Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya gudanar da jerin tattaunawa a gefen taron da ake gudanarwa a birnin Doha na Qatar. / Hoto: Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya ce mutanen Syria za su gyara makomar ƙasarsu wadda yaƙi ya ɗaiɗaita.

A wani jawabi da ya gudanar a karon farko tun bayan da ɓangaren adawa na Syria ya ƙwace iko da Damascus a ranar Lahadi, ya bayyana cewa miliyoyin ‘yan Syria waɗanda aka tilasta musu barin ƙasar a halin yanzu za su iya komawa gida cikin aminci.

Duk da tsare-tsare daban da ya fito da su na daidaita lamura, ciki har da kiran da Shugaba Erdogan ya yi na kawo mafita a siyasa, gwamnatin Assad ta yi watsi da tayin da ya yi mata, lamarin da ya ƙara jefa ƙasar cikin rikici, in ji shi, a lokacin da yake magana a gefen taron da ake yi a Doha na 2024.

“Shirin samar da zaman lafiya na Astana ya tsayar da yaƙin a 2016, gwamnatin ƙasar ta samu lokacin mai tsawo da ya kamata ta magance matsalolin,” in ji shi. “Sai dai ba su yi ba, a maimakon haka, sai muka ga yadda mulkin a hankali ya rinƙa lalacewa sannan ya ruguje wanda hakan ya yi bayani kan bayan harba harsashi ɗaya, sai Aleppo ta rushe wanda sauran biranen suka biyo baya.”

Fidan ya bayyana cewa za a iya kwatanta rushewar gwamnatin Assad da gazawarta wurin kula da al’ummar ƙasar.

"An yi watsi da bukatun al'ummar Siriya, kuma gwamnatin kasar ta kasa samar da ko da mafi ƙarancin ababen more rayuwa,” kamar yadda Fidan ya ƙara da cewa.

"Rabin jama'ar sun rasa matsugunansu, lamarin da ya haifar da matsalar bakin haure."

Ya jaddada kudurin Turkiyya na tabbatar da hadin kan kasar Siriya, da 'yancin kai, da kuma 'yancin yankin.

"Turkiyya za ta ci gaba da hada kai da kasashe makwabta da sabuwar gwamnati don sake gina kasar Syria da magance matsalolin tattalin arzikinta,” in ji shi.

"Turkiyya za ta dauki dukkan matakan da suka dace don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Syria."

TRT World