Mulkin jam'iyyar Baath na shekaru 61 a Syria ya zo ƙarshe.
Mulkin Jam'iyyar Baath na shekaru sittin da ɗaya a Syria wanda ya fara da juyin mulkin da aka yi a 1963, ya zo ƙarshe, yayin da dakarun hamayya suka ƙwace iko da babban birnin ƙasar Dimashƙa (Damascus).
Jam'iyyar 'yan gurguzu ta Baath ta karɓi mulki ne a wani juyin mulki da aka yi a 1963. A 1970, Hafez al-Assad, mahaifin shugaban da aka tumɓuke Bashar al-Assad ya samu cikakken iko ta hanyar juyin mulki na cikin gida a jam'iyyarsa, sannan ya zama shugaban ƙasa a 1971.
Bashar al-Assad ya gaji mahaifinsa bayan mutuwarsa a 2000, inda ya ci gaba da mulkin Jam'iyyar Baath.
Yayin da ake ci gaba da raɗe-raɗin cewa Assad ya gudu daga ƙasar a jirgin sama inda ya nufi Homs, a yanzu ba a san ainihin makomarsa da inda yake ba.
A cikin wata sanarwa ta gidan talabijin ɗin ƙasar, 'yan hamayyar Syria sun bayyana cewa sun kuɓutar da Dimashƙa kuma sun tumɓuke Shugaban Bashar al Assad da ya shafe tsawon shekaru 24, inda suka ƙara da cewa an saki duka fursunoni.
Sun ce "an tumɓuke 'azzalumi' Bashar al-Assad."
Masu zanga-zangar hamayya da gwamnati sun yunƙuro da yammacin ranar Asabar a garuruwa maƙota, yayin da dakarun gwamnati suka janye daga muhimman wurare, cikin har da Ma'aikatar Tsaro, da Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida, da Filin Jirgin Samar ƙasar.
Shigar masu zanga-zangar muhimman wurare, na nuna cewa gwamnati ta rasa iko da babban birnin ƙasar.
Masu zanga-zangar sun durfafi gidan kurkukun Sednaya na gwamnatin ƙasar - wanda ya yi ƙaurin suna wajen gallaza wa waɗanda ake tsare da su - suka saki fursunoni.
Dakarun hamayya sun karɓe iko da mafi yawancin birnin Aleppo sun kuma mamaye gaba ɗaya Idlib zuwa ranar 30 ga watan Nuwamba.
Bayan mummunar arangama a ranar Alhamis, ƙungiyoyin sun ƙwace iko da birnin Hama daga dakarun gwamnati.
Ƙungiyoyin da ke hamayya da gwamnati sun ƙwace muhimman wurare ya yankin Homs suka kuma fara nausawa gaba.
A ranar Juma'a, ƙungiyoyin hamayyar sun ƙwace iko da Daraa a kudancin Syria kusa da iyakar Jordan.
Da safiyar Asabar kuma, sun kwace iko da yankin Suwayda a kudanci. Sannan dakarun hamayya na yankin Quneitra suka karɓe iko da babban birnin yankin.