Wani mai zanga-zanga rike da tutar Haiti a lokacin da suke zanga-zangar adawa da Firaminista Ariel Henry da rashin tsaro a Port-au-Prince da ke Haiti a ranar 1 ga Maris na 2024. (REUTERS/Ralph Tedy Erol)./Photo: Reuters      

A farkon watan nan ne wasu gungun mutane suka kai farmaki a gidajen yarin Haiti biyu, inda suka tseratar da fursunni 4,500, sannan suka yi sace-sace a gidajen mutane da asibitoci, sannan suka kona motoci da ofisoshin ’yan sanda da wasu gidaje.

Haka kuma an taba kai farmaki a filin jirgin saman kasar. ’Yan sandan kasar da alama lamarin ya fi karfinsu.

An kashe gomman mutane, sannan an raba dubbai da muhallinsu. Yanzu ’yan daban suna ganin sun isa, kuma za su iya yin komai.

An saka dokar ta baci na kwana uku, aka mayar da ita na wata daya, wadda ta zarce har zuwa yanzu ba a sake ji daga gwamnatin ba a game da dokar. A ’yan kwanakin da suka gabata, birnin Downtown Port-au-Prince ya kasance cikin rudani da rikice-rikice.

Hakan ya sa farashin kayayyaki ya yi sama, sannan wasu kayayyakin sun yi karanci. Amma masu sayar da kayan lambu da sauran abubuwan da ake samarwa a kasar suna cigaba da kasuwancinsu kamar babu komai da ke faruwa.

Haka kuma ’yan daba ba su yi yunkurin kona Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan kasar ba. Har yanzu dai, ana fuskantar barazanar kifewar kasar baki daya.

Shi kan shi Firayiminista Ariel Henry an daina jin ta bakin shi tun bayan tafiyarsa zuwa Kenya, inda ya je domin sanya hannu a yarjejeniyar dauko hayar ’yan sanda 1,000 zuwa Haiti domin magance matsalar ’yan daba.

’Yan Haiti suna zanga-zanga a gaban otel din Marriot, inda suke zargin a nan ne Firayiministan Haiti Ariel Henry yake zama, kwana hudu bayan dawowarsa daga San Juan, Puerto Rico a ranar 8 ga Maris na 2024. (REUTERS/Ricardo Arduengo).

Henry ya bukaci dauko hayar ’yan sandan ne wata 18 da suka gabata a Majalisar Dinkin Duniya, majalisar nan dai da ta gaza wajen daidaita kasar Haiti duk da ayyukanta da dama a kasar.

Henry ya dauki matakin neman taimakon ’yan sandan ne ba tare da amincewar kungiyoyin sa kai ko kuma tuntubar ’yan kasar ba.

Ta hanyar yin hakan, kamar ya amince ne da gazawarsa wajen samar da tsaro ne a kasar, amma kuma yana cigaba da nanata cewa zai cigaba da kasancewa a mulkin domin ’yan sanda za su taimaka masa wajen samun nasarar cigaba da mulki ba tare da hamayya ba.

Firaiminista Henry ya samu kansa a tsaka mai wuya a lokacin da ya isa Jamhuriyar Dominican saboda tsaikon diflomasiyya, inda ya sauka a birnin Puerto Rico a karkashin kulawar jami’an tsaron FBI saboda filin jirgin saman na Port-au-Prince ba ya aiki sosai tun bayan yunkurin da ’yan daba suka yi kwace shi.

Tun wannan lokacin ne kimar Firayiministan ya ragu a kasar ta Jamhuriyar Dominican.

Akwai alamar sojojin Haiti sun samu nasarar taimaka wa ’yan sanda wajen tsayar da hare-haren ’yan daban. Sojojin nan dai su ne wadanda Firaministan ya gaza ba su karfin gwiwar da suke bukata wajen yaki da ‘yan daban wata 18 da suka gabata.

Taswirar Haiti. Makwabciyar ta Gabas ita ce Jamhuriyar Dominican. (TRT World).

Yadda kasar Haiti ta rikice ba kawai wayan gari aka yi da shi ba. Yana da alaka da tarihin kasar da yanayin siyasa da zamantakewarta, da kuma tsare-tsaren mulkin kasar da suka shafi mutanennta da kuma alakarta da kasashen waje wadanda suke hana ci gabanta.

A kowane mataki za ka ga akwai sa hannun mutanen Haiti da Amurka da Turai da Gabas ta Tsakiya da cibiyoyin kudi na duniya da suke taimakawa wajen kara jefa kasar cikin rudani.

Amma akwai kasashe guda biyu da suka fi uwa da makarbiya wajen jefa kasar cikin rudani. Na farko ita ce Faransa, wadda duk da kudin da take zubawa wajen inganta ilimi a kasar, ta cigaba da karbar diyya daga kasar bayan ’yancin kai da ta ba ta, inda ta rika kwashe biliyoyin daloli a tsakanin 1825 zuwa 1889.

Wannan wani bashi ne da Amurka ta biya a lokacin farko da ta mamaye kasar a tsakanin 1915 zuwa 1934 saboda da farko dai, dole na Haiti ta ci bashi daga Faransa da kudin ruwa mai yawan gaske.

Lokacin da Amurka ta zo, sai ta biya sauran bashin da ake bin Haiti, sai ya zama Faransa ba ta bin Haiti bashin kudi, sai bashin ya koma kan Amurka. Amma sai ya zama zafi biyu, ga biyan kudin bashin, ga kuma kudin ruwan da ya taru, wanda kasar ke biyan Amurka da Faransar kuma.

Dan Faransa Baron de Mackau yana mika bukatun kasarsa ga Shugaban Kasar Haiti to Jean-Pierre Boyer, a shekarar 1825 (image courtesy of Victor Duruy).

Wadannan matsalolin tattalin arzikin ba wai an kirkire su ba ne domin wanke mutanen kasar daga tabarbarewar harkokin kasar.

Tabarbarewar harkokin kasar bai rasa nasaba da talaucin da ya yi katutu a kasar tun lokacin da aka fara biyan bashin. Rashin kudin kasar ya sa dole shugabannin kasar ba sa ma tunanin bullo da hanyoyin ciya da kasar gaba.

A lokacin da kasar ke biyan bashi biyu, dole kasar ta daina damuwa da bukatun mutanenta. Idan kuma haka ya faru, dole a samu mutane a kasar wadanda za su iya yin komai domin su rayu.

Don haka, sai muka samu matasan da suke rayuwa a kananan garuruwan kasar, wadanda suka mallaki makamai tun zamanin shugabancin Jean-Bertrand Aristide a shekarun 1990s kuma har zuwa yanzu, wadanda suke da zimmar kare kansu, ko kuma samun wani karfin iko.

Wani soja yana aikin sintiri a kusa da wata alamar hana amfani da makami idan ba a Ma’aikatar Tsaro ba a daidai lokacin da kasar ke cigaba da zama cikin dokar ta baci, a birnin Port-au-Prince da ke Haiti a 6 ga Maris na 2024 (REUTERS/Ralph Tedy Erol).

Haka kuma akwai manoma wadanda suka ki sayar da gonakinsu ga manyan kamfanoni, inda suke cigaba da rike filayensu kamar yadda aka tsara a lokacin karbar ’yancin kai.

Amma kuma a daidai lokacin da suke kin bayar da fulotansu, suna kuma asibitoci da makarantu da wutar lantarki da kimiyya da fasaha domin harkokin nonamsu.

Sai dai kuma duk da hakan ana daurawa manoman haraji mai girma domin tara kudin da za a biya basussukan. Wannan nauyi ne da ke matukar danne mutanen Haiti.

Kimanin shekara 20 da suka gabata, lokacin da Faransa ba ta samu tsaikon zuba kudade a kananan garuruwan kasarta, ta fuskanci kalubale da ta sha mamaki. Duniyar ta ga zahiri a Faransa, amma ta kawar da kai: Cewa rashin inganta rayuwa mutane ko ma a ina ne, yana jawo hargitsi.

Haka kuma lokacin da aka hana mutanen Haiti damar samun ilimi da kiwon lafiya da inganta tattalin arzikinsu, sai kasar ya zama mutanen kasar da za su iya yin komai.

Bayan samun ’yancin kai daga Faransa a shekarar 1804, har yanzu mutanen kasar suna ta kokarin gina kasar ne.

Amurka kawar Faransa ce, amma saboda wani dalilin tattalin arzikinta daban, sai a farko ta ki amincewa da ‘yancin Haiti.

Sai a lokacin Yakin Basasar Amurka a zamanin Shugaban Kasar Amurka Abraham Lincoln ne ta amince da ‘yancin kasar a Yunin shekarar 1862, shekara biyu kafin a haramta kasuwancin bayi a Amurka.

Masu hikima a kasar suna cewa, “Haiti na bin Faransa bashi, Faransa na bin Haiti bashi.” Wannan maganar na nuna yadda mutanen Haiti suke kallon diyyar ’yancin kai da suke biya, da kuma yadda muke kallonsa a matsayin wani bashi da ya kamata mu biya.

Ita ma Faransa akwai bukatar ta kara gane wasu abubuwa a nan gaba sannan ta gyara wasu kura-kurenta.

Ba za mu karanta tarihi, sannan mu yi watsi da shi kamar ba shi da wani tasiri a rayuwarmu ta yau ba.

Ba don kasashen da suka kalubalanci kasashen Jamus da Italiya da Japan a Yakin Duniya na biyu sun sauka a yankin Normandy ba, da yanzu nahiyar Turai na cikin wani halin daban.

Ba don an kirkiri tsarin Marshal Plan ba, wanda aka yi a Amurka domin agaza wa kasashen Yammacin Turai, da sake gina Turai bayan yakin sai ya dauki dogon lokaci.

Turawan Amurka sun iso Haiti ne a shekarar 1915, inda suka yi shekara 19. A wannan lokacin, an cigaba da abubuwa ba daidai ba: Ana sace zinaren Haiti, ana tursasa mutanen kasar aikin karfi, da fifita kamfanonin Amurka, da sake dawo da nuna wariyar launin fata da rashin daidaito (dukkan shugabannin kasar Haiti na lokacin ruwa-biyu ne), sannan a lokacin ne aka fara shiga cikin lamarin tsaron kasar da siyasarta da tattalin arzikinta.

Jirgin ruwan Amurka (PG-5) da ke safarar zinaren Haiti zuwa birnin New York. (Photo courtesy of US Navy - Naval Historical Center).

Har yanzu ba a daina wannan tsarin na danniya ba: ko dai Amurka ta kawar da kanta a kan abubuwan da suke faruwa a kasar, ko kuma ta shiga lamarin ta hanyar kakaba wanda take so ya zama shugaban kasar kamar yadda aka yi a lokacin mulkin kama-karya na François Duvalier.

Misali, lokacin da aka dawo da Shugaban Kasa Jean Bertrand Aristide daga gudun hijira daga Amurka a shekarar 1994 da rakiyar sojojin Amuka, mulkinsa ya rage haraji a kan wasu kayayyakin da ake shigo da su, wanda hakan ya bude kofar shigo da kayayyaki daga Amurka, maimakon karfafa amfani kayayyakin da ake samarwa a cikin kasar.

Masana’antun Haiti ba za su iya ja da kayayyakin da ake shigo da su ba, wadanda farashinsu bai kai kudin da ake kashewa wajen samar da su ba a gida. Haka kuma Amurka na cigaba da fargabar kada wanda ba nasu ba ne ya dare kan karagar mulki.

Abin da muke gani a shekara biyu da suka gabata na wannan gwamnatin shi ne Amurka da kawayenta suna so duk rintsi su cigaba da rike madafun ikon kasar, duk da cewa a zahiyi Henry ya zaga wajen samar da tsaro a kasar.

Masu zanga-zanga a birnin Port-au-Prince suna kira ga Shugaban Kasa Jovenel Moise ya sauka saboda cin hanci da rashawa da tsadar rayuwa da rashin gas a ranar Juma’a, 4 ga Oktoban 2019. (AP/Rebecca Blackwell).

Tun ma kafin zamanin Ariel Henry, an fara samun matsala a kasar ne tun bayan kutsen da aka yi zaben Shugaban Kasar na 2011, inda da karfi da yaji dan takarar Jam’iyyar Haitian Bald Head Party (PHTK) ya samu nasarar lashe zaben.

Shi kan shi Darakta Janar na Hukumar Zaben, ya tabbatar da kutsen da aka samu a wata tattaunawa da ya yi a Port-au-Prince.

Tun lokacin da PTHK ta fara mulki, aka fara samun koma-baya, inda aka fara samun habakar shigo da makamai daga Amurka ga ’yan daba, da karuwar cin hanci da rashawa tsakanin ma’aikatun gwamnati da masu zaman kansu ta hanyar cewa wai kasar Haiti tana kasuwanci ne mara shinge.

Ta hanyar daina sauraron kungiyoyin sa kai, sai ya zama kama Amurka na daba wa kanta wuka ne.

Idan har Amurka ba ta fito ta ba da hakuri ba, ba za a taba mantawa cewa kasar Haiti ta tabarbare ne a lokacin da ita Amurkar ta fara sanya baki a harkokin zabenta.

Abubuwan da suke faruwa yanzu sun nuna cewa akwai bukatar a sauya wasu tsare-tsaren kasar a game da tallafin da take samu. Idan ba haka, kasar za ta cigaba da kasancewa cikin rudani ne.

Kamar sauran kasashen, ’yancin mutane na tsara yadda suke son rayuwa da aka gindaya a Majalisar Dinkin Duniya bayan Yakin Duniya na biyu yana kunshe da kare hakkin mutanen kasar, kare yadda take a yanzu da kuma tsara yadda za ta kasance a gaba.

. Lallai mutanen Haiti dimokuradiyya suke so, kamar yadda na gano a wani bincike da na gudanar wanda zan fitar nan gaba kadan. Amma suna da shakku a kan irin dimokuradiyyar da ake yi a kasar a yanzu.

Babu shakka kasar Haiti, wada tafiyar jirgin saman minti 90 ce kawai tsakaninta da Amurka za ta cigaba da zama kawar Amurka, amma akwai bukatar kawancen ya zama kowa na cin riba.

Dole kasar ta bunkasa masana’antaunta, da tallata kayayyakin da take hadawa a cikin gida, sannan ta rage dogaro da kayayyakin da ake shigo da su daga kasashen waje.

“Matsalar tsaron da muke fuskanta yanzu na bukatar agaji domin ba mu da isassun ma’aikata da kwarewar da za mu yaki matsalar. Amma duk da hakan, a bangaren maslahar lamarin a siyasance, ba a bukatar sa hannun kasashen waje.”

Su kansu mutanen kasar ba za a wanke su ba daga wannan matsalar. Bayan rashin tabbas na kasar da sa hannun Amurka ye jefa su, akwai rashin ingantattun ’yan siyasa a kasar. Ba su da tsari mai kyau, sannan suna da saukin juyawa saboda a shirye suke su yi komai domin su dare karagar mulki.

Matsalar tsaron da muke fuskanta yanzu na bukatar agaji domin ba mu da isassun ma’aikata da kwarewar da za mu yaki matsalar. Amma duk da hakan, a bangaren maslahar lamarin a siyasance, ba a bukatar sa hannun kasashen waje.

Kasar na bukatar sababun ’yan siyasa domin ana bukatar sababbin tsare-tsaren kawance da alaka da wasu kasashen domin gujewa aukawa irin kuskuren da aka yi a baya.

Sannan ba kamar yadda ake bayyanawa ba, akwa miliyoyin mutane a kasar wadanda suke kaunar kasarsu sosai, sannan suke da burin aiwatar da duk abin da suka dace domin dawo da kasar kan turbar kwarai.

Kar a manta, kasar Haiti tana da wani taririn zama na farko wajen dakatar da al’adar mallakar mutum ya mallaki mutum da ake kira servitude a Ingilishi.

Marubucin, Yvens Rumbold, daraktan sadarwa ne na wata kungiyar kwararru a Haiti. Yvens ya karanci sadarwa a Amurka, sannan ya samu kwarewa na dan lokaci tsare-tsaren al’adu a Faransa da tsare-tsaren mulki a Amurka, da kuma harkokin kasuwancin a Austria da Qatar.

TRT Afrika