Ramuwar gayyar Iran ta biyo bayan harin jirgin yaƙi da Isra’ila ta kai ofishin jakadancin Iran da ke Damascus, babban birnin Syria ne./Hoto: AA Archive

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya tattauna da takwaransa na Iran Hossein Amirabdollahian ta waya bayan harin ramuwar gayya na jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami 300 da Iran ta kai Isra’ila.

Fidan ya jaddada buƙatar Turkiyya na kauce wa faɗaɗa rikici a yankin bayan harin ramuwar gayyar na ranar Asabar da daddare kuma ya isar da buƙatar Ankara ta daina ɗaukar matakan da za su iya ƙara tashin hankali, kamar yadda majiyoyin diflomasiyya suka ruwaito.

Ministan Harkokin Wajen Iran Amirabdollahian ya nuna cewa sun gama ramuwar gayya kan Isra’ila kuma Iran ba ta da niyyar sake kai hari a ƙasar idan ba a tsokane ta ba.

Amirabdollahian ya yi gargaɗin cewa idan Isra'ila ta sake kai hari Iran, martanin da za ta mayar zai fi na baya.

Ramuwar gayyar Iran ta biyo bayan harin jirgin yaƙi da Isra’ila ta kai ofishin jakadancin Iran da ke Damascus, babban birnin Syria ne, wanda ya kashe zaratan sojin Iran bakwai ciki har da masu muƙamin janar-janar guda biyu.

Harin jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami da Iran ta kai Isra’ila shi ne karon farko da ta kai shi kai-tsaye daga ƙasarta zuwa Isra’ila.

Harin ya janyo damuwa cikin waɗanda suke tsoron cewa martanin da Isra’ila za ta iya mayarwa kan Iran zai iya janyo faɗaɗa rikici a yankin inda da ma can ake zaman ɗar-ɗar.

TRT World