Türkiye
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya ya gana da shugaban sabuwar gwamnatin Syria
Ganawar da suka yi a ranar Lahadi a Damascus babban birnin kasar Syria, na zuwa ne makonni biyu bayan hamɓarar da gwamnatin Bashar al Assad, shugaban Syria na kusan shekaru 25, a wani farmaki da dakarun 'yan adawa suka yi.Duniya
Turkiyya ta nemi a kai zuciya nesa bayan ramuwar gayyar da Iran ta yi kan Isra'ila
Babban jami’in diflomasiyyar Turkiyya ya yi kira a guji yin abubuwan da za su iya ƙara haifar da tashin hankali sakamakon hare-haren ramuwar gayyar da Iran ta kai Isra’ila bayan harin da Tel Aviv ta kai a ofishin jakadancinta da ke Syria.Duniya
Iran ta fito da 'makamai masu linzami fiye da 100' don kai wa Isra'ila hari
Iran ta fito da makamai masu linzami don kai harin ramuwar gayya bayan Isra'ila ta kai hari a ofishin jakadancin Iran da ke Syria wanda ya yi sanadin mutuwar zaratan sojojinta bakwai, ciki har da janar-janar biyu, a cewar gidan talbijin na ABC News.Duniya
Ana tayar da jijiyoyin wuya tsakanin Isra'ila da Iran yayin da suke barazanar kai wa juna hari
An yi musayar yawu tsakanin Isra'ila da Iran bayan mahukunta a Tehran sun sha alwashin kai harin ramuwar gayya sakamakon harin da Isra'ila ta kai wa ofishin jakadancinsu da ke Damascus, lamarin da ya haifar da zaman ɗar-ɗar a yankin.
Shahararru
Mashahuran makaloli