Daga Toby Green
Shekaru hudu kenan da hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ayyana Covid-19 a matsayin annoba da ya haifar da barazana ga duniya.
Kazalika a karshen watan Janairun nan ne nahiyar Afirka ke cika shekaru hudu tun soma daukar matakan yaki da annobar ta Coronavirus: kasar Rwanda ta dauki matakin rufe iyakokinta ta hanyar soke tashin jiragen sama zuwa China a ranar 31 ga Janairu 2020.
A firgicin farko da aka shiga sakamakon bullar sabuwar cutar, masu sharhi da dama sun yi kwatance da kasashen Guinea da Laberiya da saliyo wadanda suka yi fama da barkewar cutar Ebola a shekarar 2014 zuwa 2015 a matsayin misali mai kyau ta yadda za a iya shawo kan duk wata cuta mai tsanani da ta barke.
Duk da cewa lokaci ya ɗan ja, a bayyane yake cewa fannin kiwon lafiya ta duniya ba ta dauki wasu darussa ba daga abubuwan da suka faru a baya.
A zahiri, irin martanin da aka dauka kan annobar Covid-19 ya janyo bala'i a Afirka
Kamar yadda Birtaniya ta mai da hankalinta sosai kan binciken cutar Covid-19, akwai bukatar Afirka ta dauki irin wannan mataki cikin gaggawa,
Yana da matukar muhimmaci a gudanar da sahihin bincike don tabbatar da cewa ba a sake daukar shawarwarin da kasashe masu arziki suke baiwa Afirka ba.
Ko da yake wasu masu sharhi sun yi nuni da karancin mace-macen da aka samu sanadin Covid-19 a Afirka a matsayin wata alama ta nasarar da nahiyar ta samu wajen shawo kan cutar, sai dai akwai bukatar sake yi lamarin kallo na daban.
Darussan Ebola
La'akari da matsakaicin shekaru kasa da 20 na mutanen da take da su, Afirka tana da damar samun karancin adadin mutuwa daga Cutar Covid-19.
Wannan ba alama ba ce ta nasara, la'akari da irin bala'in da ya auku a lokacin da ake tunanin cewa Covid-19 zai zama barazana irin daga a Afirka kamar yadda ya kasance a wasu wurare.
Kuskuren farko da aka samu ya biyo bayan zaman kullen gida da aka yi, wanda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ingiza a cikin rahoton bincikenta kan gano ainihin gaskiyar abin da ya faru a Wuhan a ranar 25 ga watan Febrairu shekarar 2020, inda ta ba da shawarar cewa duk kasashen da suka samu bullar cutar Covid-19 su bi tsarin China na zaman Kulle.
Duk da cewa an taba gwada zaman kullen gida a Freetown da Monrovia yayin barkewar cutar Ebola.
Manyan kungiyoyin sa kai kamar Doctors Without Borders sun ba da shawarar adawa da wannan mataki a lokacin, sannan wasu binciken ilimi da aka gudanar sun nuna rashin tasirin yin hakan - duba da cewa ba zai yiwu a ci gaba da hakan a wuraren da tattalin arzikin al'umma ke da mahimmanci ba.
Ba shakka WHO na da masaniya kan Ire-iren wannan bincike, amma duk da hakan ta ba da shawarar a dauki wadannan matakai a kowane yanayi, ba tare da la'akari da tattalin arziki da abubuwan more rayuwa da zamantakewa ba.
Kuskure na biyu babba shine watsi da kididdiga al'umma, a karshen watan Maris ne masu sharhi suka bayyana cewa matsakaicin shekarun mutanen Afirka na nuna Cutar Covid-19 ba za ta yi wani tsanani a yankin ba.
Matsugunai masu cunkotso
An yi watsi da wannan bincike, don mara wa dabarun kawar da cutar baya wanda ba za a taba samun nasara a kai ba a kasashe da matsugunansu ke da cunkotso da hakan zai yi matukar wahala a iya kawar da bullar wata cuta da ta shafi numfashi.
Kuskure na uku da aka tafka shi ne dokar hana fita. Hana zirga-zirgar mutane a wasu lokutan rana a matsugunan da ake da matukar yawa - a Nairobi da Legas da Kinshasa- ba su da wani takamaiman dalili na daukar wannan mataki.
Cutar ta fi saurin yaduwa a wuraren da ke rufe, don haka tilasta wa mutane zama a wurin da akwai cunkotso na nufin kara yaduwar cutar. Ana iya dora alhakin dukkan wadannan kan kurakuren kimiyya.
Hakan na da nasaba da batun da ke nuna tasirin yawancin masana kimiyya da ke ba da shawarwari a WHO da sauran manyan kungiyoyi duk suka fito daga kasashe masu arziki, don haka, ba su fahimci yanayin zamantakewar al'umma a biranen nahiyar Afirka ba.
A zahiri, wannan manufa ce ta mulkin mallaka, ta hanyar dogaro da cibiyoyin Afirka ke yi kan kudaden da suke samu na taimako daga kasashe ketare da China.
Ansa bukatar a gaggauta gudanar da cikakken bincike kan cutar Covid-19 a Afirka bawai a takaita shi kan lamuran kimiyya kadai ba.
Kuskure na hudu da aka samu ya biyo bayan watsi da bututuwan da suka shafi lafiyar al'umma - yanayin zamantakewar da kimiyya da magunguna ya kamata suka kasance.
Tabarbarewar tsarin kiwon lafiya
Masana kimiyyar zamantakewa sun dade da sanin cewa arziki da lafiya suna da alaka da juna.
A matalautan kasashe, dangantakar da ke tsakanin ma'aunin tattalin arziki na GDP da bukatun yau da kullum na rayuwa ya bayyana a fili tsawon shekaru da dama, kamar yadda tsarin ''Prescott curve'' ya bayyana.
Kamar yadda Shirin samar da abinci na duniya WFP a yanzu ya bayyana cewa fiye da rabin wadanda ke fama da matsananciyar yunwa sun shiga cikin wannan yanayin ne tun daga shekarar 2020.
Kazalika shirin samar da ci gaba na Majalisar Dinkin Duniya UNDP ya ce 'yan Afirka miliyan 50 sun shiga matsanancin talauci a lokacin Covid, don haka a bayyane yake cewa manufofin da WHO da kungiyoyi masu karfi a Masana'antar kiwon lafiya ta duniya suka dauka sun lalata tsarin lafiyar jama'a a Afirka.
Baya ga wadannan akwai wasu karin muhimman abubuwa da dole a yi la'akari da su. Na farko, akwai rufe makarantu da tasirinsa da kuma aikin azabtar da yara. Na biyu, tasirin hana zirga- zirga da ayyukan noma .
Na uku kuma, akwai “annobar cututtuka” kamar cin zarafi da suka shafi jinsi wadanda matakan suka haifar. Na hudu, akwai tasirin dakatar da zirga-zirgar ababen hawa a duniya da kuma sake fasalin abubuwan da suka fi dacewa a mai da hakali akan su ta hayar samar da magunguna masu mahimmanci ciki har da gwajin gaggawa na zazzabin cizon sauro, wanda har yanzu ba a wadata da shi ba.
Ko shakka babu cewa binciken Afirka kan Covid zai bukaci gagarumin aik, kuma wani muhimmin abu da yake a bayyane shine: duk wanda zai yi aiki akan hakan, ba zai zama WHO ko wata cibiya ketare ba wacce ke da muradin shigar da irin wadannan munanan manufofin a nahiyar.
Marubucin, Farfesa Toby Green, masanin tarihin Afirka ta Yamma da kuma rashin daidaito a duniya. Na daga cikin marubutan littafin "The Covid Consensus: The Global Assault on Democracy and the Poor-A Critique from Left"
Togaciya: Ba dole ba ne ya zama ra'ayin marubucin ya yi daidai da ra'ayi da ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika.