Turkiyya da Qatar sun amince su kyautata dangantaka a bangarori daban-daban, a cewar wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar a yayin ziyarar shugaban Turkiyya birnin Doha.
"Mun amince mu kyautata dangantakarmu a fanni daban-daban da suka hada da hadin kai na siyasa, diflomasiyya, tattalin arziki da cinikayya kamar yadda shugabannin kasashenmu biyu masu basira suka yarda don ci-gaban mutanenmu," a cewar sanarwar hadin gwiwa da ministocin kasashen biyu suka sanyawa hannu ranar Talata.
Ministocin kasashen Turkiyya da Qatar sun sanya hannu kan yarjejeniyar ce a yayin ziyarar da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya kai Qatar, inda suka yi bikin cika shekara 50 da kulla dangantakar diflomasiyya.
"Muna murnar cika shekara 50 da kulla alakar diflomasiyya tsakanin Jamhuriyar Turkiyya da Kasar Qatar a 2023,” in ji sanarwar. "Dangantakar Turkiyya da Qatar ta fuskanci sauyi na gari tun da aka soma ta a 1973 har lokacin da suka kai matsayi na musamman na hadin gwiwa.”
Sanarwar ta kara da cewa dangantaka tsakanin Turkiyya da Qatar ta nuna irin "zurfin" tarihin da suka gina a fannin siyasa da zamantakewa.
"Dangantakar da ke tsakanin Turkiyya da Qatar a yanzu tana ci gaba da yaukaka a kowanne mataki, kuma kasashen biyu suna samar da mafita iri daya a kan harkokin da suka shafi yankinsu da ma duniya baki daya," kamar yadda sanarwar ta bayyana.