Baya ga Ingilishi da Swahili, sauran harsunan Kenya sun cakuda cikin wannan harshen na gida/Photo AA

Daga Agnes Wangari

Gina layin dogo na Kenya zuwa Uganda ya janyo fadadar yankunan birni a Kenya tun shekarar 1900.

‘Yan mulkin mallakar Burtaniya ne suka gina titin jirgin kasan daga gabar teku a Mombasa zuwa yammacin kasar da ke Kisumu.

A hukumance sunan titin, Layin Dogon Uganda, kafin a sauya masa suna zuwa Layin Dogon Kenya zuwa Uganda.

Wadannan yankuna sun fara janyo mutane daga kauyuka kuma daga kabilu daban-daban, zuwa cikin birane.

Hakan ya janyo bukatar harshe daya mai gamewa tsakaninsu, a cikin biranen da kuma gonakin da Turawan mulkin mallaka suka mallaka.

Ta haka wani salon harshe gurbatacce ya bayyana a wannan lokacin.

Watakila masu hikima ne cikin mutanen suka kirkiri harshen ta hanyar yawan amfani, ba wai don sun yi nufin hakan ba.

Harshen Sheng, wanda ake yawan kiran sa da saara ta Swahili da Ingilishi, ya fara bayyana ne a Nairobi tsakanin mabambantan mutane a shekarun 1960.

Baya ga Ingilishi da Swahili, sauran harsunan Kenya kamar su Kikuyu da Luyha da Dholuo da Kikimba sun cakuda cikin wannan harshen na gida.

Sheng, wanda ba shi da wani matsayi a hukumance, ya yi fice ne saboda saukin nahawunsa.

An fara amfani da shi ne wajen sadarwa tsakanin mutanen da suka zo daga mabambantan wurare.

A yanzu yana komawa zuwa gamagarin harshe, har ta kai wasu da aka haifa a shekarun 1980 da kuma bayan nan, suna magana da Sheng a matsayin harshen uwa.

Misalin wadannan kalmomi na Sheng masu asali daga wasu harsunan, sun hada da motii (mota), Muarabe: Balarabe, da bien (to).

Harshen Sheng ya dauki hankalin masana daga fadin duniya. Kusan shekara 10 da suka wuce, nazarin Sheng ya mai da hankali ne kan fitarwa da rarrabe yankunan harshen.

Sun hada da bayanan fayyace tsarin harshen da kuma auna rabe-rabensa da tasirinsa kan al’ummar birni.

An taba zargin Sheng da gurbata tsayayyun harsuna kamar Ingilishi da Swahili da sauran harsuna Kenya. An kuma ce yana da tasiri mara kyau ga yaran da ke nazarin Swahili a makarantu.

Amma kuma a yau, ana ganin Sheng a matsayin harshen da yake kawar da kabilanci da kuma hada kan mutane kan turbar harshe guda.

Ana saka shi cikin rukunin salon karin harshen a Swahili, ko kuma harshen matasa.

Amma nazarin da aka fitar a baya sun dauki Sheng a matsayin harshe guda, yayin da a yanzu ake kallon duk wani nau’in harshe da aka gina kan Swahili, a matsayin Sheng.

Akwai ra’ayoyi daban-daban game da matsayin Sheng. Masu goyon bayansa suna cewa yana da matukar muhimmanci ga mu’amalar matsa, saboda yana gusar tarnakin kabilanci.

Masu adawa da Sheng suna kuka da cewa yana janyo bacewar harsunan gaskiya. Kuma sun ce yana da wahalar fahimta ga wadanda ba kwararru ba, ga shi kuma yana janyo koma-baya kan harkokin ilimi a makarantu.

Sai dai kuma, akwai sabani tsakanin tsarin harshen na zahiri, da kuma maganganu kansa.

Wasu mutane musamman a unguwannin marasa galihu da ke Nairobi, ba wai suna amfani da wannan karin harshen a Sheng a maganar baka kawai, amma sukan nuna ajinsu ta hanyar amfani da Sheng a lamuran yau da kullum.

Saboda haka, idan aka ce Sheng bai sauya ba sosai cikin shekara 10 na baya, wani babban bangare na habakar da harshen ya samu yaduwa tsakanin al’ummar Kenya. Wannan yana nuna kushen da ake yi wa Sheng, bai yi tasiri ba.

Sheng yana yaduwa a wajen Kenya ta dalilin 'yan Kenya mazauna kasashen waje, da kuma yawaitar shafukan intanet masu amfani da harshen tare da Swahili.

Agnes Wangari malamin jami’a ne mai koyar da Tarihi da Harshe a Jami’ar Strathmore a Kenya.

TRT Afrika