Daga Timi Odueso
A yayin wani zama ranar 15 ga watan Agusta, 2023, Majalisar Dokokin Kenya ta sanar da cewa ta karbi wani korafi mai neman haramta shafin nan mai farin jini na TikTok.
Rahotanni sun nuna cewa wani dan kansa, Bob Ndolo, ya kai korafin bayan gano akwai bukatar sanya ido kan shafin.
A korafin, Ndolo, wanda ke shugabantar wani kamfanin kwararru na dijital ya rubuta cewa shafin na sada zumunta yana yada barna da alfasha, wanda ke barazana ga al'adun Kenya da martabar addininsu.
Mai korafin ya nemi a haramta TikTok nan-take, wanda masu amfani da shi suka kai miliyan 14 a duniya.
Amma an yi sa'a, majalisar ta Kenya ta yi la'akari da cewa haramta shafin gaba daya ba zai yiwu ba, saboda zai janyo dubban 'yan Kenya masu wallafa a shafin za su rasa kudin shiga.
A farkon shekarar nan, an bayyana cewa Kenya ce kasar da ta fi yawan masu amfani da Tiktok a duniya.
Kenya ita ce babbar cibiyar masu wallafa a TikTok ta duniya inda suka haura mawallafa 100,000, kuma suka hada da Elsa Majimbo da Moya David, wandanda a shafin suka fara tashensu.
Amma yayin da Kenya ta zabi kin haramta TikTok a nan kusa, ba haka labarin yake ba dayar kasar da ke gabashin Afirka, wato Somaliya.
Mako daya bayan majalisar Kenya ta yi bitar wannan korafi, sai kasar Somaliya ta haramta TikTok ranar 21 ga Agusta.
Wannan yana cikin matakan da aka dauka kan shafukan sada zumunta, da suka hada da Telegram da 1XBET, wadanda ma'aikatar Sadarwa ta Somaliya ya ce 'yan ta'adda suna amfani da “kungiyoyin marasa tarbiya” don yada bayanan karya da hotunan tsiraici ga mutane.
Duka da Somaliya ita ce kasar Afirka ta farko da ta saka haramcin gaba daya kan shafin, akalla akwai kasa daya ta Afirka, Senegal, ta dakatar da TikTok do kawar da tashin hankali.
A watan Agusta, bayan gwamnatin Senegal ta rushe babbar jam'iyyar hamayya ta kasar, kuma ta kame jagoransu, kasar ta dakatar da aikin TikTok do kawo karshen mummunar zanga-zanga da yada sakonnin masu cutarwa.
Ba a Afirka ne kadai TikTok take fuskantar tsangwama ba. A wasu kasashen, kamar Indiya, sun haramta TikTok ko sun saka masa wasu nau'in takunkumi kan shafin, saboda dalilin da ba na gurbata al'ada ba: wato dalilin tsare-sirrin bayanai.
Tsaron sirrin bayanai
An haramta TikTok a Indiya tun shekarar 2020, saboda tsaron kasa, amma bayanan mutanen Indiya da suka taba yin amfani da shafin TikTok har yanzu ma'aikatan kamfanin suna iya ganin sa, bayan shekara uku.
TikTok mallakin kamfanin ByteDance ne, mai hedikwata a Beijing. Cibiyar adana bayanai ta kamfanin, inda ake adana duka bayanan masu amfani da shafin, a China yake.
Tun da manhajar ta fara samun shuhura a shekarar 2019, ya yi ta fuskantar kalubale game da tsarinsa na tsare sirrin bayanan mutane.
Wasu gwamnatoci suna tsoron bayanan 'yan kasarsu zai iya shiga hannun gwamnatin China, sakamakon dokokin kasar na leken asiri don tsaron kasa.
A dokar leken asiri don tsaron kasa ta China, Sadar ta 7 da ta 10, an wajabta wa kamfanoni da ke da rijista a kasar, ciki har da na shafin TikTok, su mika bayanan da suka kamata ga gwamnatin China.
Yayin da TikTok har a watan Marin na 2023 ta musanta zargin cewa yana yada bayanan masu amfani da shafin tare da gwamnatin China, da yawan mutane suna ba su gamsu da maganar ba.
A Disambar 2022, Amurka ta haramta amfani da TikTok a duk na'urori mallakin gwamnati. Jim kadan bayan haka, a Fabrairun 2023, hukumar Tarayyar Turai ta haramta amfani da TikTok a wayoyinsu na aiki da kwamfutoci.
Tun bayan nan, tarin kasashe da suka hada da Kanada, faranda da Denmark, sun bi sawun wannan mataki.
Hukumar binciken manyan laifuka ta FBI a Amurka ta sanara da 'yan majalisun dokokin kasar cewa gwamnatin China za ta iya amfani da bayanan da ta tara daga manhajar TikTok.
A 2022, wasu sakonnin imel na sirri da aka kwarmata daga kamfanin TikTok an yi zargin ma'aikata a kamfanin suna amfani da manhajar don leken asirin 'yan jarida, ta hanyar bin sawunsu zirga-zirgarsu, ta amfani da adirsehin na'ura na IP.
Irin wadannan batutuwa suna janyo damuwa har a tsakanin shugabannin siyasa.
Babbar manufar zarge-zargen amfani da bayanai da ake wa TikTok, ya ta'allaka ne kan tsaro, da ribatarwar tattalin arziki ga kasar China.
Ko ana zuzuta matsalar?
Duk da cewa batun tsaron kasa da tsare bayanan sirri su ne kangaba a dalilan saka wa TikTok takunkumi, wasu na ganin ana zuzuta barazanar da TikTok ke yi.
“Wannan damuwa suna da hujja, ko da kuwa an zuzuta su. TikTok yana tattaro bayanai da yawa kamar sauran shafukan sada zumunta ," Wannan tsoro irinsa ake yi wa China gabadayanta.
Duk da haka, ban taba jin wani dalili da ke bukatar daukar mataki," a cewar Dr. Clifford Lampe, farfesan nazarin bayanai, kuma shugabar tsangayar Harkokin Karatu a makarantar nazarin bayanai da ke Jami'ar Michigan ta Amurka.
Ana tsaka da karuwar wannan saka ido da haramci, TikTok yana mayar da hankalinsa ga masu amfani da shafin a Afirka, nahiyar da ta zamo mai tashen harkar shafukan sada zumunta.
Duk da shafin yana nuna tasirin Afirka a matsayin kasuwar da ke girma, inda ake da akalla masu amfani da shafin miliyan 35, amma har yanzu bai zuba jari a Afirkan ba.
Masu wallafa daga Afirka suna iya samu kudi ne kadai daga TikTok ta hanyar kasuwancin masu fada a ji. Shafin ba ya biyan mawallafa a Afirka kamar yadda yake yi a wasu yankunan duniya.
Ranar 24 ga watan Agusta, daidai da ranar da haramcin TikTok a Somaliya ya fara aiki, shafin ya sanar da cewa zai bude ofis a Kenya, na farko a nahiyar Afirka.
Bayan haduwa da shugaban kamfanin TikTok, Shou Zi Chew kan batun kudurin neman haramta shafin a kasar, shugaban Kenya, William Ruto ya sanar da cewa Chew ya amince ya bude ofis a Kenya, kuma ya dauki 'yan Kenya ma'aikata a sashen kula da daidaita abubuwan da ake wallafawa.
Kamfanin na sada zumunta ya sha maimaita karyata cewa suna sabawa doka a ayyukansu a fadin duniya.
A watan Maris na 2023, shugaban TikTok, Shou Zi Chou ya bayyana a gaban majalisar dokokin Amurka, don yin bayani yadda TikTok yake amfani da bayanai.
Kuma ya sake musanta cewa gwamnatin China tana samu, ko tana iya samun bayanan mutane daga TikTok. Akwai damuwa kan batun tsaro, amma hujjar hakan ba a bayyane take ba, har yanzu hasashe ne kawai.
TikTok yana kan gaba wajen samun tsangwama a cikin kamfanonin sada zumunta na zamani. Sai dai, ana nuna damuwa kan sauran kamfanonin irinsa, kamar kamfanin Meta, da Twitter da Telegram.
Sai dai kuma a Afirka, gwamnatoci har yanzu suna bukatar nuna kulawa kan tsaron kasa, sama da al'adun al'ummominsu.
Mawallafin, Timi Odueso, babban Edita na a mujallar labarai ta TechCabal.
Togajiya: Mahangar da marubucin ya bayyana a nan ba sa wakiltar ra'ayoyi da mahangar iditocin TRT Afrika ba.