By Richard Falk
Isra'ila a wannan shekarar tun harin da Hamas ta jagoranta ta yi iƙirarin cewa ta samu ƙarfin guiwar yaƙi da ta'addaci domin kawar da Hamas da kuma a baya bayan nan rusa Hezbollah a matsayin abokiyar gaba, kuma ta haka ta raunata abokiyar gabarta da take tsoro, Iran.
Wani ƙarin dalilinta shi ne ta kawar da Hamas ta Hezbollah da kuma Houthi a matsayin ƴan kanzagin babbar abokiyar gabarta, Iran, wacce ake zargin cewa ita ce babbar jagora a "ta'addacin ƙin jinin isra'ila" a yankin Gabas ta tsakiya, ƙawancen da ake kira da a ƙasashen Yammacin Duniya da cewa "Kasance bijirewa."
Wani Sabon mummunan al'amari da ya bujiro yayin cika shekara ɗaya da fara yaƙin ranar 7 ga watan Oktoba, shi ne ƙaddamar da hare hare shigen irin na Gaza a makwannin baya bayan nan da Isra'ila ke yi kan Hezbollah a kudancin Lebanon.
Wannan mugun harin na isra'ila na baya bayan nan ya ƙarƙare ne da kai mummunan hari ta wayoyi da radiyoyi sannan kwanaki tsakani kashe daɗaɗɗen shugaban Hezbollah, Hassan Nasrallah ranar 27 ga watan Satumba ya biyo baya. Kuma hakan ya faru ne shekara ɗaya bayan Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi maganar cewa duniyar nan ta haukace yayin da tashin hankalin siyasar yanki ke ƙaruwa."
A tsaka da wannan mamayar tare da rahotanni a kullum kan ta'adi da ake aikawa da kuma wahalhalu da fararen hula ke fuskanta tsawon lokaci, an soma tambaya kan ta'addacin da Isra'ila ke aikatawa tsawon lokaci da kuma dogewa da ta yi kan amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta da musayen fursunoni a Gaza da duniya ta goyi baya.
Mene ne babban ƙudurin isra'ila da ya cancanci wannan sadaukarwar na mutuncinta a matsayinta na wayayyiya kuma halartarciyar ƙasa, duk da dai mai jawo ka-ce-na-ce ce.
Kuma akwai wata tambaya tattare da wannan tambayar: shin isra'ila na da wani shirin kawo karshen yaƙin da ka iya wanke ta, musamman a wajenta, kan wannan sadaukarwar tare da amincewa da tabon halastaccen zargin nuna wariyar launin fata da aikata kisan kiyashin da kuma jerin laifuffuka da ta aikata kan bil adama.
Matakin ƙarshe na Netanyahu
A makon Jiya, firaministan isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana a New York kuma ya gabatar da wani jawabi mai ɗaure kai a gaban Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya wanda galibin kujerun wakilan suke wayam, yana cakuɗa kalamai marasa daɗi tare da hangen isra'ila na zaman lafiya.
A wani suka na kaucewa abin da ake magana kai, ya bayyana Majalisar Ɗinkin Duniya a matsayin "taron masu ƙin jinin Yahudawa" inda duk wani zargi da aka yi wa Isra'ila, duk rashin kan gadonsa, zai samu goyon bayan "masu rinjaye kai tsaye" a kan ƙasa ɗaya tilo a duniya da yahudawa ke da rinjaye, s wannan al'ummar ta doron ƙasa wato Majalisar Ɗinkin Duniya.
A wannan gurɓataccen yanayin ne Netanyahu ya zaɓi ya sanar da hangensa na kawo karshen yaƙin da ya yi iƙirarin kawo zaman lafiya da wadata a yankin.
Abin da Netanyahu ya gabatar wa zauren Majalisar Ɗinkin Duniyar da kusan wayam yake (saboda wakilai da yawa sun fice don nuna adawa da jawabinsa) wani ƙunshi ne na siyasar yanki da aka ƙulle tare kalaman albarkar zaman lafiya.
Wani kundi ne wanda mataki na farko ya ƙunshi hallaka maƙiyan isra'ila na zahiri, ƴan kanzagin Iran. Sai kuma mataki na biyu ya biyo baya "yarjejeniyar zaman lafiya da Saudi Arabia mai cike da tarihi" da za a gabatar ta wani salo shigen yarjejeniyar Abraham da aka cim ma a zamanin ƙarshe na shugabancin Trump shekaru huɗu da suka gabata.
Waɗannan kalaman da ke ayyana "wata sabuwar Gabas ta Tsakiya" kambabawar Netanyahu ce, wanda ya ce "akwai tarin albarkar da irin wannan zaman lafiyar da Saudi Arabia zai kawo."
Banda waɗanda ke son su yaudaru da irin wannan hasashen matakin ƙarshen, galibin mutanen da suka san abin da suke yi sun fahimci cewa wani misali ne na farfagandar gwamnati.
Netanyahu ya bayyana taswirar Sabuwar Yankin Gabas Ta Tsakiyarsa da babu alamar ƙasar Falasɗinu a cikinta, duk da Saudi Arabia ta nuna cewa ba za ta wanzar da zaman lafiya da Isra'ila ba har sai ƙasar Falasɗinu ta wanzu.
Irin wannan ƙin yin la'akari da abu ba kuskure ba ne. Ƙawancen Netanyahu da jam'iyu masu tsattsauran ra'ayin addini ƙarƙashin jagorancin masu tsattsauran ra'ayi irinsu Ministan Tsaron Ƙasa Itamar Ben-Gvir da Ministan Kuɗi Bezalel Smotrich zai rusa duk wani yunkurin gaske kan samar da yarjejeniyar ƙasar Falasɗinu da aka amince da shi a hukumance.
Ba abu mai yiwuwa ba ne a yarda cewa Netanyahu bai da masaniya game da wannan tarnaƙin, domin abin da kamar wuya, idan za a ɗan saya, cewa yana tsammanin karɓuwar wannan hangen nasa na matakin ƙarshe wanzar da zaman lafiya, ko da kuwa a Washington.
Tuhumar asalin matakin ƙarshe na Isra'ila
Ƙarƙashin batun hulɗa da jama'a game da batun matakin ƙarshe na Isra'ila akwai wani abun damuwa
Tun ma kafin gwamnatin Netanyahu ta karɓe iko a farkon shekarar 2023, a bayyane yake cewa ajendar siyasa ta isra'ila tana da wani shirin ɗaukar matakin ƙarshe da ba a bayyana ba da zai kammala Shirin kafa ƙasar Yahudawa bayan kwashe daruruwan shekaru ana kama-wuri-zauna.
Hakan ya fara bayyana a gare ni ne lokacin da gwamnatin Isra'ila ta gabatar da wata dokar kundin tsarin mulki ta ƙwaryaƙwarya a shekarar 2018.
A cikin, an rubuta haƙƙoƙin Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi a cikin dokar isra'ila kamar ba su ƴancin cin gashin kan Yahudawa, da kuma kaddamar da harshen Hebrew a matsayin harshen isra'ila ɗaya tilo a hukumance, da kuma faɗaɗa ƴancin kare kai na ƴan isra'ila zuwa matsugunan West Bank da aka mamaye.
Wannan matakin doka da majalisar dokokin ta ɗauka ne ya tabbatar da matakin isra'ila na ƙarshe game da batun ƙasa ɗaya da aka fi sani da "Maɗaukakiyar Isra'ila," wata dabara ta faɗaɗa ƴancin cin gashin kai a kan West Bank da Gabashin Jerusalem abin da ya saɓa wa dokokin duniya da kuma Ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya, har da na ƙasashen Yamma.
Irin waɗannan dokoki na wajibi ba za su sauyu da dokar majalisa ta yau da kullum ba,sai dai wata doka irinta ta nan gaba ta shafe ta.
Da gwamnatin haɗin gwiwa ta Netanyahu ta karɓi mulki, akwai wasu alamu masu tayar da hankali da ke nuni da cewa wannan dokar wajibi ta 2018 za a gaggauta ƙaƙaba ta a matsayin abu mafi muhimmanci a wajen Isra'ila.
Da farko ta nuna alama ne ta tashe tashen hankali a West Bank da aka mamaye da ke kai wa ga an isar da saƙo ga mazauna wajen cewa: "ku bar nan ko mu halaka ku."
A watan Satumba 2023, jawabin Netanyahu da ya ƙunshi taswirar yankin da bai ƙunshi Falasɗinu ba ya samu gindin zama ne sakamakon wani yunkurin diflomasiyya na daidaita dangantaka da wasu ƙasashen Larabawa, wata ƙarin manuniya za a kafa "Maɗaukakiya Isra'ila".
Waɗannan abubuwan tare tsokana a masallacin Al aqsa su suka haddasa na 7 ga watan Oktoba, al'amari da shi da kansa ya zama a cukurkuɗen da binciken ƙasashen duniya ne kaɗai zai kawar da shi.
Kuskuren lissafi a duk ɓangarorin
Duniya da farko ta runguma ko kuma aƙalla ta lamunci labarin harin 7 ga watan Oktoba da ya fito daga Isra'ila, har ma da bayanin dalilin yin ramuwar gayya tare da hujjar dokar ƙasashen duniya wacce ta ce mutum na da ƴancin kare kai.
Yayin da aka samu ƙarin bayanai, hujjar isra'ila ta farko kan mayar da martani sakamakon 7 ga watan Oktoba ta zama matsala. An tabbatar cewa shugabancin Netanyahu ya samu gargaɗi da yawa game da yiyuwar Hamas za ta kai hari.
Bayan an kwashe watanni ana yin bayar da horo, bisa ga dukkan alamu na'urorin saka ido na Isra'ila masu inganci matuƙa ba su yi aiki ba, kuma girma da tsaurin martanin ya sa ana zargin cewa Isra'ila na neman abin da za ta fake da shi ne ta haddasa kwashe Falasdinawa daga gaza sai kuma West Bank da aka mamaye ya biyo baya.
Hakan ya zama kamar mafarin kafa "Maɗaukakiyar Isra'ila" a hukumance da kuma cikar burin ainihin matakin ƙarshe na Isra'ila.
Idan za a tuna baya, Hamas ta Isra'ila duk su biyun sun yi kuskuren lissafi. Ita isra'ila bisa ga dukkan alamu ta yi lissafi ne da kisan kiyashin da zai haddasa imma miƙa wuya a siyasance ko kwashe jama'a, da kuma sabon zagayen Falasɗinawa ƴan gudun hijira.
Yadda suka jure haka, mawiyaci ne a hasasho kowanne irin miƙa wuya daga Falasɗinawa, ko da wane irin rage su harin Isra'ila zai yi, na ɗaukar matakin ƙarshe da bai haɗa da kyakkyawar makomar siyasar Falasɗinawa ba.
Isra'ila ba ta fahimci irin shaƙuwar da ke tsakanin Falasɗinawa da ƙasar ba, ko da kuwa a lokacin da suka fuskanci bala'i mafi muni.
Ana samun ƙarin ra'ayin jama'a mai tattare da fushi a faɗin duniya bayan uzuri da suka yi wa hare haren Isra'ila, ganin ta'adin da aka tafka da kuma mutane da aka yi garkuwa da su a harin da Hamas ta jagoranta.
A nata bangaren, Hamas ba ta ɗauka martanin isra'ila zai yi muni haka ba saboda sabo da hare haren da ta saba kaiwa da ba shi da alaƙa da matakin ƙarshe na Isra'ila.
Iƙirarin yin nasara da Isra'ila ta yi ya nuna gwamnatin ƙawance ta Netanyahu tun farko ta himmatu wajen ɗaukar matakin ƙarshe don tabbatar da "Maɗaukakiyar Isra'ila", tare da faɗaɗa yaƙin ya ƙunshi Lebanon kamar zai fi bayar da fa'ida.
Yadda suka jure haka, mawiyaci ne a hasasho kowanne irin miƙa wuya daga Falasɗinawa, ko da wane irin rage su harin Isra'ila zai yi, na ɗaukar matakin ƙarshe da bai haɗa da kyakkyawar makomar siyasar Falasɗinawa ba.
Wannan zai kasance ko ƙasar Falasɗinu mai cikakken ƴanci ko kuma sabuwar ƙasa ɗaya ta tarayya da ke kan bigiren daidaito tsakanin al'umomin biyu.
Daga karshe, babu yanayin siyasa a halin yanzu na ɗaukar matakin ƙarshe da zai gamsar da duka al'umomin biyu.
Marubucin Richard Falk farfesan Dokokin Ƙasashen Duniya mai murabus ne a jami'ar Princeton, Tsohon mai bai wa Majalisar Ɗinkin Duniya rahoto na musamman kan Falasɗinu da aka mamaye, kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka wallafa muƙalar da aka wallafa kwanan nan mai taken: Liberating the United Nations: Realism with Hope" (2024). Ana saka shi a jerin ƴan takarar lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya sau da yawa tun shekarar 2008.
Togaciya: Ra'ayin da marubucin ya bayyana ba dole ne ya yi daidai da ra'ayi,hange, tunanin da manufofin editan TRT Afrika ba.