa”, in ji Macron, wanda ya kara da cewa “muna bukatar mu kawo tsare-tsare da suka fi Marshal Plan wayewa”.

A maganarsa, ya nuna yatsa kan matan Afirka, sai yake nuna haihuwar ‘ya’ya bakwai ko takwas shi ne tushen rashin zaman lafiya a Afirka.

Wannan salon a nuna masu laifi wani mummunan misali ne na yadda ake ganin mata suna hana ci gaba.

Abin takaici shi ne wannan ba sabon abu ba ne a duniyar masu ra’ayin wayewa, wadanda suke ganin rayuka a matsayin jari da za a iya sadaukarwa wajen neman cimma muradun ci gaba.

Karkashin tsarin gamewar duniya, tsarin wayewa ya sake dawo da tsofaffin dabarun mulkin mallaka cikin sabon mazubi mai kyalli da aka yi wa lakabi da tallafin ci gaba, a duniyar da aka ce ta bar mulkin mallaka a tarihi.

Sai dai wannan tsari raina Afirka ne da ga masu cewa za su kawo gyara.

TRT Afrika: don gabatar da tsantsar Afirka

Labarta Afirka a matsayin abin raini mamakon wani batu mai zaman kansa wani tsari ne mai saukin ganewa.

A wani gefen, abu ne mai sarkakiya wanda ke da tushe a tarihi da fikirorin da suka kebance mutane bakake.

A daya gefen kuwa, dalilan da ke kawo shi mai sauki ne: wato samun iko kan yanki mai fadi ta kowace irin hanya.

A takaice dai, tamkar sauya kida ne amma rawa ba ta canja ba. Lokaci yayi na barin wannan salo don fara nuna Afirka da kyakkyawan ambato.

Lokaci ya yi da za mu fahimci yalwar al’adun da tarihin Afirka, don nuna cewa Afirka tana da muryarta da take magana da ita, maimakon daukar ta abar rainawa.

TRT World ta samar da TRT Afrika, mai yada labarai a harsuna hudu: Swahili da Hausa da Ingilishi da Faransanci.

Wannan mataki yana da burin sauya salon ambaton nahiyar Afirka, don sauya akalar labaran Afirka a duniya da za su bayyana arzikinnta da siyasarta da mutanenta da kuma al’adunta.

TRT Afrika