Kenya: Kalubalen dake fuskantar William Ruto

Kenya: Kalubalen dake fuskantar William Ruto

Bayan guguwar da ta kunno wadda ta kawo nasara, William Ruto zai fuskanci hakikanin wahalar matsalar tattalin arziki.

Tsakann hauhawar farashin kayan masarufi, rashin aikin yi, bashi mai hauhawa, cin hanci da rashawa, da mummunan yanayin da dan adam ke ciki, kalubalen da sabon shugaban ke fuskanta na da dimbin yawa.

Daga 13 ga Satumba, 2013 William Ruto dan shekaru 55 ya zama Shugaban Kasar Kenya na 5 tun bayan da kasar ta samu ‘yancin kanta a ahskerar 1963. An rsantsar da shi a Kotun Koli dake Nairobi, ba tare da halartar abokin hamayyarsa Raila Odinga mai shekaru 77 da ya bawa tazara da kuri’u 233,000. Ruto dake matsayin Mataimakin Shugaban Kasa mai barin gado, ya lashe zaben da kaso 50.49, inda Odinga kuma ya samu kaso 48.85 na kuri’un da aka jefa, inda ya yi rashin nasarar zama shugaban kasa a karo na 5, duk da Shugaban Kasar ma barin gado Uhuru Kenyatta ya goya masa baya.

Lokaci na kurewa, kuma a bayyana take karara, William Ruto ba zai samu isasshen kuma yalwar lokaci ba, duba da yadda jama’ar kasar suke sa ran kawo sauyi nan take, ga kuma kalubalen tattalin arziki da na yanayin jinkai da jama’a ke ciki a kasar.

Yanayin da ake ciki a Kenya ya munana, saboda hauhawar farashi ya kai kaso 8.3 a watan Agustan da ya gabata, sannan a 2021 kuma ya kama kaso 7.5, duk da ana da manufar rage hakan zuwa kaso 5.5 a 2022, kamar yadda Bankin Duniya ya shaida.

Hauhawar man fetur ya janyo tashin kayan masarufi da dama. Garin masara da ake yin tuwo da shi, ya zama ‘yan kasa gama-gari ba sa iya saya.

Kasar na illatuwa daga rikicin da Rasha da Yukren ke yi, su ne kasashen waje biyu dake bawa Kenya mafi yawan hatsin da take bukata, alkama da masara.

Dadin dadawa, farin da ya mamayi yankunan kasar da dama ya kara ta’azzara karancin samar da amfanin gona a Kenya, wanda shi ne kaso 22 na kayan da kasar ke samarwa, sannan ga matsalar tsada da karancin takin zamani, wand dukkan su daga Yukren da Rasha ake shigar da su Kenya. A lokacin gangamin zabe, William Ruto ya yi alkawarin bayar da tallafi a wannan bangare dake da muhimmanci ga tattalin arzikin Kenya.

Mummunan yanayi

Wani babban kalubale da matsala dake fuskantar sabon Shugaban Kasar shi ne, rashin aikin yi ga matasa, inda kaso 75 na ‘yan shekaru kasa da 35 ba su da aikin yi. A kowacce shekara, jami’o’in Kenya na yaye dalibai dubu 500,000 da suke fara neman abun yi, kuma babu wanda ya san a ina ne za a ba su aikin. Alkaluman Bankin Duniya sun bayyana akwai a kalla matasa miliyan 5 da ba su da aikin yi a Kenya--- kuma bangaren da ba na gwamnati ba ne yake samar da kaso 80 na aiyukan yi a kasar.

Domin magance rashin aiyukan yi, tsohon Shugaban Kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya dogara kan karuwar zuba jari a bangaren gina kasa, wanda ya hada da zamantar da tashar jiragen ruwa ta Mombasa, da kuma gina layin dogo tsakanin Nairobi da Mombasa. Amma kuma wannan aiki na da tsada, ya kuma kara yawan bashin da ake bin kasar --- musamman yadda darajar kudin Kenya ke faduwa kasa warwar idana aka kwanta shi da dalar Amurka, inda ya karye da kaso 5 tun farkon shekara inda dalar Amurka 1 ta kama Sulai din Kenya 10.45 a ranar 13 ga Satumban 2022. Bankin Duniya ya yi hasashen bashin Kenya ya kai dala miliyan 70 wanda shi ne kaso 67 na kayan da take samarwa, inda China ce kasar dake kan gaba wajen baiwa Kenya basussukan kudade.

Wannan na nufin a tsakanin 2013 zuwa 2022, bashin da ake bin Kenya ya ninka sau 4. Wakiliyar Bankin Duniya a Kenya Mary Goldman ta bayyana damuwarta tare da jan hankalin makusantan kasar kan hatsari dake tattare da cin bashin.

William Ryto ya yi alkawarin samar da shugabanci na gaskiya tare da gujewa cin basussuka musamman ma daga wajen China, cin hanci da rashawa abu ne da ya dami ‘yan kasuwa a Kenya.

Yawaitar cin hanci da rasha da shugaba rikitacce

A rahoto kan cin hanci da rashawa na 2021 da Kungiyar ‘Transparency International’ ta fitar, Kenya na nan a jerin masu fama da cin hanci da rashawa inda take na 128 kan batun kwatanta gaskiya wajen mu’ala da jagoranci.

Kuma sabon shugaban kasar da ya yi gangamin zame kan kautata rayuwa da hbaka tattali arziki, akwai bukatar ya zama abun koyi kuma mai zaburar da sauran jama’a su kwatanta gaskiya da rikon amana.

Batun cin hanci kan William Ruto ya riga shi isa ga jama’a. An samu damuwa ga yadda ya dinga suka a lokacin yakin neman zabe, har sai da shugaba mai barin gado Uhuru Kenyatta ya ambaci Ruto da sunan ‘barawo’. A matsayin shugaban wajen da ya tara dukiyar dabbobi, kayan gona, gidajen zama da na otel, sabon shugaban kasar bai samu nasarar na zargar sa kan cin hanci da kwatar kasa ba, wanda har ta sanya masu adawa da shi suke kiran sa da “Sarkin Damfara”.

Wata sabuwa kuma, kwanakin baya an umarci mataimakin Shugaban Kasar Kenya Rigathi Gachigua da ya mayar da dala miliyan 1.7 ga lalitar gwamnati saboda hannu a wasu aiyukan cin hanci da rashawa da yake da shi.

Fari da bukatar gaggawa ga aiyukan jin kai

A karshe, sabon Shugaban Kasar ai fuskanci sabbin abubuwa da dama masu wahalarwa na sauyin yanayi. Wasu bangarori na arewaci da gabashin Kenya na fuskantar matsanancin fari da ba a taba samun irin sa a shekaru 40 da suka shude ba. Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa a kalla akwai mutane miliyan 2.5 da suke fama da rashin cimaka, sama da yara kanana ‘yan kasa da shekaru biyar su dubu 460,000 da a kalla mata masu juna biyu dubu 90,000 na fama da matsanancin rashin abinci.

Tattalin arziki a wadannan yankuna na Kenya, wadanda suka dogara kan noma da kiwo, ya shiga mawuyacin hali.

A kalla kaso 50 na shanun da ake kiwatawa a kasar sun kare saboda karancin ruwa da ciyayi. Hatta namun daji ma ba su tsira ba: A yanzu ba a ci ka samun dabbobi irin su rakumin dawa da bauna ba dake dogaro kan ciyayi. Makiyaya na sayar da dabbobinsu don su samu su rayu.

A kokarin mayar da martani ga “annobar kasa”, tsohon Shugaban Kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya kafa Hukumar Magance Fari ta Kasa (NDMA) a Nairobi. Gwamnati da Kungşyoyin Kasa da Kasa ne suke daukar nauyin hukumar mai bayar da aiyukan jin kai, tana fama da matsalolin kudade.

Wannan na bayyana irin kalubale da matsalolin tattalina rziki da aiyukan jin kai da William Truto zai fuskanta, wanda suna da dama; Suna daidai da hawa dutsen Kilimanjaro, waje mai tsayi a Afirka.

TRT Français