Daga AAA Majid
A wannan makalar, zan nuna yadda harshen Swahili yake tare da nazarin yadda ya taso har ya zama harshen sadarwa a Afirka.
A nan gaba kadan, ya kamata harshen Swahili ya hau wani babban matsayi, kuma ya taka babbar rawa a cikin Afirka.
Abin ban sha’awa shi ne amfani da harshen Swahili ya samu sabuwar gudunmowa, bayan da UNESCO ta amince da shi kuma ta ayyana Ranar Harshen Swahili ta Duniya a duk bakwai ga watan Yuli.
Wannan wata gagarumar nasara ce ga Swahili, saboda ya kafa sabon tarihi fitacce a tsakanin harsunan nahiyar Afirka.
Harshen Swahili ya samu muhimmiyar karbuwa har a wajen hamshakan gidajen jarida kamar su BBC da DW da VOA da French Radio da Japan da China da UN Radio, da TRT da sauransu. Duka wadannan suna da tasoshin harshen Swahili zalla.
Akwai wasu abubuwan da suke taimakawa sosai wajen habakar harshen.
Gasanni da wasanni da tarukan siyasa da harkokin tattalin arziki duka sun ba da gudummowa matuka ga manyan harsuna a wajen yada labarun wasannin kwallon kafa.
Gasar Kofin Kwallon Kafa ta 2022 da aka yi a Qatar, da kuma wanda aka yi a baya a Afirka ta Kudu sun kasance manyan misalai na yadda harshen ke tattaro masu jin sa cikin murya daya.
A fagen siyasa kuwa, Majalisar Gabashin Afirka tana amfani ne da harshen Swahili don tattaunawa a zauren majalisar.
Za a iya alakanta habakar harshen Swahili a Afirka kan saukinsa, da saukin koyonsa. Hakan yana bayyana cikin tsarin nahawu da ginin jimla da sautin harshen.
A yanzu sauran kasashe suna fahimtar cewa harshen yana da saukin koyo. Sakamakon haka, baki sukan koyi harshen ba tare da wata wahala ba.
Kungiyoyin kasa-da-kasa masu yawa sun yi ta tura mutane zuwa kasashe kamar Tanzania da Kenya don su koyo harshen, tun a shekarun 1960.
Sakamakon wannan, harshen Swahili bai kebanta ga nahiyar Afirka ba kadai, yana samun karin masu amfani da shi, har a Turai da Amurka.
Rahotanni masu dama sun nuna yadda dalibai Turawa da Amurkawa suke zabar harshen Swahili a matsayin harshen Afirka da za su koya a karatunsu na jami’a.
Haka nan kuma, akwai rahotannin da ke nuna cewa wasu hukomomin soji a wajen Afirka suna koyo da koyar da Swahili domin dalilan tsaro.
Harshen Swahili yana cikin manyan harsuna 10 na sahun-gaba cikin harsuna 6,000 da aka fi magana da su a duniya.
Kari a kan haka shi ne Swahili harshen hukuma ne a Tanzania da Kenya da Uganda da kuma Jamhuriyyar Dimukradiyyar Congo.
Jami’o’i da yawa a kasashen Afirka kamar su Afirka ta Kudu da Rwanda da Malawi da Ghana da Zimbabwe da Burundi da Kenya da Uganda duka sun shigar da Swahili cikin tsarin karatunsu.
Akwai karin shirye-shirye don ganin an fara amfani da harshen a Namibia da Arewacin Afirka. Babu wani harshe mai asali a Afirka wanda ya cimma wannan kyakkyawan cigaba.
Bugu da kari, ranar 9 ga watan Disamban 2022, an kafa tutar harshen Swahili a kan Dutsen Kilimanjaro, wanda ya zamanto kololuwar waje da ke doron nahiyar Afirka.
Wannan wata alama ce da ke nuna dacewar muryar harshen ta watsu zuwa duka fadin nahiyar Afirka.
Farfesa Aldin Mutembei na Jami’ar Dar es Salam, shi ne ya kirkira da kuma aiwatar da wannan kudiri, tare da hadin gwiwar gwamnatin Tanzania da kuma kamfanoni masu zaman kansu.
Ba a raba daya biyu, bayan la’akari da abubuwan da suka bayyana, hobbasan da shugabannin siyasa a Tanzaniya da kuma wasu ‘yan kasashen waje kamar shugaban ‘yan adawa a Afirka ta Kudu, Julius Malema da sauran masu ruwa da tsaki suka yi, harshen Swahili yana da babbar damar ya zamanto harshe mafi muhimmanci wajen sadarwa a Afirka, sama da kowane harshe da ke nahiyar.
Sai dai duk da wannan fata da aka ambata a nan, akwai kalubalen da ke hana harshen Swahili hanzarin samun yaduwa a nahiyar.
Wadannan kalubale sun hada da kangin tunani irin na masana da ‘yan siyasa da shugabannin Afirka.
Mummunan tunanin ya samo asali ne daga raunin basira, sakamakon mugun tasirin sabon salon mulkin mallaka.
Wani karin dalili shi ne tsoron kar a bar mu baya a harkokin fasaha, da rashin kishin kasa da kishin Afirka, da tsoro mara dalili ko tsanar sabon abu ko wanda ba a fahimta ba, da talauci, da ma wasu tarin dalilan.
Amma kuma, akwai alamu masu yawa da ke nuna cewa harshen na Swahili yana da shuhura a yau, sama da yadda yake a baya, sakamakon juyin da aka samu a tattalin arziki da siyasa da zamantakewa.
Idan za a dauki wani babban mataki a yau, harshen Swahili zai zama wakilin muryar nahiyar Afirka.
Wannan shi ne harshe daya tilo wanda ke da asali a Afirka, wanda kuma yake da wannan dama.
(AAA Majid malami ne mai koyar da yaren Kiswahili da adabi a Jami'ar Musulunci ta Morogoro a Tanzania)