Wani mayaƙin lyan tawaye yana taka kan gunkin tsohon shugaban Syria Hafez al-Assad, wanda aka ruguza a wajen hedikwatar Ma'aikatar Tsaro da ke gundumar Kafr Sousa ta Damascus ranar 9 ga Disamba, 2024. / Hoto: AFP

Har yanzu ina tuna tafiyata ta farko zuwa Aleppo, Syria, ranar 28 ga Yuni, 2001. Ina kamar ɗan shekara bakwai.

An fara hutun makaranta a Sifaniya, kuma kamar da yawan iyalai da ke rayuwa a wajen Syria, mahaifina Fathallah, yana tara kuɗi duk shekara saboda wannan tafiya.

Tafiya ce mai tsada, musamman ga iyalai da ke da yawa. Amma ba ya taɓa daina ba mu labari game da Syria: kan Aleppo, musamman Al-Bab, da al'ummar garin, da mabambantan ƙabilu da addinai, da tarihi, da ɗanɗano.

Kuma wannan ya sanya ƙauna, da alaƙarmu da ƙasarmu, wadda ya assasa a zukatanmu tamkar shi.

Yakan ce ya kamata mu so birnin Madrid, amma ba tare da manta inda muka fito ba. Yana da burin wata rana ya samu ikon komawa Syria.

Yana mafarkin gina asibitoci da makarantu da masallatai, da cibiyoyin jinƙai.

Amma mafarki ne mai wahala, kuma ya sani. Syria ta kasance cikin ƙunci tsawon shekaru ƙarƙashin mulkin jam'iyyar Baath, kuma mahaifina, kamar sauran tarin mutane, an tilasta masa barin ta a 1969.

Ba don yana so ba, amma saboda ba shi da wani zaɓi.

Inas al Hachem da ita da Maryam, wata matashiya tsatson Syria da Sifaniya, waɗanda babansu si ma daga Aleppo yake. Hoto: Inas al Hachem

Tare da tallafin danginsa da kuma nasa ƙoƙarin, ya kammala digirin likitanci a jami'ar Complutense University ta Madrid, yayin da yake aiki don ɗaukar nauyin kansa.

Ba ya gajiyawa da tuno Syria. "Yanto al'ummarsa abu ne da ake yawan ji a maganganunsa.

Yaƙin basasa

Mu koma zancen tafiyata ta farko zuwa Syria. Ina tuna yadda ta yi tasiri kai na. Komai ya burge ni kuma ya ƙayatar da ni, amma abin da ya fi jan hankalina shi ne hotunan Shugaba Bashar Al-Assad, a duk inda ka shiga.

Na tambayi me ya sa hotunansa ke ko'ina, sai mahaifiyata da yayana suka ce, "'Yi ƙasa-ƙasa da muryarki," saboda su sun koyi darasi a tafiye-tafiyensu na baya.

Tamkar ba za a iya ambatar Assad idan ba yabon sa za a yi ba.

Lokacin da juyin juya-hali ya ɓarke a 2011, tamkar mafarkinsa ya fara zama gaskiya ne.

Mun laru da fatan abubuwa za su sauya game da mu. Mun bibiyi labarai kullum, muna kallon labaran yaƙin a Al Jazeera.

Da fari, mukan kira danginmu don taya juna fatan alheri da jin sabbin labarai, amma daga baya sai labarun suka koma munana marasa iyaka: hare-haren bam da kame da ɓatan mutane. Mun rasa mutane da dama.

Kawuna na wajen uwa, Mahmoud, wani likitan dabbobi mai 'ya'ya shida, ya mutu a harin bam yayin zanga-zanga a Aleppo.

'Ya'yan baffana biyu, Firas da Hasan, sun ɓace, kuma ba mu ga gawarsu ba balle mu bizne.

Ɗan baffana Amani, Ali Rakan, shekarunsa 14 kacal, gwamnati da sojin Rasha sun halaka shi. Wani baffana kuma ana kama shi.

Bayan tsawon lokaci, damuwarmu ta ragu ta koma kyakkaawan fata. Amma mahaifina bai daina mafarki ba. Dun matakin da 'yan tawaye suka ɗauka tamkar dominsa ne.

Ya ce nasara ta zo kusa. Ba mu taɓa tunanin wannan fafutuwa za ta ƙare a shekaru 14 ba. Sai dai mahaifina bai rayu har ya ga wannan ba, saboda ya rasu shekaru uku baya.

Ƙarshen Assad

Daga nan, ranar Lahadi komai sai ya sauya. Dare 8 ga Disamba zai zama abin tunawa. Lokacin da babbar binin Damascus ya zo hannu, labarin ya cim mana da ƙarfe 5:30 na safe awanni biyu kacal na barci. Mun san wannan zai zama ƙarshen Assad.

Za ka ga yayana da ni a nan Istanbul muna kallon TV, muna bibiyar labaran. Muna kuma neman sabbin labarai a Twitter da Instagram.

Muna hirar bidiyo da dangi —wasu a Madrid, wasu a Qatar, Norway, Syria, Jamus… duka a faɗn duniya. Dun wata ƙarin nasarar 'yan tawaye ta zamo abin murna.

Da ƙarfe 3:30 na safe, ina gyangyaɗi, amma ina ankare, har sanda yayana ya tashe ni bayan kamar awanni biyu, yana kukan farin ciki: "Bashar ya tafi! Bashar ya tafi!" Mun ɓarke da murnar da ba zan iya misaltawa ba. Dariya, hawaye, da runguma. Mun kasa komawa barci.

Mun fita titi a Istanbul, muka je kusa da Fatih, inda tarin al'ummar Syria da aka ɗaiɗaita suke rayuwa. Mutane suna raba alawa, masamman halawet el jibn, wata alawar gargajiya.

Wasu kuma suna waƙa "Al'ummar Syria al'umma ɗaya ce…, ɗaya, ɗaya" suna murna. Duk da ba mu san juna ba, a ranar mun zamo dangi.

Mun taya juna murna. Bayan tarin wahala, mun haɗu muna murna kan nasara ɗaya, muna kyautata fata tare.

Masu zanga-zanga suna kuwwa suna ɗaga tutar tawayen Syria, wadda ake kira da tutar juyin juya-hali, suna taro a Trafalgar Square, tsakiyar London, ranar 8 ga Disamba, 2024, don murnar kawar da gwamnatin al Assad (AFP).

A ƙarshe, 'yan Syria sun cancanci sake farin ciki. Mun daina kasancewa 'yan gudun hijira, mun sake zama al'umma mai matsuguni, mai suna, mai kyakkyawan fata.

Mun shirya wa gobe

Syria, ko kuma kamar yadda muke son kiran ta, Sham, ƙasar Jasmine, za ta zama abar tunawa saboda kyawunta, da tarihinta, da daɗaɗɗen cigabanta, da al'adunta, ba wai yaƙe-yaƙenta ba.

Na san abin da ke gabanmu ba mai sauƙi ba ne. Gina ƙasar da ta baro yaƙi ba shi da sauƙi. Amma dai alal aƙalla, a karon farko cikin shekaru, muna da abin yin alfahari da fata kan gobe.

Ina ganin duk waɗanda muka rasa, da waɗanda suka ba da rayuwarsu kan wannan, daga Hamza al-Khatib, shahidin farko na juyin juya-halin, wanda aka azabtar aka kashe a Daraa don kawai ya rubuta "'yanci" a jikin bango, zuwa Abdul Baset al-Sarout, wanda jigo ne na wannan gwagwarmaya.

Wani tsohon gola na tawagar ƙwallon ƙafa ta Syria, muryarsa tana rangaɗawa a titunan Homs, a wata bajinta da ya yi wadda ta halaka rayuwarsa.

Ina tuna mahaifina da murmushin, saboda na san shi ma yana murmushi. Na gode wa Allah.

Kuma tabbas, tuni muka fara shirin tafiyarmu ta gaba. Saboda a yanzu, a ƙarshe, za mu iya sake ziyartar Syria da Aleppo. A wajenmu, haka yake kamar yadda yake a gare shi.

Asali an buga wannan maƙala a TRT Espanol.

Marubuciyar, Inas Al HashemI mataimakiyar mai gabatarwa ce a TRT Español.

Togaciya: Ra'ayoyin da marubuciyar ta bayyana ba sa wakiltar mahanga, da ra'ayoyin eidtocin TRT Afrika.

TRT Afrika