Daga Muhammed Ali Ucar
Sauye-sauyen cinikayya ƙasa da ƙasa da ke bujurowa cikin hanzari suna shafar tattalin arziƙi da ya ginu kan sayar da kaya ga ƙasashen duniya kamar Jamus.
Tunda aka sake zaɓar Donald Trump a matsayin shugaban ƙasar Amurka, akwai yiwuwar a samu ƙarin kuɗin fito, abin da ke zama babbar barazana ga daidaiton tattalin arziƙin Jamus.
Tsawon gwamman shekaru, Jamus ta dogara da Amurka a matsayin babbar abokiyar cinikayya, amma wannan dogaron yana ƙara bayyana ɓaraka a tattalin arziƙin na Turai mafi girma.
Amurka ita ce ƙasar da ta fi sayen kayayyakin Jamus. A shekarar 2023, Jamus ya fitar da kaya zuwa Amurka da suka kai na Euro biliyan €157.9, abin da yake daidai da kaso goma na jimillar adadin kayayyakin da ta fitar waje.
Hakan ya zamar da Amurka kasuwa a kai miki dole musamman ma a fannonin ƙera ƙeren motoci da masana'antu na Jamus.
Amma dai buƙatar da Trump ya gabatar ta kuɗin fito kashi -25 kan kayan da aka shigo da su daga Canada da Mexico, kashi 10 a kan kayan Turai sai kuma har kashi 60 kan kayan da aka shigo da su daga China - zai iya kawo wa matsayin Jamus cikas a wannan muhimmiyar cinikayyar.
Idan Trump ya aiwatar da barazanarsa, kayayyakin da Jamus ke fitar wa Amurka za su ragu da har kashi 15.
Bangaren ƙere ƙeren motoci da na masana'antu, waɗanda sune ƙashin bayan tattalin arziƙin Jamus, su za su fi jin jiki. Masana'antar ƙera motoci ta Jamus, babban jigo a nasarar tattalin arziƙinta, wataƙila ta yi faɗi-tashi wajen maido da kasonta na kasuwa a Amurka.
Masana tattalin arziƙi sun yi kashedin cewa, waɗannan matakan karya lagon, za su iya jefa, ba wai Jamus ba kaɗai, har ma nahiyar Turai ita kanta, cikin matsalar tattalin arziƙi.
Moritz Schularick, shugaban Hukumar Tattalin Arziƙi Ta Duniya (IfW), ya bayyana yiwuwar mummunan tasirin waɗannan kuɗaɗen fiton a kan tattalin arziƙin Jamus.
A halin da ake ciki, ministan Harkokin Tattalin Arziƙi na ƙasa Robert Habeck, ya buƙaci a zauna a teburin tattaunawa, yana buƙatar kungiyar Tarayyar Turai da ta mayar da martani da murya ɗaya.
Babbar fargabar ita ce barazanar da Trump ya yi ta ƙaƙaba kuɗin fito har kashi 60 kan kayayyakin China, abin da tasirinsa ba zai taƙaita ga China ba kaɗai domin har harkokin samar da kaya na duniya sai ya taɓu, ya shafi Turai da Jamus.
Waɗannan matakan za su iya haifar da hauhawar kuɗaɗen sarrafa kayayyaki kuma ya raunata matsayin Jamus a cinikayyar ƙasa da ƙasa.
Idan manufofin karya lago na Trump suka tabbata, za su iya yin babban lahani ga dangantakar Jamus da abokiyar hulɗarta ta cinikayya mafi muhimmanci kuma su jefa ƙasar cikin koma-bayan tattalin arziƙi.
Matsalolin tattalin arziƙi masu ƙaruwa
A cikin gida, Jamus na fuskantar ƙalubale. Hauhawar farashin na ci gaba da ƙaruwa sannan korar ma'aikata da kamfanoni ke yi na ci gaba da kassara tattalin arziƙin.
Zuwa watan Nuwamba 2024 farashin kayayyaki da ayyuka sun ƙaru da fiye da kashi biyu idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, abin da ya laƙume ƴan kuɗaɗen jama'a sannan ya jinkirta bunƙasar tattalin arziƙi.
A halin da ake ciki, manyan kamfanonin Jamus suna sanar da sallamar ɗinbin ma'aikata.
Volkswagen na shirin rufe kusan masana'antu uku da sallamar dubban ma'aikata. Thyssenkrupp, wani babban kamfanin ƙarafa, yana da burin rage guraben aiki kimanin 11,000 zuwa shekarar 2030.
Deutsche Bahn ya ssnsr da hasarar Euro biliyan €1.2 a watanni shida na farko na 2024 sannan ya yi shirin sallamar aƙalla ma'aikata 30,000 zuwa shekarar 2029.
Shi ma kamfanin Bosch ya sanar da rage ƙarin gurbin aiki 5,500. Idan aka yi jimilla, wannan rasa ayyukan ya zarci guraben aiki 120,000, abin da ya ƙara kassara gogayyar tattalin arziƙin Jamus sannan ya ƙara rashin tabbas.
Har ila yau, Jamus na fuskantar matsalar yawan jama'a: al'umma da galibinta tsofaffi ne kuma take fuskantar tsananin ƙarancin ma'aikata.
Kafin ta iya dawwamar da bunƙasar tattalin arziƙi da kuma daidaita tsarin zamantakewarta, Jamus na ci gaba da dogaro da ma'aikata daga ƙasashen waje.
Amma kuma, jawo hankali da kuma ci gaba da riƙe ma'aikata daga wasu ƙasashe na buƙatar magance abubuwan da ke kawo tarnaƙi wajen tabbatarwa Jamus na ci gaba da gogayya a fagen jawo hankalin ma'aikata daga wasu ƙasashen duniya.
Kafin a cim ma haka, wajibi ne Jamus ta yi amfani da manufofin rungumar jama'a da za su jawo hankali da kuma dace da ma'aikatan ƙasashen waje.
Nuna wariyar launin fata da ƙyamar baƙi na zubar da mutuncin ƙasar a idon duniya kuma yana kawo cikas ga nasarar nashewar ma'aikata daga wasu ƙasashe da mutanen ƙasar.
Yaƙi da nuna wariya da kuma kyautata zamantakewa suna da muhimmanci wajen samar da daidaiton tattalin arziƙi da zamantakewar Jamus.
Jamus za ta hana shedar zama ɗan ƙasa ga mutanen da ke amfani da taken goyon bayan Falasɗinu a kafofin sada zumunta
Hanzarta hanyoyin tsugunar da mutane zai taimaka wa ma'aikata daga wasu ƙasashen su bayar da gudummawa yadda ake buƙata a fannonin tattalin arziƙi da tsarin ilimi.
Wajibi ne fasahar zamani da ƙirƙira su taka muhimmiyar rawa wajen farfaɗo da ɓangaren ƙwadago. Bunƙasa cigaban fasahar zamani, musamman a ɓangarorin masana'antu da ayyuka, za su samar da guraben aiki wa ma'aikata a gida da waje.
Ɓangaren ƙwadago da ya mayar da hankali kan fasahar zamani zai ƙarfafa gogayyar Jamus cikin ƙasashen duniya sannan ya zamar da ita ƙasar da take iya jawo hankalin ƙwararrun ma'aikata a faɗin duniya.
Wani muhimmin mataki shi ne rage ɗawainiyar cika ƙa'idojin hukuma. Tsawo da sarƙaƙiyar matakan da ake bi kafin samun izinin yin aiki suna sage guiwar mutanen da suka yi matuƙar cancanta, waɗanda a galibin lokaci suka zaɓi yin aiki a wasu ƙasashen.
Rage waɗannan matakan zai kyautata matsayin Jamus a kasuwar duniya sannan ya ƙara mata kwarjinin gogayya.
Sake nazari game da dogaro da wani ta fuskar cinikayya
China ta samu gagarumin cigaba a shekarun baya bayan nan wajen kare tattalin arziƙinta daga kutse daga waje.
A shekarar 2000, kimanin kashi 48 na cinikayyar China da ƙasashen G7 ta yi; zuwa shekarar 2024, wannan adadin ya ragu zuwa kashi 30.
Har ila yau, cinikayya da Amurka ya matuƙar raguwa. Yayin da China ta fitar da kayan da suka kai na dala biliyan $536 zuwa Amurka a shekarar 2022, wannan adadin ya ragu zuwa kashi 20% a shekarar 2023.
Domin cike waɗannan giɓan, China ta mayar da hankali kan kulla yarjeniyoyin cinikayya da kuma zuba jari kan kayayyakin more rayuwa a tsakanin ƙasashe masu tasowa.
Wannan muhimmin matakin raba ƙafa ya koya wa Jamus babban darasi.
Yawan dogaro da ƙasar ta yi da Amurka da China ya sa ta zama mai sauƙin fuskantar kasadar tattalin arziƙi.
Idan ta ƙulla hulɗa mai ƙarfi da ƙasashe masu tasowa a Afrika, da Kudu maso Gabashin Asiya da kuma Amurka ta Kudu, Jamus za ta iya taƙaita rauninta na tattalin arziƙi.
Amma fa, irin wannan mataki wajibi ne ya samu tagomashi gagarumin zuba jari a fannin fasahar zamani da dawamammen makamashi, da kuma tabbatar da samar da tsarin tattalin arziƙi na zamani kuma mai nagarta.
Idan ta yi koyi da China, Jamus za ta iya bunƙasa matsayinta a fagen cinikayyar duniya sannan ta iya jaddada makomar tattalin arziƙinta.
Yiwuwar haɗin guiwa tsakanin Jamus da Turkiyya
Ƙoƙarin raba ƙafa a tattalin arziƙi da Jamus ke yi zai iya cin gajiyar kyautata dangantakarta da Turkiyya.
Kasancewa tana zaune a muhimmin waje, ga ta da ma'aikata masu karsashi da kuma masana'antu masu bunƙasa cikin hanzari, Turkiyya ta zama abokiyar hulɗa mafi dacewa da burin tattalin arziƙin Jamus.
Masana'antun Turkiyya, musamman a ɓangarorin ƙere ƙeren motoci, da fasaha da kuma makamashi, sun dace sosai da buƙatun Jamus, kuma za su iya tallafawa hulɗar cinikayyarta yadda ya kamata.
Bugu da ƙari, hulɗa tare tsakanin Turkiyya da Tarayyar Turai za ta zabge wa Jamus yawan kuɗaɗen da za ta kashe sannan kuma ta samu sauƙin tafiyar da al'amura, da kyautata yiwuwar samun ƙulla alaƙa nan gaba.
Bunƙasar tattalin arziƙin Turkiyya ya samar da wata gagarumar dama ta bayar da gudummawa ga harkokin cinikayyar Jamus.
Ingantacciyar alaƙa tsakanin Jamus da Turkiyya ba za ta bunƙasa gogayyar cinikayyar Jamus ba ne kaɗai, face za ta samar da muhimmiyar damar raba ƙafa domin kauce wa fuskantar kasadar tattalin arziƙi.
Bayan batun tattalin arziƙi, wannan ƙawancen zai iya haifar da dangantakar siyasa ta kusa, abin da zai share hanya wa ƙarin kyakkyawa kuma muhimmiyar dangantaka.
Jamus tana cikin tsaka mai wuya, da ke buƙatar sauyin dabaru cikin gaggawa domin magance matsalolinta na tattalin arziƙi da Kuma dacewa da sauye sauyen da ke bujurowa na cinikayyar duniya.
Jaddada matsayinta a cinikayyar duniya da kuma magance matsalolin tattalin arziƙi na cikin gida na buƙatar ɗaukar matakai masu dogon zango da ke hangen gaba.
Marubucin, Muhammed Ali Ucar mai taimaka wa bincike ne a Cibiyar Bincike ta TRT World. T
Togaciya: Ra'ayi da marubucin ya bayyana ba dole ba ne ya zo daidai da ra'ayi, fahimta, da hangen da Ku manufofin editan TRT Afrika ba.