Narendra Modi na Indiya (L) da Xi Jinping na China (R) na fuskantar kalubale mai girma a tsakanin kasashensu, wato gwabza fada a fannin fasahar intanet (AP/Manish Swarup).

Daga Mir Seeneen

Duk da yunƙurin da aka yi a baya-bayan nan game da sasantawa, Indiya da China da alama sun kasance manyan abokan hamayya fiye da kowane lokaci.

A shekarun baya bayan nan dai kasashen biyu sun kulla huldar diflomasiyya, inda shugaban kasar China Xi Jinping ya ki halartar taron ƙungiyar G-20 na shekarar 2023 wanda firaministan Indiya Narendra Modi ya jagoranta.

A nasa bangaren, shi ma Modi ya ƙi halartar taron kungiyar hadin gwiwa na Shanghai na bana a Kazakhstan.

Sai dai kasashen biyu sun amince da yarjejeniyar kan iyaka da aka kulla sosai kan yankin Ladakh da ake takaddama a kai a watan Oktoba.

Dangane da waccar yarjejeniya, ma'aikatar harkokin waje ta Indiya (MEA) ta bayyana kyakkyawar dangantakarta da Beijing a watan Disamba.

Sai dai da wuya irin wannan yunƙurin son zuciya ya kawo ƙarshen rikicin da ake yi a kan fasahar intanet tsakanin ƙasashen na Asiya masu yawan al’umma da ya haura biliyan bibbiyu.

Rikicin fasahar intanet

Takaddama ce da ke ci gaba da ruruwa tun farkon barkewar annobar Covid, lokacin da New Delhi karkashin Modi ta mayar da rikicin zuwa ayyukan tafiya sararin samaniya ta hanyar ba da sanarwar dakatar da manhajoji 59 na China da suka hada da Weibo, a cikin 2020.

Ana ganin matakin a matsayin bude wata sabuwar ƙofar taƙaddamar a yakin da ake ci gaba da gwabzawa a fasahar intanet, a daidai lokacin da Indiya da China ke takaddama a kan iyakar Ladakh.

Muhawarorin da ake rura wutarsu a kafafen watsa labarai da shafukan sada zumunta na Indiya na ƙara rura wutar wannan rikici na fannin dijital, inda ake zargin manhajojin China da ƙunssar "abubuwan da ba su dace ba" da ke da yiwuwar zame wa tsaron ƙasar barazana.

A sakamakon haka, sai masu sharhi na kasar China su ma suka ƙaddamar da nasu yakin na kishin kasa, inda suke wallafa maƙaloli a kafafen yada labarai na gwamnati wadanda suke suka da mayar da martanin kan Indiyawa.

Har ila yau, ta gargade su kan abin da ka je ya zo da suka hada da tabarbarewar lamarin Kashmir a Majalisar Dinkin Duniya da fara aikin soji a Ladakh da Arunachal Pradesh.

Wannan yaƙin cacar bakan sun sa New Delhi ta kara sanya takunkumai kan fitattun manhajoji na kasar China kamar TikTok da sunan wata fafutuka da aka yi wa taken "Make in India", inda a karon farko manhajojin Indiya suka fara mamaye duniyar fasahar intanet ta ƙasar.

Sai dai kasashen biyu sun amince da yarjejeniyar kan iyaka da aka kulla sosai kan yankin Ladakh da ake takaddama a kai a watan Oktoba.  

Gasa ko gogayya na tantance manufofin ci gaban ƙasa na waɗannan ƙasashe da suka daɗe da samun wayewar zamani waɗanda kuma a baya suka ci gajiyar cinikayya da musayar al'adu a tsakaninsu.

New Delhi na kallon Beijing a matsayin babbar abokiyar gasa, lamarin da ya sa Indiyan ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye zuwa China da hana biza da korar 'yan jarida da kuma sanya hannun jarin China a Indiya.

Indiya ta kuma sanya takunkumi kan mu'amalar jama'a da tattaunawa ta kafofin watsa labarai da shirye-shiryen musayar dalibai da ayyukan al'adu da tarurrukan zane-zane da sana'o'i, lamarin da ya sa mu’amala mai kyau tsakanin Indiya da Sinawa ke yin wahala.

Kafin zuwa gaɓar yin wannan gasa, ƙasashen biyu sun ji daɗin ƙawancensu a farkon shekarun 1990. Sun ƙirƙiri nasu kasuwannin a duniya.

Amma saboda ƙwararrun sana'o’i, Beijing ta ninka kuɗin shigarta idan aka kwatanta da na takwararta ta Asiya.

Wannan dai ya haifar da gaba, duk da cewa kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a shekarar 1993 da kuma yarjejeniyar hadin gwiwa ta tsaron kan iyaka a shekarar 2013.

Sauran batutuwa

Yakin fasahar intanet alama ce ta batutuwa masu zurfi da Indiya da China suke samun yi sabani a kansu cikin shekaru da yawa, ga kuma batun takaddamar da suke yi a kan yanki.

Beijing ba ta ja da baya ba yayin da ta nuna rashin gamsuwa da goyon bayan Indiya ga batun lardin Taiwan. 

Da farko dai, akwai sojojin Beijing a kan iyakar Ladakh, da kuma tekun Indiya, inda New Delhi ke zargin China da amfani da jiragen ruwa na leken asiri.

Beijing ba ta ja da baya ba yayin da ta nuna rashin gamsuwa da goyon bayan Indiya ga batun lardin Taiwan.

Katafariyar ƙasar da ta yi zarra a fannin masana'antun ta kuma zargi New Delhi da yin katsalandan ga batun Tibet a shekarar 2019 ta hanyar ba da mafaka ga shugaban addinin Buddah, Dalai Lama, wanda Sinawa ke gani a matsayin mai neman ballewa.

Kazalika adawar kasashen biyu ita ce ke bayyana rashin jituwar da ke tsakaninsu. A matsayin wani bangare na ƙasa biyu masu adawa da juna, Indiya tana goyon bayan Indo-Pacific Quad, yayin da China ta jefa nauyi a bayan shirin Belt and Road Initiative.

A matsayinta na mamba ta BRICS – manyan kasashen duniya da suka hada da Brazil da Rasha da Indiya da China, da Afirka ta Kudu - Modi a kaikaice ya yi wa China shaguɓe ta hanyar kiranta da "mai adawa da Ƙasashen Yamma" yayin wani zaman rufe taron a wannan Oktoba.

Babban abin da ke damun firaministan Indiya shi ne raguwar tasirin New Delhi a ƙungiyar, yayin da Beijing da Moscow ke ci gaba da burin samun faɗaɗa a duniya.

Fito na fito a kan Kashmir

Amma a ƙoƙarin zama "Vishwa Guru" - jagoran duniya - "sabuwar Indiya" na Modi ya ƙi zama na biyu a Asiya.

Kasar ta fito fili ta ki amincewa da hanyar tattalin arzikin China-Pakistan a yankin Kashmir da ke karkashin Pakistan, kuma ta yi kira ga Beijing ta kai hari a Arunachal Pradesh.

BRICS

A daya hannun kuma China na adawa da matakin bai daya da New Delhi ta dauka na sauya alkiblar yankin Kashmir.

A watan Agustan 2019, New Delhi ta soke matsayi na musamman ga Kashmir da ke rikici kuma aka ƙirƙir Ladakh a matsayin yanki na daban daga gare shi.

China ta nuna rashin amincewa da matakin, tana mai cewa ya saɓa wa kudurorin Majalisar Dinkin Duniya kan Jammu da Kashmir.

Wannan ɓacin rai daga baya ya kunno kai kan batun wa ke da cikakken iko a kan Ladakh, inda Sojojin Yantar da Jama'a suka fafata da Sojojin Indiya a wani rikici da aka kira mafi muni tun bayan yakin Sin da Indiya a 1962.

Shekaru biyar bayan haka, yayin da bakin iyaka ya haifar da sabuwar gaba a Asiya, ministan harkokin waje na Indiya yana son a kiyaye yarjejeniyar kan iyaka.

Duk da haka, da yawa a Indiya na kallon wannan a matsayin ja da baya na dabara lokacin da yaƙin Ukraine ya kusantar da China da tsohuwar ƙawancen tsaro ta Indiya, wato Rasha.

Yunkurin na Beijing ya samo asali ne daga hadin gwiwar Amurka da Indiya kan kayan aikin sojan ruwa da fasahohi.

Yayin da ake ci gaba da yin shawarwarin zaman lafiya da kokarin diflomasiyya, adawar da ke tsakanin Indiya da Sin a fannin fasahar intanet ta kasance muhimmin fagen daga.

Yakin na zamani, wanda matsalolin tsaron kasa da gasar tattalin arziki ke haifarwa, na iya kara tsananta, inda kasashen biyu ke da burin sarrafa sararin samaniya da kuma tasirin duniya.

Marubucin, Mir Seeneen wakilin Kudancin Asiya ne, wanda ake wallafa rubutunsa a The Guardian da Al Jazeera da The Diplomat Magazine da SAAG, da sauransu.@MirSeeneen.

Togaciya: Ra'ayoyin da marubuciyar ta bayyana ba sa wakiltar mahanga, da ra'ayoyin eidtocin TRT Afrika.

TRT World