Batula ita ce mace daya tilo da ke aiki a matsayin direba a tsakanin sansanin 'yan gudun hijira na Hagadera da kuma Babban Asibitin Garissa a Kenya. Hoto: Batula Ali

Daga Dayo Yussuf

Garissa yanki ne da ke Arewacin Kenya wanda yake daya daga cikin wurare a kasar da suka fi zafi, inda a wasu lokuta yanayi yake kaiwa maki 40 a ma'aunin selshiyos. Kasar wurin fayau take kuma a bushe take, sannan akwai tsaunuka.

Kasar wurin tana da kyau a fannin aikin gona, inda mazauna wurin suke noma da kiwon dabbobi.

A koyaushe direbobi suna bai wa dubban rakuma da tumaki da awaki hanya domin tsallaka titi da taimakon makiyayan da ke zaune a yankin.

Daya daga cikin direbobin da ke bin wannan hanyar ita ce Batula Ali Abdullah. A matsayinta na mace mai tuka motar daukar marasa lafiya, Batula tana nuna wa jama'a cewa za ta iya wannan aiki wanda maza suka fi yin sa.

Idan ka yi tafiyar kimanin kilomita 10 daga gabashi ne za ka samu sansanin 'yan gudun hijira na Hagadera. Babban sansanin 'yan gudun hijira ne da ya kunshi mutane 100,000, inda adadin yake karuwa a kowace rana.

Wadanda suke zaune a wannan dadadden sansanin 'yan gudun hijira mutane ne da suka fuskanci bala'in fari ko kuma matsalar rashin tsaro daga al'ummominsu galibinsu mata da kananan yara.

Batula tana aikin tukin ne tsakanin sansanin 'yan gudun hijirar da Babban Asibitin Garissa, inda take bayar da daukin gaggawa da marasa lafiya da suka fi bukata.

Ceton rayuka

"Na kasance direba tsawon shekara 15. Na yi aiki a matsayin direba a ma'aikatar ayyuka tun shekarar 2019, na fara aikin a matsayina na direbar motar asibiti," kamar yadda Batula ta shaida wa TRT Afrika

A wasu lokuta Batula tana tuka marasa lafiya akalla 15 a rana. Hoto: Batula Ali

Batula ita ce kadai mace da take tuka motar daukar marasa lafiya a yankin kuma tun lokacin da ta fara tuka motarta ta farko a 2019, ba ta taba gajiyawa ba. "Nan ne abincina yake," in ji ta.

"Ina jin dadi idan na ga yadda nake taimakon mutane wajen kai su wurin da za a ba su agajin gaggawa. Na dauki mata wadanda suke gargarar mutuwa. Na garzaya da su asibiti kuma an ceci rayuwarsu," in ji ta.

Batula ba ta taba tsammanin za ta yi aiki a fannin kowon lafiya ba. Amma a shekara hudu da suka wuce ta tsunduma a fannin.

A wasu lokuta Batula tana tuka marasa lafiya 15 a rana. Tana alfahari da gudunmawar da take bayarwa wajen ceto rayukan jama'a da suke cikin mawuyacin hali.

"Na taba taimaka wa wasu mata sun haihu kuma na taimaka wajen yanke mahaifa. Na ji dadi cewa ni ma na taimaka," in ji ta.

Mata suna jin farin ciki

A yanzu Batula tana da burin zurfafa iliminta a fannin kiwon lafiya ta hanyar samun horo. "Ina tunanin zuwa na samu horon zama ma'aikaciyar jinya ko ungozoma. Ina ganin babban abu ne ka taimaka wajen kawo mutum wannan duniyar. Hakan abu ne mai dadi," in ji ta.

Batula ta ce ta sha wahala kafin a yarda da ita a matsayin mai tuka motar marasa lafiya. Hoto Batula Ali

Labarin Batula ya karade kasar Kenya da kuma wasu yankuna a makwabciyar kasar Somaliya. Ta ce yawancin matan suna farin ciki idan ita ce take tuka motar.

"Mata 'yan asalin Somaliya ba sa sakin jiki idan huldar aiki ta hada su da maza. Idan ina wajen kuma zan iya taimakawa, suna yin farin ciki sosai. A wasu lokutan ma suna tambaya ina nake," kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.

Wasu suna cewa wannan ya nuna akwai bukatar kara samun mata a fannin kiwon lafiya da bangaren ba da agajin gaggawa. "Ina fatan ganin karin mata da 'yan mata a wannan fanni. Za su iya aikin," in ji ta.

Shawo kan kalubale

Batula tana karfafa wa 'yan mata daga yankin gwiwa, inda hakan yake sa su ganin cewa abu ne mai yiwuwa a kara yawan direbobi mata masu tuka motar daukar marasa lafiya da ma'aikatan fannin kiwon lafiya.

"Idan 'yan mata suka ganni 'ina tafiya da gudu' a motar daukar marasa lafiya da jiniya, sai su yi shewa. Sai su tambaye ni ko su ma za su iya zama direbar motar daukar marasa lafiya," in ji ta.

Ta ce ta sha wahala kafin mutane su yarda da ita a matsayin direbar motar daukar marasa lafiya.

Batula ta ce a farko ta fuskanci kalubale daga wasu 'yan gidansu da wasu mutane wadanda suke ganin tana wuce iyaka.

"Da farko ba su fahimci abin ba. Amma a yanzu suna farin ciki da ni. Suna alfahari da aikina."

Aikin mai tuka motar marasa lafiya yana bukatar sadaukar da kai kuma yana cin lokaci a wasu lokuta, inda a wasu lokuta za a kira ka a tsakiyar dare. Batula ta ce wadannan suna daga cikin kalubalen da take fuskanta.

Ko da yake, ta ce hakan ba sanyaya mata gwiwa sai dai ma kara karfafa mata gwiwa da yake yi. Ta yi amannar cewa bayan farin cikin da take samu saboda aikin, mutane da yawa suna alfahari da ita saboda kula da karfafa gwiwa.

TRT Afrika