Wata mace 'yar Sudan da aka raba da matsuguninta a cikin wani tanti a sansanin ZamZam a arewacin Darfur, Sudan a ranar 1 ga Agustan 2024. (Reuters/Mohamed Jamal Jebrel).

Daga Tufail Hussain

A farkon wannan shekarar, na ziyarci Sudan don na ga yanayin da 'yan'adam ke ciki a kasar. Abin da na gani ya girgiza ni.

An tirsasa daukacin 'yan gida guda na rayuwa a cikin tanti guda daya kuma suna cin abinci sau daya a rana, sansanonin 'yan gudun hijira sun cika da mutanen da aka tsugunar da ke ta tururuwa, kuma mutane na bayar da munanan labaran halin da suka samu kansu a ciki.

Amma wani abu da ya girgiza ni matuka shi ne yadda lamarin bai ja hankalin kasashen duniya ba.

Yakin Sudan ya kawo halin shiga yunwa da rikici 'yan gudun hijira mafi muni a duniya. Sama da mutane miliyan 11 sun rasa matsugunansu, sama da yawan dukkan mutanen biranen Londin da Birmingham.

Rabin jama'ar kasar su miliyan 25.6 ba su da abinci, ma'ana ba su san lokacin da abincin da za su ci a nan gaba zai zo ba.

Kuma a yanzu yunya ta isa zuwa Darfur a yayin da yaki ya tirsasa manoma barin gonakinsu, 'yan kasuwa sun gudu daga kasuwanni inda aka sace kayayyaki, kuma an hana a kai wa jama'a taimako.

Amma har yanzu hankalin kasashen duniya bai koma kan rikicin ba wanda aka fara tun Afrilun 2023 kuma an hana kai kayan taimakon jin kai.

A yayin da na ziyarci sansanin 'yan gudun hijira a Port Sudan d Gedaref, ban ga wasu masu daukar labarai ba. Shekaru 20 da suka gabata, ba za a iya ganin haka game da tsanantar rikicin Sudan ba.

Tabbas, Akwai kalubale babba ga 'yan jaridu idan aka kalli rikicin kasar, kuma 'yan kasar Sudan 'yan jarida na fuskantar cikas wajen kawo rahotannin rikicin.

Kuma duk da wadannan kalubale, amma a 'yan watannin da suka gabata an samo kawo rahotanni masu kyau.

Amma yana da muhimmanci a ce yawan labaran da ake kawo wa su yi daidai da girman rikicin.

Ba tare da jan hankalin kafafen yada labarai, ba za a samu matakin siyasa, diplomasiyya da jin kai yadda ya kamata ba.

Amma me ya sa Sudan ke son jan hankali? Akwa dalilai da dama a kasa d asuka hana Sudan jan hankalin kasashen duniya.

Duniya ta sauya

Abin takaici, ina da ra'ayin a matsayinmu na duniya mun juya baya, mun yi biris da matsalolin wasu mutanen.

Matsalar tattalin arziki a 'yan shekarun nan ta lalata al'amura da yawa a duniya, ciki har da kawo talauci da wahalhalu a kasarmu, Birtaniya.

A kungiyar 'Islamic Relief UK', shirye-shiryenmu na cikin gida sun karu a kowacce shekara inda muke kokarin rage radadin talauci da ke daduwa a kasar.

Wannan na nufin cewa wahalhalun da mutane ke sha a kasashe sun zama marasa muhmmanci da za a mayar da hankali gare su.

Yario dan watanni 17 da ba ya samun isasshen abinci ke karbar ruwan sha a dakin kwantar da yara na Asibitin Mercy a Gidel kusa da Kauda a ranar 25 ga Yunin 2024., (Reuters/Thomas Mukoya).

Dadin dadawa, mun ga yadda wasu a kafafen yada labarai sun muzanta 'yan gudun hijira da masu neman mafaka da ke kokarin zuwa Birtaniya.

Shekaru 30 baya wa ya taba tunanin za mu iya juya wa wasu da ke fama da matsaloli baya da suke guje wa rikici da keta hakkokin dan adam?

A shekaru goman da suka gabata ko kamancin haka, rikici a Afirka na gwagwarmayar samun kula wa da jan hankali. Mutane nawa ne suka san cewa Somalia na fama da matsanancin fari?

Ko kuma cewa mummunan rikicin da ya kacalcala Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo?

Ana yawan yin mummunan kallo ga nahiyar Afirka a kwanakin nan, kamar yadda aka dinga muzanta tallafin jin kai, haka abin yake a nan a yanzu.

Wadannan ra'ayi da babu su, watakila suna kara ingiza nuna wariya da nuna bambanci ana sane ko bisa kuskure, sun sanya batutuwan Afirka su zama batutuwan da kasashen Yamma ba s adarajantawa.

A gaskiyance, mun ga cewa 'yan kasar Sudan ne da kan su suke gwagwarmayar daukar nauyin sauran 'yan kaar da rikici ya rutsa da su.

Kauyuka da dama sun marabci 'yan gudun hijira a gidajensu tare da ba su abinci.

Kungiyoyin yankunan kasar ne ke ta kokarin bayar da taimakon jinƙai, amma suna ta gwagwarmaya saboda al'amarin ba karami ba ne.

Mafita ta hanyar siyasa

Akwai manyan masu karfi a duniya da ke wajen nahiyar da suke kara rura wutar rikicin Sudan, suna yin biris da hanin MDD na kai makamai.

Rashin mayar da hankali ga irin wadannan batutuwa na da illa sosai, saboda a lokacin da mutane suka nuna rashin kulawa, sai a samu rashin matsin lamba na siyasa da daukar matakan da suka kamata.

Tunanin mutane da rashin wayar da kai ba sa taimakon wannan rikici. Wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da Islamic Relief UK suka gudanar a Savanta, an gano kashi 70 na manyan mutanen Birtaniya sun ce ba su san komai game da rikicin Sudan ba.

A karshe, lokacin da aka fara rikicin Sudan bai taimaka wa kasar ba, saboda ya zo a lokacin da ake fama da rikicin Gaza tare da mayar da hankali gare shi.

Gaza ta mamaye kanun labaran gidajen jaridu na kasashen duniya tun Oktoban 2023.

Abin da muke gani a kasar ya munana sosai, a yayin da sojoji suka aikata munanan laifuka ga Falasdinawa.

Wannan ba ya nufin wai za a manta da Gaza ba za a bayar da labarin yakin ba. Mutanen da ke Gaza na fuskantar bakin rikici, amma har yanzu an kas atsagaita wuta.

Kuma kafafen yada labarai ba za su daina dakko rahotannin ta'annatin ba kafin a kawo karshen rikicin.

Manufofin yada labarai na duniya na ta gwagwarmayar kawo labaran jin kai a kan lokaci. Idan ka waiwaya baya zuwa shekarun 2000, rikicin yankin Darfur na Sudan ya dinga zama a jaridu, amma kuma aka yi biris da rikicin DRC.

Jama'ar Sudan da suka gujewa rikici a yankin Murnei na Darfur da ke Sudan inda suke tsallaka iyakar Sudan da Chadi a ranar 4 ga Agustan 2024 (Reuters/Zohra Bensemra). 

A shekarun 2010, labaran rikicin Siriya da Lebanon ne ake gani a jaridu, amma aka manta da rikicin Yemen.

A yadda ake rikici a wannan shekarar a Gaza, Lebanon da Ukraine, sai aka manta gaba daya da Sudan wanda abin takaici ne matuka.

A shekara mai zuwa, gwamnatoci da kamfanonin dillancin labarai a duniya na bukatar mayar da hankali ga abubuwan da ke afkuwa a Sudan, kuma su sake tunani kan yadda za su bayar da labarin jama'ar Sudan yadda ya kamata.

Rawar da 'yan jaridar kasa da kasa za su taka na da matukar muhimmanci, kuma ya kamata a goyi bayan hakan, saboda kyawawan rahotanni na iya kawo sauyi kuma da bayyana ko gwamnatoci na da niyyar tallafa wa Sudan ko ba su da ita.

Marubucin wannan makala, Tufail Hussain, Daraktan Kungiyar Islam Relief UK. Yana da kwarewa da sanayya a bangaren bayar da tallafin jin kai da taimakon jama'a, yana taimaka wa wajen kawo sauyi da karfafa wa matasa da janyo hankalin duniya ga rikicin jin kai.

Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar mahanga, da ra'ayoyin editocin TRT Afrika.

TRT Afrika